← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 35

Sashe 23

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da daddare yana zaune ya gama cin abinci sai ga Mai Gari, Liman, da wasu dattijai guda uku, suka zauna aka sake gaisawa, Mai Gari ya yi gyaran murya ya ce

"Ya Sheik a matsayina na Mai Gari na zo da wata buƙata" Buɗar bakin Sheik sai cewa ya yi

"Haba Mai Gari ai babu abin da za a nema a rasa a wajensa, har da cewa ya yi alƙawari tun bai ji abin da ake buƙata ba.

Mai Gari ya ce

"Wannan yarinyar da ka yi wa ruƙiyya da yamma mai ido ɗaya... Gaban Sheik ne ya faɗi tunaninsa ko za a ce aljannun ne suka sake tashi, saboda dama dai ya san lafawa suka yi ba wai sun bar jikinta bane.

Mai Gari ya cigaba da cewa

"Aljannu sun karɓi ƙarfin jikinta, sun hana ta sakat sun ce sai an ɗaura mata aure da kai, in ba haka ba wani gagarumin bala,i zai sauka a garin nan sai sun kashe rabi da kwatar jama,ar gari...

MAMAN AFRAH
09025576222

[7/11, 4:08 PM] Mom mashkur & Afrah: IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo?
To shiga group É—in IMZEEDVENTURE!
Za ki sha mamaki! 🤩Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau
📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
📩 DM: WhatsApp
📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture

👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️
NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝
Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*

BOOK1️⃣
PAGE 11

*RAHMA*

Tsabar firgici da mamakin furucin Ma'aruf tsaye ta miƙe, shi kuma Ma'aruf ganin Sulaiman sai hakan ya sanya ya shafawa idanunsa toka, don a yau ya ci alwashin babu gudu babu ja da baya, dole ya bayyana sirrin zuciyarsa ko ta halin ƙaƙa ko da kuwa hakan zai zama sanadiyyar afkuwar gagarumar matsala.

Hannu biyu ya saka a aljuhunsa ya yi wata irin tsayuwa ta yaran zamani, in ban da su da suka san shi kuma suka raina masa hankalin cewa shi baƙauye ne babu wanda zai ce ya taɓa zama a wani ƙauye, cike yake yau da kwarjini haɗe da haiba kyawunsa ya ƙara bayyana, yana sakin wani shu'umin murmushi, yana mai kafe masoyiyar tasa Rahma da idanunsa da ta ji sun zame mata tamkar miki, don yau sai ta ji ya mata wani kwarjini sai dai ba za ta bar kwarjininsa ya rinjayi zuciyarta ba, dole za ta tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, saboda ma kar ya yi gigin furta wata kalma a gare ta.

Mummy kuwa kallon ƙasƙanci da raini ta shiga jifan Ma'aruf da shi, ganin yana tsaye a inda tilon ƴarta take sannan ga ɗan minista da take fatan ya zama sirikinta wato Sulaiman.

Sulaiman kuwa tun lokacin da ya ji furucin Ma'aruf sai zuciyarsa ta buga, tsanar da ya yi wa Ma'aruf ɗin ta ƙara linkuwa a zuciyarsa, a gefe ɗaya su duka yana jifansu da kallon tuhuma, musamman tauraruwar tasa wato Rahma.

Rahma ita ta rasa ma abin cewa don furucin Ma'aruf ya bata ɗimbin mamakin da ta kaaa furta uffan duk da a ƙoƙarinta na ganin ta masa tatas.

Mummy ce ta katse shirun da ya ratsa wajen, da kuma kallon tuhumar da wasu suke jifan wasu, sannan da zulumi da taraddadin da zukatan wajen suke ciki ta ce

"Ma'aruf lafiyarka kuwa, wanann wane irin daƙiƙanci ne? Ko an faɗa maka bakin rijiya wajen wasan makaho ne" Ta faɗa tana masa alama da hannu na tambaya. Amma abin mamaki maimakon ya girmama ta kamar yadda yake yi a kullum sai ta ga ya ɗan murmusa ya ce

"Mummy ina baki haƙurin furucina sai dai, furucin da zan yi yanzu zai sha gaban wanda kika saurara, amma sai dai ina so matsayinki na Mummynah ki tayani neman karagar mulki a zuciyar Rahm... A ƙufule Mummy ta ɗaga masa hannu alamar dakatarwa tana huci kamar kumurcin zaki ta ce

"Allah wadaran naka ya lalace wai jakin dawa ya ga na gida, an faɗa maka ni ina da wani ɗa a duniya da ya wuce Rahma? Idan mafarki kake ka falka daga mummunan mafarkin da kake yi, ka wartsake idanunka ka san da wa kake magana, Rahma ta fi ƙarfin talaka baƙauye irinka ka taka a sannu in ba haka ba za ka ɗakko ruwan dafa kanka" Rahma ce da ƙwallar takaicin furucin Ma'aruf ya cika mata ido saboda takaicin cewa yana neman karagar mulkin zuciyarta ta shiga nuna shi da yatsa ta ce

"Wallahi ahir ɗinka, ko giwa ta faɗi ka sani ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka, wallahi, wallahi, wallahi, idan har baka taka a sannu ba za ka yi da na sani na har abada, rainin ma ya yi yawa, ni Rahma kake wa wannan furucin? Ina so ka sani matsawar baka dawo cikin hankalinka ba to za ka taka dakalin da yake ɗauke da ruwan ɗanyar kuɓewa, a ƙarshe ka zame ka karkarye a banza a wofi" Ta faɗa tana hayayyaƙo masa.

Sulaiman fara takawa ya yi a sannu sai da ya zo har gaban Ma'aruf ya tsaya, kallon kallo aka shiga yi, tsakanin Ma'aruf da Sulaiman, shi Sulaiman ransa a mugun ɓace shi kuma Ma'aruf yana sakin wani shu'umin murmushi.

Hannu Sulaiman ya sanya a cire glases ɗin fuskarsa, ya kafe Ma'aruf da idanunsa da takaici ya sa suka yi jawur, yana masa wani kallo irin na raini, ba komai yake baƙanta masa zuciya ba sai yadda Ma'aruf ya fi shi kyau da cikar haiba, kai zai iya cewa Ma'aruf ya fi shi komai kuɗi ne kawai zai Sulaiman zai faɗa masa.

Sai dai inda gizo yake saƙar shi ne, Sulaiman babu ɗigon ko da son Rahma a zuciyarsa, ba komai bane a zuciyarsa sai yaudara yana so ne kawai ya raba ta da mutuncin ta, shi ya sa ya yi amfani da zaƙin baki da nuna soyayya da kulawa na ƙarya har ta amince da shi, a halin yanzu duk ta rabu da samarinta duk da dama su ɗin ma za ni ce ta tarar da muje mu, ma'ana babu wani na kirki duk ƴan ƙarya ne ƴaƴan manya masu kuɗi.

Baƙincikinsa ɗaya shi ne ya fahimci matsawar Ma'aruf ya furta so ga Rahma to ko da a ce bata son sa to zai yi iya yinsa ya ga ya hana shi cim ma burinsa, haka ya fahimta saboda ya lura ko a cikin gidan za su hira, sai yake neman zame musu ƙadangaren bakin tulu, yana hana su rawar gaban hantsi.

Ba ma wannan ba kawai zuciyarsa ta bashi raina masa hankali suka yi, ma'ana ya fara zargin Rahma tana son Ma'aruf ne in ba haka ba ya zai zo ya tarar da su a lambu tare ya yi shiga mai kyau, sannan shi da kansa ya ji Rahmar tana faÉ—in wasu kalmomi na soyayya ga Ma'aruf shi ma kuma Ma'aruf É—in ya mayar da martani, zuciyarsa ma ta bashi cewa zuwan Mummy wajen ne ta musu alama da cewa ya iso wajen shi yasa suke masa wasa da hankali suke raina masa wayo. Ya dara tunanin kawai ma amfani ake yi da shi ana cin kuÉ—insa.

Hannu Sulaiman ya kai ya dafa gefen kafaɗar Ma'aruf amma sai Ma'aruf ya saka hannu ya ɗauke hannun Sulaiman daga kafaɗarsa ya warɓar da shi, daga Rahma har Mummy baki suka saki saboda yau ɗaya Ma'aruf ya sauya musu, ran Sulaiman ne ya ƙara ɓaci a ganinsa wannan baƙauyen har ya kai ya masa haka? A ƙufule ya nuna shi da yatsa ya ce

"Kai ƙaramin ƙwaro, ƙaramin ɗan iska, ina so ka sani ko da mai ka zo an fika, ruwa ba sa'an kwando bane kuma ni na fi ƙarfin in yi tarayya da kai a wajen mace ɗaya... Rahma jin wannan furucin sai ta lumshe idanu, tare da sakin wani murmushi saboda ta lura Sulaiman zai ladabtar sa Ma'aruf ko da kuwa da kalamai ne, Mummy kuwa jinjina ta hau yi wa Sulaiman a zuciyarta, tana jin gwara ma a bar shi da Sulaiman ɗin ya nuna masa kudu ba arewa ba ce.

Sai dai me? Sai suka ji saɓanin abin da suke tunanin ji wato Sulaiman ya cigaba da cewa

"Don haka in dai Rahma ce ka je na bar maka" Daga Mummy har Rahma sai da gabansu ya yi mummunar faÉ—uwa, suka shiga zare ido jin za su yi babbar asarar É—an masu kuÉ—i, duk da suna da kuÉ—i amma sun san Sulaima tsani ne a wajensu na cim ma wasu burika a rayuwarsu.

Da sauri Rahma ta matso tana kafe Sulaima da idanu ta ce

"Ka san mai kake faɗa kuwa Baby? Yanzu my love wannan ƙazamin kake yi wa furucin ka bar masa ni, in ce dai wasa kake ko?" Ta faɗa tana kallonsa don so take ta ga ya wawwanke fuskar Ma'aruf da kyawawan maruka, don ya zame masa izna kuma darasi a nan gaba, don su basa so su masa wani abu cibi ya zama ƙari idan Daddy ya dawo.

A zuciye Sulaiman da yake jifan Rahma da kallon tsana ya ce

"Ke dalla malama dakata! An ce miki kowa sakarai ne, ko kin ɗauka ni ɗin ma sakarai ne irin samarin da kika yaudara saboda kin same ni kika sallame su? To ni da hankalina, na san abin da nake, ni za ki rainawa hankali, in zo in same ki kuna soyayya amma ki nuna mini bariki, to ni nan na fiki sanin bariki idanuna a buɗe suke yadda bakya zato" Ya faɗa yana hayayyaƙo mata tamkar zai kai mata duka.

Ma'aruf ya ji daɗin hakan ya san kuma ko da bai auri Rahma ba to tabbas ya cire mata mugun iri a rayuwarta, saboda ya san Sulaiman mayaudari ne ba don Allah yake sonta ba, yana amfani da ita ne saboda cim ma wata dama tashi daga ya samu biyan buƙata ya tabbatar zai cikawa rigarsa iska, in ma bai barta da guzurin ciki ba.

Mummy ce ta dafe ƙirji ta ce
Chapter 23 · 0% Book details