Sashe 5
Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lami matar Sheik tun daga lokacin da ya tafi take cike da tsammanin jiran dawowarsa, tana son idan ya kawo kuɗin nan ta ɗauki nata ta mayarwa mai saniya nata, shi ma Ibran ta sammasa wani abu daga ciki saboda ta san shi da idon son naira. Tun bayan sallar la'asar motocin kasuwa suka fara dawowa, tun daga lokacin take ta sintiri wajen da motocin suke sauka amma duk motar da ta kawo mutane bata samub mijinta a ciki,duk sai ta shiga damuwa tana fatan dai ba saniyar ce bata siyu ba, ko kuma ta ƙi yin daraja shi ya sa bai dawo da wuri ba, duk da ta san ta faɗa masa ya siyar ko ma nawa ne ita ba asarar ta bane indai ta ɗauki kuɗinta. Dab da magriba tana tsaye riƙe da tsantsa ta rasa mai yake mata daɗi, don zuwa lokacin hankalinta ya fara tashi, tana tsaye kamar daga sama sai ta ji an fisgi kafaɗarta, juyowarta ke da wuya idanunta ya sauka a kan Jummai tudun adashe, tana wani muzurai sai huci take kamar kububuwa.
Rai Lami ta haÉ—e itama tana aika mata harara, cike da masifa Jummai ta ce
"Lami ashe baki da hankali ashe tunanin yara ne da ke, saniyar marayun kike je kika kunce? Ina kika kaita, kin san dai tsohon mijina da ya mutu gadon ƴaƴana da aka bani na saya saniyar nan tun tana ƙanƙanuwa na kiwata musu ita, a kan wani kuɗin adashe ki je ki since mini ita?" Ta faɗa tana dawowa gaban Lami har zanin Jummai yana neman kuncewa ta gyara. Kallon ko in kula Lami ta jefe ta da shi ta ce
"Wato kuÉ—in adashe ba kuÉ—i bane ko? Saniyar marayu ita ce abun kirki da tattalawa... Katse ta Jummai ta yi da cewa
"Ni ba wannan ba mu je ki bani saniyar nan tun muna mu biyu kin dan dai ta marayu ce na faÉ—a miki" Wata dariyar rainin wayo Lami ta yi ta ce
"To sai su ɗauki na annabawa, ki jira dawowar Ibra mijina daga kasuwa in ya kawo kuɗin saniyar sai in ɗauki kuɗin adashena in baki ragowar in ya so sai ki sayi wata ƙaramar ki kiw... Tun kafin Lami ta ƙarasa Jummai ta wani zaro idanu tana dafe ƙirji ta ce.
"Kanki É—aya kuwa Lami?Saniyar kika bada aka kai kasuwa?" Ta faÉ—a cike da takaici dama dawowar ta kenan, aka faÉ—a mata ko gida bata je ba ta kama hanyar gidan Lamin shi ne ta hange ta tsaye.
"Ras kuwa, ai da nake kai miki kuɗin zubin adashen kike karɓewa baki taɓa sanin kaina ɗaya ne ko ba ɗaya ba sai yanzu da na ɗauki saniya" Masifa Jummai ta shiga yi tamkar za ta hau Lami fa duka, ita ma da ba kanwar lasa ba suka haɗu suna yi har mutane suka fara taruwa ana basu haƙuri, Jummai tana cewa ko Ibran ya dawo da kuɗin daga kasuwa sai ya koma ita saniyar ta kawai ta sani.
Wani dattijo yaa basu haƙuri a kan a jira Ibra ya dawo amma har motar ƙarshe ta kasuwa ta dawo amma babu Ibra a ciki, nan hankalin Lami ya tashi don ta fara wani tunani da ban, sai da ta samu wani direban motar shanayen da Ibra ya shiga ta tambaye shi, nan yake ce mata suna sauka a kasuwa ko cikin kasuwa Ibra bai shiga da saniya ba, aka fara tayawa, nan ya samu wani ya saya ya bashi kuɗin don har la'ada ya bayar.Ya ce wata mota ma Ibra ya shiga, don a yanayinsa ma bashi da niyyar komawa Mai Mangwaro. Jummai kamar ta yi hauka sai zage-zafe da tsinuwa take, amma kuma tana riƙe da mayafin Lami a kan cewa ƙafar Lami ƙafarta sai ta nemo Saniya, magana ya girmama har gaban mai gari.
Bayan an faɗawa mai gari komai, sai ya rasa ma yadda za a yi da Ibra tun da komai dai na maganar yana hannunsa, don haka sai mai gari ya aika wani yaro ya zo da Tasallah kakar Ibra, yaron da zuwansa ya samu Inna Tasallah tana kwance a kan tabarma daga yin sallar isha'i ta ɓingire a kan sallayar. Sallamar da saurayin yake rafkawa ita ta falkar da ita daga ɗan baccin da ya ɗauke ta.
Bayan ya gaishe ta ya ce
"Inna saƙon kira ne daga fadar mai gari" Inna warai ta ware daga ɗan baccin, tana zaro ido da mamaki ta ce
"Idirisu Allah sa dai lafiya, ya za a yi a ce mau gari yana kirana da wannan daren?" Idrisu ya ce
"Inna Ibra ne dai yake son tada miki zaune tsaye, ya karɓi saniya a wajen Lami, kuma saniyar ta Jummai ce, kasuwa Lami ta ce ya kai ya siyar amma har kowa na kasuwa ya dawo amma babu Ibra, yanzu dai suna can gufane a gaban mai gari Jummau ta ce sai an biyata" Salati Inna Tasallah ta shiga zabgawa tana tafa hannuwa ta ce
"Wannan yaro an yi taƙadari, yanzu Ibra ina zai je da saniyar mutane, a ce mutum ya girma bai san ya girma ba, yanzu a ce mutum da iyalinsa shi ba wani yaro ba amma sai jan rigima, ni yanzu ai ni ya tsunduma a masifa, ni da ko kaza bani da ita, wallahi Ibra albasa bata yi halin ruwa ba, iyayensa mutanen kirki ne amma tun da suka mutu nake jigila da shi, tun yana yaro bai barni na huta ba" Ta faɗa tana fashewa da kuka irin na tsofaffi.
Haƙuri Idrisu ya shiga bata, taba goge idanu tana face hanci ta shiga ɗaki jim kaɗan ta fito da wata roba mai ɗan girma tana riƙe da ita, waje suka fito ta saka mukulli ta kulli gidan, suka farw tafiya ta shiga faɗin
"Wannan kalwa da barkonon da kuka da suke cikin robar wannan su kaɗai ne mallakina a duniyar nan, su nake kira suke amsawa, yau ban da cinikin naira ɗari ban yi ciniki ba, ita ma ɗarin gata nan a cikin robar, idan mun je ko da an buƙaci wani abu daga gareni in biya kuɗin saniyar sai in juyewa mai gari wanann kayan don su kaɗai ne da ni.
*GIDAN ALHAJI ADNAN JIBO*
Hajiya Nuritya ce zaune a tangameman falon ta da ya gaji da kayan alatu, tana zaune ta harɗe ƙafafunta hannunta riƙe da waya ƙirar iphone 16 pro mx sai wani ɗan yatsina fuska take lokaci zuwa lokaci. Shigowar mai aiki falon ɗauke da tire wanda aka ɗora plate da ta yanka kayan marmari, ko sallamar da ta yi bata amsa ba, haka ta ƙarasa gaban Hajiya Nuriyya ta durƙusa ta ajiye tiren tana mai cewa
"Barka da hutawa Hajiya, na kammala yankawa" Shiru Hajiya ta yi bata amsa ba, kamar ba za ta yi magana ba zuwa can ba tare da ta kalli mai aikin ba ta ce
"Ki je ɗakin Rahma ki sanar da ita kin gama yanka mata" Da to ta amsa cike da girmamawa, sama ta haura ta je ƙofar ɗakin ta tsaya, tana tsoron ta ƙwanƙwasa ta yi laifi, amma haka ta daure son babu yadda za ta iya tun da in bata sanar da ita ba ɗin ma, laifin ne gwara dai ta sanar ɗin.
Kamar tana jin tsoro haka ta shiga ƙwanƙwasawa a hankali, duk don gudun laifi" Sau biyu kawai ta buga sai ta dakata tana jiran jin amsa, tun da ta san dai in har idanun Rahma biyu to tabbas za ta ji bugun sai dai amsar ce sai an kai ruwa rana.
Sai da ta É—auki kimanin minti biyu zuwa uku tana jira sannan ne cikin muryar Rahma mai sanyi ta ce
"Waye?" Cike da girmamawa ta ce
"Ni ce Hajiya ta ce an gama yanka kayan marmarin"
Cike da izza Rahma ta ce
"Na ji" Baki mai aiki ta taɓe tamkar Rahma tana ganinta, juyowa ta yi ta bar ƙofar ɗakin, tana zuwa ta sanar da Hajia ta fita don zuwa ta cigaba da aikinta.
Sai bayan kamar minti goma sha biyar, sai ga wata kyakkyawar budurwa wacce ba za ta fi shekaru ashirin ba kuma ba za ta gaza shekara sha tara ba, tana tafiya kamar bata so, sanye take da fararen kaya tas riga da wando a jikin gaban rigar an yi zanen heart da pink colour, sai aka rubuta BEAUTY.
Kyakkawa ce ajin farko, sai dai bata da ƙiba, ƙarasowa ta yi ta zauna a kusa da Hajiya Nuriyya, Hajiya cike da soyayya da son nuna kulawa ga tilon ƴar tata, ta ajiye wayar hannun, ta mayar da hankalin ta kanta ta ce
"Mai kike so ne eh baby nah?" Ta tamabaya tana kallonta cike da soyayya.
ÆŠan yatsina fuska ta yi tana É—an tura baki ta ce
"Fruit É—in ne ba zan iya ci ba" Ta faÉ—a cikin muryar sangartattun yara.
Murmushi Hajia ta yj ta ɗakko ta shiga bata, suna cikin haka sai Alhaji da Yaya Ma'aruf suka yi sallama suka shigo, Yaya Ma'aruf ɗan gidan yayan Alhajin ne a ƙauye yake shi ne ya zo karatu birni ya sauka a gida ƙanin mahaifin nasa.
Yaya Ma'aruf mutum mai ibada da kula da addini, yana son ganin mutum yana riƙo da sallah, sai dai kuma ya sauka a gidan kawunsa inda yake ganin ana wata rayuwa ta da ban.
Da gudu Rahma ta tashi ta je ta rungune mahaifinta tana cewa
"Oyoyo Daddy nah" Yana nuna farin cikinsa ya raba ta da jikinsa yana riƙe da hannunta yake cewa
"Oyoyo baby fatan kin ci abinci" ÆŠan tura baki ta yi ta ce
"Ban son cin abinci yau Daddy fruit nake ci" Murmushi ya yi yana riƙe da ita suka ƙarasa tsakiyar falon.
Yaya Ma'aruf cike da girmamawa ya shiga gaishe da Hajiya, amma ta amsa kamar bata so, don ita har yanzu kallon wanda bai waye ba take masa, kallon baƙauye, ita dama ba don dai ɗan gidan ƙanin mijinta bane kuma mijinta yana jin maganar Yayansa da tuni ta kore shi daga gidan.