← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 35

Sashe 35

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

A nan take tambayarsa labarin wani balarabe da ta hanga lokacin da ta iso, Mai Gari ya kwashe komai ya faɗa mata, dangane da Sheik a take ta ji ta kamu da muguwar ƙaunarsa, kuma in dai shi ne ta amince ko a cikin kara ne tw zauna ba wai a ƙauye ba. Ta sa a ranta idan Daddy ya zo garin nan ba za su tafi ba sai ta mallaki Sheik a matsayin miji, dole Daddy ya gina musu gida mai kyau inda za su rayu, ta haifi ƴaƴan larabawa, idan kuma Sheik ɗin yana so sai su tafi Abuja su rayu a can amma dai bata da mijin sai balarabe daga ƙasar Yemen.

Bata faɗawa Mai Gari ba ta dai bar maganar a zuciyarta zuwa safiya. Haka ta kwanta cike da shauƙi da ƙaunar Sheik tana fatan ya zo mata a mafarki.

*DARE*

Darebya tsala, kowa yana bacci sai dai Sheik sa tun da ya ga baƙuwar nan ya kasa sukuni, idanunsa yanzu ma sun hana shi ya runtsa saboda ya sanya tunanin ta a ransa kawai burinsa ya ji matar nan a kusa da shi. Juyi ya yi yana jon tunanin da ya saka a ransa ya hana shi sukuni. A take ya yanke shawara, tsaye ya tashi ya ɗako wani zani da hijabi cikin kayan da yake tsinta idan aka zo aka taru ana karɓar magani, sai a ga hijabi wani lokacin a rasa mai shi ko ɗankwali ko hula ta mata ko zani.

Zanin ya ɗaura ya saka hijabin, yana jin cewa yau ko ta halin ƙaƙa sai ya je ya ji ɗumin jikin baƙuwar nan, shaiɗan yana ta zuga shi yana masa linzami.

A zuciyarsa ya ce

"Ai na lura tana cikin buƙatar kulawa da soyayya, kuma ai ba za ta gane waye ba, buƙatar maje hajji sallah" Ya faɗa yana fitowa waje, yana duba gabas da yamma arewa da kudu ya ga babu kowa sai kukan karnuka kawai.

Katangar Mai Gari ya kama ya ɗare, da yake bata da tsawo ya sauka a hankali, yana lashe baki ya shiga ƙarewa ɗakunan gidan kallo yana so ya gano inda zai samu baƙuwar, ko dogon tunani ba ya yi ya fi so kawai ya ganshi a ɗakin.

Ɗakin matar Mai Gari ya fara leƙawa amma jin ana sakin munshari kamar an shaƙe raƙumi sai ya zaci ɗakin Mai Gari ne a tunaninsa Mai Garin ne yake munsharin.

Wani ɗaki ya shiga yana ji a jikinsa tabbas a nan masoyiyar tasa take, da sanɗa ya ƙarasa ya haye katifar ganin ta lulluɓe ruf da bargo shi na ya bankaɗa ya yi wa kansa masauki a ciki.

A hankali ya lallaɓa ya rungumo na bargon, a zuciyarsa yana cewa

'Alhamdulillahi, Æ´ar fara zo ki ji lallausar fatar balarabe'

Bai tsaya a nan ba ya kai baki zai kamo bakin, amma cikin rashin sa'a sai ya cafko hancin, ya manta ma da ƙirjinsa da aljannu suka masa ajiya, jin an cafki hancinsa sai hakan ya hana na cikin bargon shaƙar numfashi da kyau, yana riƙe da hancin a bakinsa yana sauke numfashin cin nasara da cikar burin sa.

Fisge-fisge na cikin bargon ya fara, yana son ƙwacewa amma Sheik ya ƙara zage ƙarfinsa ya maƙalƙale.

Cikin hargitsi aka ce

"Kai wai waye a nan ne, wane shegen ne ya shigo mini bargon yana lasar mini hanci kamar tsohon maye?"

Sheik a zuciyarsa ya ce

'La'ilaha ilallahu ba baƙuwa ba ce Mai Gari ne ai!"

Gaban Sheik ne ya doka da ƙarfi ya fara janyo salati a zuciyarsa da fatan Allah kuɓutar da shi, a take ya fara ƙoƙarin ficewa daga cikin bargon, Mai Gari jin haka sai ya kai hannu ya riƙo shi, tunanin Mai Gari rigar mutumin ce ya riƙo ashe hijbin ne ya riƙe saitin fuskar, Sheik ya rasa ta ina zai fito da kan nasa ma domin Mai Gari ya cukwikuye, yana faɗin

"Wane kwarton ne wai, wato an ga na yi baƙuwa daga birni"

*A NAN NA KAWO ƘARSHEN BOOK 1 MAI SON SHIGA GROUP YA ƘARANTA ZAO BIYA 500, MAI SON CMPLT DOCMENT 800*

IDAN KINA SON JIN YA ZA TA KAYA KI BIYA KI KARANTA A NUTSE

*MAMAN AFRAH
09025576222*

*ZA A BIYA TA FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA 09025576222*
Chapter 35 · 0% Book details