← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 35

Sashe 19

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai zaƙu har cikib kaina wallahi, wannan mangwaro da zan samu iri ai da na shuka, to ke waye yake kirana in ka ji kira ai samu ne"

Baki Lami ta damƙe cikin dakewar murya ta ce

",Inna, ina ce dai kina sane yau kwana ukun da Mai Gari ya ɗauka a kan maganar saniyar da Ibra ya tafi da ita" Tari ne ya sarƙe Inna jin wata gagarumar matsala sabod ita kwata-kwatanta manta don maganar ta kwanta mata , sanadin tarin da ta yi mangwaron hannunta ya suɓuce ya faɗi a ƙasa amma ko ta kansa bata bi ba ta ce

"Lami waye ya faÉ—a miki wannan magana, yanzu haka ma Mai Gari ya manta da zancen nan amma saboda ke ce mai tada zaune tsaye kika je kika tado da maganar ko?"

Lami ta ce

",To ba ni ɗin ba ce, Jummai ce tun da sanyjn safiya ta je faɗawa Mai Gari cewa kwana uku sun cika amma Ibra bai dawo gari ba, to da ta je da safen Mai Gari ba ya nan sun yi asubanci sun je wani ƙauye gaisuwa, shi ne yanzu ta koma da yamma, tana can ma fadar Mai Gari cike maƙil da mutane, yanzu ma daga can aka aiko ni kiranki, saboda kowa ya hallara amma ban da ke" Idanun Inna suka yi rau-rau tana tunanin abin yi sai ta ji hankalin ta ya tashi domin ita ta manta da wannan maganar kwata-kwata ashe dai yau wa'adin kwanakin zai cika.

Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta ce

"Kai jama'a ba dan na shiga ban ɗauka ba bata fitar da ɓarawo wallahi da babu abin da zai kai ni fadar Mai Gari, saboda bani da kuɗin saniya, ban ajiye ba "

Lami ta ce

"To Inna ni ina zan gane wannan yaren naki, Mai Gari za ki yi wa bayani" Banza ta yi da Lami ta wanke hannunta, ɗaki ta shiga ta haɗo kan kuɗin kayan miyan da ta sayar, akwatin ƙarfen ta ta buɗe tana zaune a gaban akwatin ta fito da atamfofi guda uku ɗinkakku, wanda a wanke suke tas sun sha linki takaicin ɗakko atamfofin take ji a ranta amma haka ta zuba a ledar Viva ta fito ta ɗakko wata samira irin ta ƴan da mai hawa huɗu duk sun yi lamba a jiki, ta ce Lami ta riƙe mata, ita kuma ta yafa gyalenta ta ɗauki ledar atamfofin ta rufe gidan suka kama hanya a ranta tana cewa

'Ba saniya ba ko giwa ce Ibra ya gudu da ita in na bada kayan nan ba zan ƙara komai ba' Ta faɗa tana kallon setin samirarta da yake kan Lami...

MAMAN AFRAH
09025576222

[7/9, 3:38 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BcJ4LIJJQlfHRgfiJUnBJo?mode=r_c

👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*

BOOK1️⃣
PAGE 9

*SHEIK*

Jin kamar dai babu alamun wani da zai taho daga ƙofar gidan ya kawo masa ɗauki, wato ya tabbatar muryarsa bata isa waje ba, don haka yanzu kam matar ta cim masa ba zai iya ma bari ta cigaba da azabtar da shi ba, dakyar ya ƙwace kansa ta shiga binsa da gudu suna tsere a ɗakin bai ankara ba sai ya ji ya kama rigarsa daga baya a haka yake gudun tana jansa tana rinjayarsa kasancewarta ƙatuwa ta fishi ƙiba, sai ya zamana dakyar yake iya gudun kasancewar rigarsa jallabiya ce a zuciyarsa ya ce

'Ina ganin ikon Allah, in ban da maluntar nan da na ɗakko ta larabawa ina dalili mutum zai kafa fama kullum da doguwar jallabiya kana tafiya tana taɗe ka' Ya faɗa a daidai lokacin sun zo saitin ruwan da ya ajiye, wanda yake kwalfa yana ba mutane, ruwan ne suka ture ya zube, tsautsayi ya sa suka shiga ciki gabaɗaya Sheik ya yi gaba ya yi baya ji kake tim santsi ya kwashe shi ya faɗi, ya yi zaman ƴan bori a cikin ruwan ita ma tana ɗora ƙafarta sai ta zame ta tiƙu da ƙasa.

A reran ta je ƙasa, ganin haka Sheik ya yi ta maza ya daure ya matso don ba ƙaramin buguwa mazaunansa suka yi da ledar ba, qulhuwallahu ahad ya shiga karanta mata yana tofa mata sai dai wannan karon ba tofi ƙarami yake yi ba tsabar bala'in da yake ganinsa a ciki, yawu kawai yake tofa mata ba kaɗan ba.

Karkarwa ya ga jikinta yana yi kuma ya fahimci kamar jikinta ya yi sanyi alamar aljannun za su sake ta, da hanzari ya janyo hularsa ganin ta ɗan leƙo daga bireziyar da ta saka ta a ciki, bai sake bi ta kanta ba sai ya shiga suturta kansa wato ya saka hularsa da gemun, mukullin ya gani a inda ya faɗi daga hannunta ya ɗauka ya buɗe ƙofar yana mayar da numfashin wuya, jin maganar wani mutum yana rafka sallama sai Sheik ya ɗauki wata ƙatuwar bulala da take ajiye ya ɗaga ya tsulawa matar nan da ƙarfi ta ce

"Zan fita" Gabansa ne ya faÉ—i sai yanzu ya fahimci ashe aljannun basu saka ta ba, sai ya ji mutumin nan na waje yana cewa

"Ah ashe dai ruƙiyya ake yi wa matar nan, shi ya sa ta daɗe ta bar mutane a layi ana jiran fitowarta, bari in fita in faɗawa jama'a halin da ake ciki" Ta haka Sheik ya fahimci cewa mutumin da ya shigo ya zo ne ya ga dalilin daɗewar matar.

Can kusa da katifar ya koma yana raɓe, har sai da ya ga matar rana sakin atishawa wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke ganin yana sha n wahala a maluntar nan ta BOGI amma ƙarfin hali da sa kai wanda ya fi wauta ciwo ya hana shi barin maluntar bogin.

Duk da ya san yana amfani da maluntar yana damfarar jama'a bayan ya san shi jahili ne babu abin da ya sani, ko surorin qur'ani da yake karantawa izun ƙasa ne, tun lokacin yana zuwa makaranta kafin ya kangare da ya kangare kuwa ai makarantar ma ba ya zuwa. Ko karatun bokon ma ko secondary bai gama ba.

Zaune ta tashi tana kalle -kalle ta ce

"Waye ya kawo ni nan" Sheik ya ce

"Magani aka miki maza tashi ki je gida, kike shan sauran ruwan alwalar la'asar da magriba, sauran aljannun kan naki za su kama gabansu" Shiru ta yi ba don ta gama fahimta ba, ta muskuta ta tashi tana ganin yadda duk ta jiƙe, fita ta yi Sheik a fili ya ce

"Gwara in faɗa miki bogi ki tafi yo ina na ga nutsuwar baki magani ma ki je ki ƙara shaƙo ni, ni na rasa mai hular gashin nan nawa ta yi wa aljannu da mutane, duk abin jikina ba a kaiwa komai farmaki sai hula ta" Ya faɗa yana gyara zaman hular, yana tuno artabun da ya sha da aljannu suka ɗauke masa ranar nan.

Dakatar sa masu shigowa ya yi, ya sauya jiƙaƙƙiyar rigarsa ya goge ruwan, a haka ya cigaba da karɓar mutane suna bashi kuɗin yana tarawa ransa fari ƙal yake ji idan ya kalli kuɗin nan yana zaune yake samu.

Sai da ya gama da jama'a ya ce sai kuma gobe za a cigaba da karɓar mutane.

Tun daga wannan rana Sheik ya zama limamin garin Ƙundu, shi yake jan sallah, sai dai waɗannan ƙananun surori na ƙasa su ne kullum yake jan sallar da su, idan yana jan sallah ya ƙara maƙe murya ya lanƙwasa sai ka ɗauka cewa a masallacin makka ne ake jan sallar amma dai a wajen mutanen Ƙundu, saboda su ne basu gama tantance asalin karatun balaraben mutum da kuma Sheik baƙar fata wanda mayuka da sabulai suka wanke masa fata. Idan za a yi sallah mutanen ƙauyen kafin Sheik ya zo masallaci sai masu manyan wayoyi adroid su zo su kunna recording su ajiye wayoyin, daga an yi sallah an idar, sai ka ga idan sun fita daga masallacin suna samun wuri su kunna, suke ji sai ka zo wucewa ka ga mutum ya duƙufa da earpiece a kunna sai dai ka ji yana faɗin

"Allahu akbar, uhmmm, ma sha Allahi, Allah ƙara lafiya babban malamin ƙasar larabawa"

Sai ya zamana hatta mata masu waya sai su ba mazajen su, wayar in za su je masallaci su É—akko musu sallar Sheik.

Wanann dalilin ne ya sa Mai Gari ya ce Sheik ya musu karatun qur'ani wanda za suke saurara a waya, na izu sittin irin wanda ake turawa na su Ahmad Sulaiman da yake Mai Gari yana da irin su a waya. A nan ne fa gizo yake saƙa, don Sheik ya san dai bai sauke qur'ani ba hakan ya sa ya ƙaƙalo ƙarya kamar yadda ya saba ya ce

"Ai an fi so mutum yake sauraren abin da ya iya, wato tun da basu sauke qur'ani ba ba za suke saurara, na fi so kuke sauraren izufin ƙasa saboda kuke biyawa yadda za ku ƙara ƙwarewa a hadda" Ya faɗi haka don ganin ya tsira daga tarkon wannan, hakan sai ya sa Mai Gari ya gamsu Sheik ya musu rukodin ɗin iya surorin ƙasa da ya iya, suke saurare.

Batun magani kuwa duk waɗan da Sheik ya ba magani sai suka zo suke godiya da saka albarka a cewarsu magani ya musu amfani, saboda Sheik yana zama ya yi wa'azi a kan cewa ba a ƙaryata malami ko a tuhume sa, hakan ya sa ko da mutum bai ga amfanin magani ba sai yaja bakinsa ya yi shiru, sannan ma dama duk abin da aka baka a matsayin magani in dai ka yarda cewa zai yi to ko ba maganin bane yana maka magani.
Chapter 19 · 0% Book details