← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 35

Sashe 21

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruɗin da yake ciki ya sa bai rataya hiramin a wuyansa ba kamar yadda yake saƙalawa, yau sai ya masa naɗin gwaggwaro, daga gaban goshin ma naɗin ya ɗan zamo ya karkace sai ya yi tamkar tsohuwa, ya ya ɗauki zumuƙeƙen carbinsa, ya ɗauki littafinsa na ƙamus, sai wani ruwan magani da ya karɓo cikin magungunan da ya siyoa wajen malaminsa, shi tsabar ruɗani ma ya manta ko ruwan maganin mene ne.

Yana fitowa ƙofar ɗaki ya ga saka takalminsa ya ga su Mai Gari tsaye suna jiransa, fitowarsa ke da wuya duk da ruɗun da suke ciki sai suka fara magana cikin girmamawa.

"Allah ya taimaki balaraben Malamin, Allah ƙara ilimi, haƙiƙa mun samu jajirracce da yau sai dai kowa ya yi hijira daga garin nan don ba za mu iya da wanann aljannun ba" Sheik a zuciyarsa ya ce

'Kwa mini kirari mana tun da kun haɗani da aikin tsohuwar gawa da sabuwa, yau ai sai ta Allah' Ya faɗa yana yin yaƙe tare da ƙara ƙanƙame littafinsa a ƙirjinsa yana jan carbin haka suka fito daga gidan bayan ya kulle ƙofar.

Abin da basu sani ba shi ne, Sheik ya fi su shiga ruÉ—ani da tashin hankali.

Tun da suka fito tsakiyar garin maza suka fara tururuwa don sai lokacin, suka ji ƙarfin gwiwar fitowa tun da Sheik ya fito gani suke aljannu ba za su fafata da Sheik ba ko su ja da shi.

Sheik ne a gaba mutane gari suna take masa baya, sai wani bada faɗi yake shi ala dole masanin qur'ani da addu'o'i, ana cikin tafiya, sai lokacin ya kalli ƙafarsa, idanu ya zaro ganin takalman ƙafarsa gamin bauta ne, wato takalmin ƙafar dama takalminsa ne sandal amma kuma na ƙafar hagun ne ba wai na ƙafar dama bane, don haka a juye yake, shi kuma takalmin ƙafar hagun ɗin silifas ne na wankansa, amma kuma ƙafar dama ne a hagun ɗin wato dai shi ma a juye yake a zuciyarsa ya ce

'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, mutanen garin nan kun saka ni a masifa, da tashin hankali tun da uwata ta haife ni ban taɓa wannan gamin bautar takalmin ba, amma yau saboda kun jefani a ruɗani gashi nan, takalmin kwalliya da na wanka na saka, su ɗin ma kowanne ba ƙafar ba ce'

MAMAN AFRAH
09025576222
[7/10, 4:03 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BcJ4LIJJQlfHRgfiJUnBJo?mode=r_c

👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*

BOOK1️⃣
PAGE 10

*MAƘABARTA*

Tun da Sheik ya lura da takalminsa sai ya wayince ya je kusa da Mai Gari ya masa raÉ—a cewar garin saurin ya zo ya ceci gari ya sako takalmi ba iri É—aya ba, Mai Gari ya ce

"Allahu akbar! Tabbas Sheik kana ƙaunar garin nan" Nan ya nuna masa babu komai ruɗun da jama'a suke ciki ma ba zai bari su lura da takalmin ba, kuma ko sun lura ma sai a musu bayani. Wannan bayanin ne ya sa Sheik ya ji daɗi tun da ya lura yanzu dai ba za a zargi cewa tsabar ruɗani ne ya sa ya sako takalmi gamin bauta ba daidai ba.

Tun da suka zo dab da maƙabarta Sheik gabansa ya fi na kowa faɗuwa, amma a haka ya daure yake jan carbi, da yake maƙabartar ƙauyen ba a kewaye take ba, sai dai akwai bishiyoyi da suka mata ƙawanya, sannan akwai hanyar da aka ware don ake shiga ta wajen.

GabaÉ—aya jama'ar sai suka yi turus kowanne yana tsoron shiga, Sheik ne a kan gaba sannan suka mara masa baya. Suna shiga jikinsa yana karkarwa amma sai ya maje ya nuna ba karkarwa jikin nasa yake ba, mutane gabaÉ—aya suka tsaya suna jiran su ba abin da zai faruwa, kowa yana gefe.

Ƙarasawa ya yi gaban kabarin guda biyu gabansa yana faɗuwa, kallon ɗaya da aka tono ya yi, wani yawu ya haɗiye muƙut ya juya ya kalli Mai Gari ya duk kamar a ce asss su zura da gudu, ɗan wayincewa ya yi ya ce

"Babu tsoron Allah a wannan lamari, a ce a tone gawa tsohuwa da sabuwa, kai Allahumma ajirni min wannan mummunan aiki, ya subhanallah," Ya faÉ—a yana girgiza kai irin na malamin da ya ga an yi wani aiki marar kyau.
Wani ne daga cikin tawagar mutanen ya ce

"Ni fa a hanya na haÉ—u da masu binne yaron can, na ji suna cewa wai ji suka yi yaron ya saki kuka shi ne aka rasa mai tsayawa a cikin su...

Kafin saurayin ya gama magana Sheik ya kai hannunsa mai carbi ya sharce gumi, ya ce

"Alkazibu, ƙarya haramun, babu gawar da za ta yi kuka" Duka wurin babu wanda ya tona don shi Sheik sani ne bai yi ba kafin ya zo garin wataran tsakiyar dare ake jin ƙaran turmi ana daka a cikin maƙabartar ko dai a ji ƙaran injin markaɗe, abubuwa dai barkatai.

Mai Gari ya kalli Sheik ya ce

"Ya Sheik ko da matsala ne?" Sheik ya ce

"Ah haba matsala da kanta ƙarya take ta doshi balaraben Malami daga Yemen" Wani sanyi ne ya ratsa zukatan mutanen wajen.

Sheik ya matsa gaban gawar guda ɗaya, ya buɗe littafin hannunsa, ya shiga dubawa kamar mai duba qur'ani ki littafin addu',oi ya ji ya kasa komai so yake ya karanta wata addu'a ko sura amma bakinsa ya ƙi basa haɗin kai, ganin haka ya juya ya kalli jama'a ya ce

"A karanto" Suka kalle shi da rashin fahimta.

"Mai za a karanto?" Mai Gari ya tambaye shi

Sheik ya ce

"Kowa ya karanta karatun da ya iya" Ya faɗa don shi ya kasa saamun kowacce sura ma bare ya karanta, haka kowa ya buɗe baki yana karatu a nan Sheik ya fisge wata surar ya fara, kowa yana kaiwa ƙarshe sai aka yi ɗif, matsawa ya yi ya ɗauki shebir ya fara kwashe ƙasar kabarin, saboda gabaɗaya ƙasar ta koma ta rufe inda za a mayar da mutumin yana cikin kwasowa ya ga cinyar mutum a ciki, gabansa yana faɗuwa ya juyo zai sanar da mutane tun da su suna can baya sun bashi wuƙa da nama.

Kafin ya furta komai sai ji ya yi gawar wajen ta saka ƙafa ta tura shi sai ga Sheik ya kusa ya faɗa ciki, dakyar ya yi nasarar komawa gefe yana haki lokacin mutane duk sun ƙara ja baya, littafinsa da ya ajiye ya ɗauka tare da maganin nan da ya ɗakko na wajen Malam yana nufo mutane gabansa yana faɗuwa don ya tabbatar gawar nan ta tura shi gashi tsohuwar gawa.

Yana zuwa ya ce

"Kar ku damu wannan ba wani abu bane, akwai siddabarun aljannu a lamarin, kuma wannan mayar da gawar kabari ba na mutum É—aya bane ku matso mu taru mu yi aiki tare" Kowa ya fara zare ido Sheik ya ga suna masa kallon tuhuma.

Da sauri ya nuna musu robar maganin hannunsa ya ce

"Wannan magani ne daga ƙasar Yemen na taho da shi idan aka yayyafa a bakin kabari aljannu suna guduwa cikin daƙiƙu" Si ya ga kowa ya ɗan saki jiki.

Bai nuna musu ya ga cinya a cikin ɗaya kabarin ba haka suka mayar da gawarwarkin don sun yarda da maganin da Sheik ya barbaɗa basu san cewa shi kansa Sheik ɗin bai san maganin mene ne ba wataƙila ma yana cikin magungunan mallakar da za a ba mata.

Kabarin yaro nan ne kawai ya rage, Sheik ya ce tun da ba gawar garin ba ce a nemo ƴan garin su zo su binne, don tun da ya ji saurayin nan ya ce an ce gawar ta yi kuka sai ya tsorata dama gabaɗaya ma ƙarfin hali yake yi.

Mai Gari ya ce ai kawai su binne tun da yana cikin tawagar mutane ai su ma garin namu ƙarƙashin mulkinsa yake. Kai Sheik ya gyaɗa tana wayincewa, sun kewaye kabarin mutane damƙam, Sheik tun da shi ne balarabe shi ne yake jagorantar komai.

Hannu ya miƙa zai ɗauki yaron , da ya miƙa hannu ta wajen kan yaron sai ya ga kamar ba shi ya ɗago kan yaron ba, kamar dai gawar ce ta ɗago da kanta, da sauri ya janye hannayensa ya ɗago sai ya ga ba a lura da abin da ya gani ba, kamar gawar ta san mai yake tunani kawai sai ya ga ta fara ɗagowa sai ga yaro a zaune dakaka duk da yana sanye da likkafani, Sheik da ya tashi a firgice ya tsallake yaron sai ƙafarsa ta maƙale da likkafanin da aka ƙulle ƙafar yaron yana fisga ya yi tsalle da yake yana ɗaya gefen ne Mai Gari kuma suna ɗaya gefen, sai lokacin kowa ya lura da abin da yake faruwa, tun da dama gawar yaron daga can gefen kabarin take ba a dab da kabarin ba, tsalle ɗaya Sheik ya yi ya tsallake ramin kabarin sai gashi a gaban Mai Gari ya kama rigar Mai Gari, jama'a kowa ya fara kama gabansa da yake dama maƙabarta ba wani a kewaye take ba sai kowa ya fara kama gabansa wasu gabas waau yamma wasu arewa, Mai Gari da Sheik suna cikin mutanen da suka fita ta yamma.

Don Mai Gari ya warce riƙon da Sheik ya masa haka suke falla gudu kowa yana ta kai- ta kai.

Babbar rigar Mai Gari sai tashi sama take, rawanin ya kunce yana binsa yaraf, ko takalmi babu a ƙafarsa ya sille, Sheik ƙafarsa maƙale da dogon tsumman likkafanin da aka ɗaurewa yaron ƙafa, haka suka ratsa ta cikin gonaki suna sheƙa gudu, Sheik ya tattare jallabiyarsa saboda gudun samun akasin faɗuwa, suna cikin gudu da yake Mai Gari ne a gaba Sheik yana take masa baya, jama'a kuwa kowa ya yi tashi hanyar, kamar daga sama sai ganin wannan yaron da suka baro a maƙabarta zaune a kan makara ya diro a gabansu, Sheik ya taka wani uban birki shi ma Mai Gari haka, sai Sheik ya juya a guje ya bi wata hanyar sai tafiyar ta kasance Sheik ne a gaba Mai Gari a baya gawar yaro tana take musu baya.
Chapter 21 · 0% Book details