Sashe 33
Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har dare ya tsala yana nan tsakar ɗakin yana murƙususu, ganin dai abin ba zai masa ba, tashi ya yi ya lalaɓo ya fito yana sanɗa ya nufi ɗakin Jummai, tun kafin ya ƙaraso yake jin tashin munsharin Jummai, da na yaran da suke kwance a tsakar ɗakin. Da yake akwai fitilar ƙwai irin ta mutanen da, an barta a kunne amma kuma an rage hasken.
Inna wacce ita ma baccin ta kasa tana ta juye-juye, a kan idanunta Sule ya shigo ɗakin, ai kuwa ta ɗan ɗago kai yake mata zancen kurma da hannu yana tambayarta ina adda, da hannu ta nuna masa inda ta ga Jummai ta ajiye, lallaɓawa ya yi ya ɗakko ya tura ƙasan gadon, gaban gadon ya ƙarasa ya juya bayansa Inna da sauri ta tashi ta ɗare bayan Sule ya goya ta, cike da zumuɗi suka baro ɗakin Jummai ransu fari ƙal.
Ashe tun shigowar Sule Jummai ta falka tana kallonsa munsharin ƙarya take, kawai ta bari ta ga gudun ruwansa, suna fita ta sakko daga gadon ta ɗauki addarta, ta fito ta bi bayansu Sule yana shiga ɗakin ya garƙama sakata, sai kuwa ga Jummai ta sake dawowa, amma kasancewar a rufe sai ta kasa shiga, ta window take musu magana tare da cin alwashin muddin Sule ya kusanci Inna sai ta ɓalla ƙofar ta zo ta musu aika -aika.
Tsabar tsoro sai Sule ya kasa komai, tun da tana tsaye ma Jumman tana kallon su, haka ya zauna a ƙasa yana kifa wani uban tagumi, don shi ya ga mace a ɓagas yana ganin ya tsinci dami a kale, babu sadaki babu kuɗin aure ko biyar bai kashe ba.
Inna tana zaune ta miƙe ƙafa tana jin kamar ta shaƙe jummai, a haka suka kwana babu wanda ya runtsa a cikin su.
Da asuba haka Inna ta yi alwala sai da ta ɓata buta guda a wajen tsarki saboda ni'imar da ƙwaƙwalwar raƙumin nan ta sanya mata a zuciyarta ta ce
'Wannan yarinya Jummai an yi Æ´ar kan uwa, da bata kasa ta tsare ba jiya Allah kaÉ—ai ya san ganimar da za mu kwasa, amma don asara kalli yadda nake wanke ni'imar a banza tana bin makwararar banÉ—aki'
Haka ta yi sallah ranta duk ba daɗi shi dama tun da ya tafi masallacin ma bata ganshi ba, ita kuma Jummai sai da ya fita sannan ta bar ƙofar ɗakin, amma Inna a ranta ta ci alwashin yau sai ta kai ƙara wajen alwalin ta wato Mai Gari.
Haka kowa ya kama sabgar gabansa, Duduwa kishiyar Jummai ce ta yi É—umame ta kaiwa Inna,, haka yaran Jummai suka tare a É—akin Inna suna ta murna Inna mai kayan miya ta zama amaryar babansu, haka ta É—auki tsiran nan ta raba musu.
Jummai kuwa wata kaza ta kama aka yanka ta gyara ta dafa, ta juye a kwano ta bayar aka kaiwa Mai Gari ba tare sa kowa ya san wanda aka kaiwa ba.
Dama ta san a rina wai an saci zanin mahaukaciya ta san dole ta amsa kiran Mai Gari yau, shi ya sa ta yi riga malam masallaci, ta dafa kaza ta aika masa saboda toshiyar baki da kuma cikar burinta.
Wajen ƙarfe goma aka aiko kiran Jummai daga fadar Mai Gari, haka ta tarar da Inna da Sule a can, bayan ta zauna Mai Gari ya kalli Inna ya ce
"Tasallah wai lafiya kike ta tagumi kina cika kina batsewa?" A ƙufule ta ce
"Haba Mai Gari ya kake so in yi to? Ko baka ji a akan abin da muke ƙaran Jummai ba"
Mai Gari ya ce
"Na sani mana"
Inna ta É—ora da faÉ—in
"To wannan ne dai ai ka ji kan maganar, amarcu dai daren jiya bai ciyu ba" Ta faÉ—a tana gallawa Jummai harara. Amma buÉ—ar bakin Mai Gari sai ya ce
"To ai Jummai ta fiku gaskiya" Sule da Inna suka kalli juna suka kalli Mai Gari, Jummai ta saki wani murmushi, don ta san tabbas Mai Gari ya ji daÉ—in dahuwar kalwar da ta yi masa wacce ta sha farin maggi.
Nan ya shiga faÉ—in dole a bi abin da Jummai ta ce har zuwa dawowar Ibra wannan shi ne adalci. Kowa ya ji ba a kyauta amma amma mai gari in ya tuna dabgen kazar da ya ci da sanyin safiyar nan sai ya ji ba zai iya musawa Jummai ba
An yanke hukunci a kan Inna ta zauna a É—akin Jummai takaici kamar ya kashe Sule, Inna kuwa ba a magana, haka aka tashi daga fada kowa yana jimami ban da Jummai da ta san amasar tambayar.
Tsawon kwana biyar Inna tana kwana a É—akin Jummai, saboda yanzu an kasa kwana ma tsakanin Duduwa da Jummai amma ban da Inna Tasallah. Yau da ya kama alhamis tun da yamma Jummai take gyare gyare sannan kuma Inna tana lura da magungunan mata da take sha, sai dai kuma ta san yau bakin Duduwa ne ba na Jummai ba.
Abin da ya ba Inna mamaki yau yaran ba a É—akin za su kwana ba, tun da wurin ta musu shimfiÉ—a a wani É—aki da ake ajiye tarkace ta gyara musu tas.
Tsakanin Inna da Sule sai gani daga nesa Jummai ta kasa ta tsare duk da Inna ta ci wani alwashi da zai rusa duk wani shirin Jummai, saboda tana ta ayyana yadda za ta zamewa Jummai ƙadangaren bakin tulu.
Haka ta ga an gyara ɗakin, gadon ta hau ta kwanta, ita ma Jummai ta hau. Tsakiyar dare Inna tana bacci sai ta ji an dafa mata kafaɗa ranta fari ƙal ta buɗe idanu tunanin ta ko Sule ne, amma abin mamaki sai ta ji Jummai ce, Jummai ta ce
"Inna tashi matata" Idanu Inna ta zaro tana tunanin ko ta yi makuwa ne amma saj ta ji da gaske take, cike da mamaki ta ce
"Mai kike cewa Jummai?"
Jummai ta ce
"Tashi za ki yi ki biya ni sadakina"
Inna ta ce
"Na ce miki sai Ibra ya za a biya ki"
"
Jummai ta ce
"Ai kin san a birni an ce akwai abin da ake yi mace tana auran mace to nima yanzu kin zama matata, don haka dole ki bani haƙƙina" Ta faɗa tana farwar zanin Inna, sai ga zanin Inna an warɓar gefe sai ɗan tofin ta(Skirt ɗin ciki)
A take Inna ta tuna da ana cewa ana lalata mace da mace in bata manta ba an ce hakan yana faruwa a gaske to yaushe Jummai ta zama a haka ba a sami ba, a take Inna ta hau ihu tana cewa
",Ihu kwartuwa, Sule taho ka ga marar imanin nan za ta mini fyaÉ—e...
*MUMMY*
Babu wanda zai gane ko ya iya fasalta yadda tanji wani abu ya caki ƙahon zuciyarta, jikinta ne ya hau karkarwa a lokacin da ta yi wa idanunta masauki a kan fuskar yarinya, ko daga bacci ta tashi tabbas ba za ta kasa shaida Zainab Zee ba ƙawar ƴarta. Hannu ta saka ta dafe bango ɗaya hannun tana nuna su da yatsa.
Duk rikicewar Hajiya Daddy ya fi ta rikicewa saboda shi ji ya yi wani irin tsoro da fargaba a masa dirar mikiya, bai taɓa zato ko mafarkin wannan rana ba, kenan duk wannan sirrin da yake binnewa ya aka yi Hajiya ta sani.
Mummy kanta ne ya shiga juyawa, a take ta yanke jiki yaraf ta zube a ƙasa, Alhaji ne ya yi kanta yana kiran sunanta, ita kuma Zee ganin yadda duk ya birkice sai take ganin kamar ya fi son matarsa a kanta ita a nata ganin tun da ba zaman dadiro ne suke yi ba, ai ba komai ba ne don Mummyn ta sani, ita a ranta ma daɗi ta ji doin za ta saki jiki ta yi rayuwarta son ranta, duk da ta san dai yanzu tun da Hajiya ta sani da wuya ta ci gaba da samun Daddy a ɓagas kamar a baya da kullum ma yake mallakin ta, babu ranar bakin ta babu na Hajiya.
Haka ya kira mai gadi ya fito da mota shi kuma ya kinkimo Hajiya ya saka a motar Zee kuma ganin yana rawar ƙafa kawai sai ta ce ita banu inda za ta je.
Asibiti ya kai Hajiyar inda aka shiga bata taimakon gaggawa.
Bata farfaɗo ba sai wajen asuba, ta falko da kiran sunan Rahma, Daddy yana riƙe da hannun ta ko da ta kalle shi sai abin da ya wakana jiya ya dawo mata a take ta warce hannunta tana fashewa da kuka.
Misalin ƙarfe bakwai aka sallame su, amma Hajiya ta ƙi shiga motar ta hau napep duk da cewa Daddyn yana tabbayar mata cewa ba fasiƙanci yake yi ba matarsa ce ta sunna.
A ganinta ya ci amanar ta tun da ya yi aure matar har da ciki.
Daddy yana bin bayan napep É—in da take ciki har suka je gida, ko parking bai gama ba ya kashe motar ya fito shi ya sallami mai napep É—in ma ta hanyar masa transper tun da bai fita da kuÉ—i ba.
Yana shiga falon ya haura sama kasancewar bai ganta a ƙasa ba, zaune ya tarar da ita a ɗakinta a bakin gado tana ta faman rasgar kuka Rahma tana bata haƙuri, duk da Mummy ta mata bayani amma ta ji haushin Daddy da kuma Zee da ta auri ubanta.
Daddy yana shigowa Rahma wani takaici ya cika mata zuciyarta, a take ta yi ƙunci, fita ta yi daga ɗakin ta shiga ɗakinta ta kwanta a kan gado ta fashe da kuka, tunanin ta ɗaya yadda mahaifinta ya auri ƙawarta yanzu abin da ya tsaye mata a rai wai har Zee tana ɗauke da cikin mahaifin nata kenan Zee ta ga Daddyn ta babu kaya a jikin sa har wani abu yana shiga tsakani.
Mummy kuwa ko sauraren sa bata yi ba ta ce ya fita mata a É—aki, haka ya fita yana tunanin gwara ya bari idan ta huce ya yi aikin lallashin.