Sashe 1
Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[6/25, 4:05 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J
👳ðŸ»â€â™‚ï¸ *MALAMIN BOGI*👳ðŸ»â€â™‚ï¸
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.ðŸ“
Daga marubuciyar:
Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*
BOOK1ï¸âƒ£
PAGE 1
Mashin ne yake tafiya a hankali, mutane biyu ne a kan mashin ɗin, mai tuƙawa sai kuma wani farin mutumi wanda yake sanye da jallabiyar fara tas da hular larabawa sai hirami rataye a wuyansa.
Tun da suka shigo cikin ƙauyen Ƙundu, mutane suka zubawa mashin ɗin ido ba komai suke kallo ba sai wanda yake goye a bayan mashin ɗin. A tsakiyar garin mashin ɗin ya tsaya kusa da wata majalisa da mutane suke zazzaune. Sakkowa mutumin ya yi yana rataye da wata jaka a kafaɗarsa inda mai mashin ɗin yake miƙo masa jakar da ya ɗora masa a gaban mashin wacce da alama kayansa ne a ciki. Cikin wata murya mai taushi da yake furta hausa kamar ɗan koyo amma cikin furucin akwai ƙalƙala na larabci ya ce
"Nawa ne kuɗin" Mai mashin ɗin ya faɗa masa, amma maimakon ya bashi abin da ya faɗa sai ya fito da kuɗi mai yawa daga aljihun ya miƙa masa ya ce ya ɗauki kuɗinsa, yana mai cewa
"Wannan kuɗin ma sai da na iso nigeri'a na yi canji, ban san ya lissafin kuɗin yake ba" Ya faɗa yana ɗan shafa lallausan gashin kansa wanda yake haɗe da saje suna sheƙi kana gani ka ga balarabe usul.
Bayan mai mashin ya ɗauki kuɗinsa ya miƙa masa sauran, ɗauke da jakarsa ya nufi wajen majalissar nan cikin hausar mai kamar larabci ya ce
"Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh ya ahlu hazihil ƙarya" Ya faɗa yana ɗaga musu hannunsa da yake saƙale da carbi yana ja. Duk suka mayar da hankali kansa, suna amsa masa a tare, hannu ya shiga miƙa musu suna musabiha kowa yana jin daɗin gaisawa da balarabe farar fata.
Cike da É—an girmamawa ya ce yana son a kai shi gidan shugaban garin, nan wani ya masa jagora yana cewa gidan mai gari. Balaraben nan yana faÉ—in
"Ayyuwa, mafi mushkila" Da haka suka kama hanyar gidan mai gari, kasancewar yammaci ne, sai suka samu majalisar mai gari a cike da jama,a ana fadanci, mai gari yana zaune ya ƙwame a kan kujera. Ganin farin mutumin nan yana biye da ɗaya daga cikin mutanen ƙauyen sai kowa ya zubo masa idanu, amma bai karaya da kallon ba, ya maje yana ɗan murmushi mai bayyana haƙoransa wanda suke ɗauke da haƙorin makka guda biyu.
Mai gari kuwa ya saki baki da idanu yana bin mutumin da kallo, shi in ba a waya ba idan ana nuna hoton ka'aba da yake ganin fararen fata, sai ya ce bai taɓa ganin farin mutum kamar wannan ba. Tun kan su yi magana, mai gari ya yi ƙarfin halin faɗin
"Audu daga una ka samo balaraben mutum?" Ya faɗa yana kallon wanda ya rako baƙon. Audu ya hau masa bayanin cewa yanzu aka sauke shi a mashin, kuma wajen mai garin ya buƙaci a kawo shi. Mai gari ya hau faɗin cewa jama'a su matsa su ba mutumin waje, haka Audu ya ajiye jakar a gefe ya koma gefe ya tsaya, suka zubawa baƙo na mujiya.
Mai gari ya kalli baƙo ya ce
"Barka da zuwa Malam, daga ina kuma wajen wa ka zo" Ya faɗa yana kallonsa, har mai gari ya fara tunanin ya fara yi wa baƙon maganar bebaye, don sai ya yi tunanin ko ba ya jin hausa, amma dai ya san tun da har Audu ya ce ya faɗa musu wajen mai garin zai zo to tabbas yana jin hausa.
Har ya ɗauke tsammani sai ya ji baƙo ya yi gyaran murya, ya ciro jakarsa ya ta rataye,
Shek ya É—an sunkuya kaÉ—an, yana murmushi da kamun kai ya ce
“Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu
“Ni sunana Sheikh Abu Abdurrahman Al-Yamanini É—an Yemen ne daga Al-Mukalla. An turo ni nan Najeriya domin taimakawa al’umma wajen magance matsalolin da suka shafi ruÆ™iyya ta shaiÉ—anun aljannu, da cututtuka na zuciya da jiki.â€
“Na karanci ilimin hadisi da ruÆ™iyya tun ina É—an shekara 9, kuma Alhamdulillah, na yi aiki a masallacin Umar bin Khattab a can Æ™asarmu.â€
“Ban zo nan domin neman duniya ba, sai dai in taimaka da abin da Allah ya bani. Na riga na shirya tsari na musamman da za a gudanar da ruƙiyya ta jama’a kowace da kuma maganin mantuwa, ruɗu da zalunci" Ya faɗa yana ɗorawa da faɗin
“Na riga na fara shirya ruwan da aka karanta masa ayatul kursiyyu da suratul jinn sau 70. Da yardar Allah, wannan ƙauye zai zama mai kwanciyar hankali, dama na samu labarin matsalolin garin nan ne a wajen wani bawan Allah, a inda ya mini kwatance aka sako ni a hanya don na zo na taimaka"
“Wannan hidima kyauta ce, sai dai idan wanda aka warkar ya ga dama ya kawo sadaka... kamar yadda ake yi a Yemen!â€
Yana sunkuyar da kai, jama’ar wurin suna cewa "Allahu Akbar!"
Mai Gari yana gyara rawani da kallon mutanensa ya ce
“Wallahi wannan ba Æ™aramin bako bane, jama'a ku kalli yanda yake fari kamar an wanke shi da ruwan zamzam!â€
Ya cigaba da faÉ—in
“Ka ce Yemen? To wannan kauyen namu na Ƙundu bai taɓa samun baƙo daga ƙasar larabawa ba. Kai ne farko, to tabbas alheri ya shigo ƙauyen Ƙundu da yammacun nan!†Ya ce ba tare da ya jira cewar kowa ba ya ɗora da faɗin
“Mun dade muna fama da matsaloli, mazajen da suka daina kataɓus a wajen matansu, matan da suke magana da kansu, kawai ka ga zabgegiyar mace ta dage tana zance ita kaɗai, yaran da suke kuka ba dalili ba dare ba rana sy damu jama'a muna ta zargin shaiɗanun aljannun nan ne suke buɗe musu maganai(Idanu) Amma yanzu Allah ya kawo mana ƙare kukan ka muna yi wa Allah godiya" Ya kai ƙarshen jawabin yana juyawa ga mutanen da suke kewaye da shi, wanda dama asali a wajen suke zaune da wanda suka zo daga baya.
Ya ce daga yau, Sheikh Al-Yamani zai zauna da mu, za a bashi ɗakin baƙi na gidan baƙina da sannan za a riƙa kai masa tuwo da dare da ɗumamen safe, da rana za a kai masa dambu ko fura ni a matsayina na Mai Gari na ɗauki wannan nauyin†Ya ce yana gyaran zaman rawaninsa, don a nasa ganin ya ƙure iya ƙurewa.
A ɓangaren mutanen wajen suna jinjinawa Mai Gari bisa namijin ƙoƙarin da ya yi, amma a zucuyar Sheik ba haka bane, ransa ne ya ɓaci jin an ambaci tuwo da dambu, saboda ba zai lamunta ba, ya baro tuwo a ƙauyensu sannan yanzu ma yake fama da tuwo da dambu.
Kai ya É—ago yana faÉ—in
"Ma sha Allah, Alhamdulillahi hamdan-hamdan, sakallahu bil kairi" Mai Gari ya washe baki don furucin balaraben kaɗai ya masa nuna da cewa baƙon ya jinjina masa.
Don haka cike da ƙarfin gwiwa ya dubi jama'a ya ce kun ji sai larabceni yake yana mini addu'a wataƙila har da addu'ar zuwa makkah ya mini" Jama'ar garin kasancewar jahilci ya musu katutu suka hau gyaɗa kai, balarabe kuwa a ransa ya ce
'Tashin hankali gobarar gemu, wallahi in na yarda da wannan wawancin in nutse a wajen nan, dole in nemawa kaina mafitar cin daɗi ko na murmure, a kan me zan zo in ke ruƙiyya da ƙarfin tuwo da dambu, wallahi dole na samarwa kaina ƴanci daga cin tuwo da dambu' A fili kuma ya ce
"Liy su'alun(Ina da tambaya) Ya faɗa yana ɗaga yatsa, duk da basu san mai ya ce ba, don shi ma kansa ba wai ya ƙware bane a larabcin, larabci ne na ƙarfin hali da ya zauna yake koya a wajen wani saurayi, sannan a ƙamus na larabci mai fassarar hausa yake ƙara samun ƙwarewa.
Mai Gari cike da ɗan razana yake kallon baƙon balaraben nasu, don bai san wannan larabcin da ya yi ba cike da ƙarfin hali ya yi namijin ƙoƙarin faɗin
"Ya Sheik, mene ne sussu,aliy(Liy su'alun yake nufi).
Balarabe ya ce
"Ina nufin ina da tambaya" Murmushi ya yi ya ce a zuciyarsa
'Allah sa dai ba wata tambayar ƴar ƙure zai mini ba, ni da ko bihim ban sani ba a yaren larabci, kai ko cewa aka yi zo in kashe ka Mai Gari ba sani na yi ba' A fili kuma sai ya ce
"Allah sarki mene ne tambayar?" Baƙo ya ce
"Na ji ka ce za a ke bani tiwi da dimbo(Tuwo da dambu yake nufi, amma cikin ƙalƙalar larabcin rainin hankalinsa ya ce tiwi da dimbo shi a dole bai san tuwo ba.
Shiru Mai Gari ya yi don bai fahimci komai ba, sai da Audu wanda ya rako baƙon da yake ya fahimci manufar Sheik sai ya ce
"Yana tambayar tuwo da dambu" Mamaki ya so kama Mai Gari amma kuma da ya yi tunanin baƙon daga ƙasar waje yake ta larabawa sai ya ce
"Ikon Allah na kwance ya faɗi, wallahi an samu akasin lissafi Malam abincinmu ne na hausawa, mu nan duk wanda bai san tuwo ba sai muke ganin kamar saɓo ma ya yi, don shi muka ci muka girma kuma shi muke ci har yanzu"
Ya Sheik ya É—an yatsina fuska ya ce
" La a'alamu hazihil ism(Ban san wannan sunan ba) Shiru Mai Gari ya yi yana tunanin kar baƙon ya ɓaro masa wani gagarumin abu tun da shi ya ce zai ke ciyar da shi saboda bajinta.
Sheik ya ce
"Mu a namu ƙasa dajaja wato kaza safe da rana dare sai mutum ya ci, kuma muna shan shayi mai kauri wanda madara ta isa sosai, bama cin komai bayan wannan sai shimkafa ƴar gwamnati ta buhu" Ya faɗa yana ɗago carbi ya shiga ja.
Mai Gari gumi ya shiga haÉ—awa, kasancewar duk kiwon da ake a gidansa ba a ci ko tattabara ba a ci bare kaza, idan har an yi yanja a shekara ne ake layya da sallah, shi ma gudun jama'ar gari su yi da shi, suke ganin yana shugaba bai yanka ba.