← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 109

Sashe 99

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin bacci taji ana shafa mata fuska, kafin gently taji anja lips dinta, ahankali take bude idanunta, fuskan Asad tagani dab danata yana kallonta tanajin saukan numfashin shi akan fuskanta, juyamai idanunta tayi tareda murguda baki ta yunkuro taredasa hannunta tana tureshi tai magana ciki ciki tace "ni kadena sani agaba kana kallo tom, ina Mum dina"? tai maganan tana kalle kalle ganin babu kowa acikin jirgin, saikuma tajuyo takalleshi dasauri yanda yake binta da kallo tace "munkawo" gyadamata kai yayi yana mikewa tsaye yace "let's go" yay hanyar fita tabishi abaya dasauri, wani dogon jeep tagani dayayi kusan jirgin atsayi, bude mata kofa Asad yayi ahankali yana kallonta, ahankali tafara saukowa tana kalle kalle garin sanyi na bala'in dataji yana shiganta har cikin kashi dudda abayan dake jikinta, dawani sauri tasauko tazo ta shige mota jikinta narawa ta zauna kusada Ammi, wani bargo Ammi tadauka ta rufa mata tace "sannu kinji sanyi ko" gyadamata kai tayi tace "Mum kaman kankara" dan dariya Ammi tayi tana satan kallon Asad dake daddanna waya yana zaune kusada Sharif tace "su tun October ake fara musu sanyi mukakai gida saiki wanka da ruwan zafi" shiru tayi ahaka sukakai wani hadadden anguwan taga sun shiga wani gida haka dan madaidaici dan baikai gidansu na Abuja girma ba saidai gidan yahadu exactly ginin kasan waje, fiffitowa akai daga motan Ammi na rikeda hannun Du'a tace "muje kiga gidanmu na nan, anan gidan Asad ya zauna dayana karatu anan kasa, gidanshi ne ma, wanan ne gidan da Baban ku yabashi kyauta dazai fara university" dan murmushi Du'a tayi suka shiga gidan tana kalle kalle, gidan ko'ina plants da flowers kaman gidan da ake saida fulawowi, murmushi Ammi tayi tace "mijinki nada this wired hubby yanason flowers bakiga ko gidan ki akwaisu burjik ba, he always grows flowers aduk inda yake, kuma jibi yanda suka karama gidan kyau" tai maganan tana danna door bell na falon, saiga wani namiji da uniform yabude kofan cikin turencin su yace "welcome Ma'am".

8️⃣3️⃣

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

M Shakur

NOW LET'S TALK.
Haba Anty wanan handbag dinan naki, da takalmin nan naki, da zanin gadon nan naki duk sun tsufa suna bukatan chanji, kinkosan M Shakur nasaida jakunkuna, takalma dakuma zannuwan gado hadaddun gaske???
yi maza kiyi saving number M Shakur sanan kimin magana nima na seva naki domin dinga ganin tallan zannuwan gado, takalma da jakunkuna a status dina.....ku garzaya agurguje kuyi saving number na sanan kumin magana sabida nima nai saving akwai wani hugeeee giveaway dazanyi na jaka, takalmi dakuma zanin gado.

Ga number na nan 07012181461.

you can also chat me up directly by clicking on this link
wa.me/+2347012181461

Oya asaurara aji!
Wanan February zan fara group din Matan aure wanda nasaba yi last month ne kawai banyiba sabida this novel wanda zan gamashi before this month end.

Group din Matan auren na group ne danake koyarda ilimi na zamanta kewan aure, ilimin dazai amfaneki wajen haukata Oga akan gado, ki iya different styles, da abubuwa da dama na gyara jikinki, dakuma yanda zaki gyara jikin mijinki ta yanda zakiji dadin shi.

Inayin classes din Saturday and Sunday of kowani sati ne.

Idan kinason ki shiga group din registration is 1k kacha.

Zaki turo ta 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turomin evidence of payment sainai adding naki a group din.

Murmushi Ammi tayi tashiga su Dr da Dad biyeda ita, Asad na gungura Dad awani hadadden keken guragu abaya ahankali, suka shiga falon, Babban gidane sosai gashinan oyinbo settings, ana shiga falon Dad yadago kanshi yakalli Asad yace "dakuna nawane a sama"? Asad na kallon fuskanshi yace "guda biyar ne Dad" wani kalan makale murya yayi kaman wanda ya riga yay giving up rayuwa sanan yadaga hannunshi yana kama na Asad yace "son kainake so ka zauna dani, sabida kaine zaka iyamin komi kaga mahaifitarka ita kanta tana bukatan hutu, sai Dr abashi daki daya, Sharif daki daya, sai daki daya Ammin ka da Du'a kaji" kowa kallon Abba yake, wani abu Asad yahadiye awuya harga Allah baiji dadi ba ko kadan ahankali yace "okay Abba" kaman daga sama sukaji Sharif yace "Dad nizan zauna dakai, inyaso Asad sai abashi daki daya da matarshi ko Dad" wani kalan kallo Dad yama Sharif kaman yatashi yadaba mai wuka aciki yakeji da kyar yadaure yahadiye fushin sanan ahankali muryanshi narawa sosai yace "ohhh.....I am sorry....I think I am being selfish here, namanta Asad yay aure yanada mata" dago kanshi yayi ahankali da idanunshi dasukai jajir sun cika da kwalla yakalli Asad yace "Asad bari Sharif yazauna dani kai kudauki daki daya da matarka" ayanda Dad yay maganan kokai waye sai ranka ya mota ahankali Asad yace "no Dad zan zauna dakai" hannu Dad yabude dasauri yace "hug me my son" zuwa Asad yayi ya rungume shi tsamtsan, at this point Dr yakara tabbatar wa Dad kankat ne kan matar danshi yake wanan haukan lallai, how will this family react idan suka gane mutumin nan lafiyan shi kalau all because of yanason yaci wanan kyakkyawan yarinyar dabama tasan kanta yake wanan haukanba yake all this abubuwan.

Sun dade ahaka sanan Dad yasakeshi yana goge hawaye yakalli Sharif yace "show Dr his room, sweetheart kema kuje dakinku kuhuta ni anan dakin kasa zamu zauna" yay maganan yana nunama Asad wani babban daki dake nan kasa ahankali Asad yaturashi zuwa dakin, Kuku su kuma nashigo da akwatinan su.

Saida suka shiga dakin sanan ahankali Ammi tazaunar da Du'a akan gadon dakin kafin taja kujeran gaban madubi zuwa bakin gadon tazauna sanan takama hannayen Du'a tace "Daughter na listen to me" taidan shiru tareda sakin ma Du'a murmushi sanan tace "nasan anshiga hakkin ku dayawa, aurenku duka duka kwana nawa kuna cikin cin amarci baban ku yahau ciwo and he's all over mijinki baki samin kulawanshi da time dinshi yanda yakamata" dasauri Du'a ta saukar dakanta tace "Mum please kidena maganan nan ni wlh baki shiga hakkina ba kinji na rantse" dan murmushi Ammi tayi ahankali tace "you see ko tun kafin muyi aure da Baban ku he's this man da Allah ya zubamai rakin ciwo, baida dauriya ko kadan jibe fa da girman shi ga yara ga kowa amman zai iya yayta muku kuka idan yana ciwo, he's such a small boy whenever he's sick" tai maganan tana murmushi kafin ahankali tasaki hannun Du'a takai hannayenta kan fuskanta tace "kinga Asad shi kadaine dan da Allah yabashi aduniya, is being long dayay ciwo barin ma cinyon shanye wan jiki, so idan ya makalkale Asad haka yaki barinshi nan da chan is because ganin shi makes him happy and it gives him peace, so dan Allah bear with my son kinji Du'a, don't be angry" ahankali Du'a ta gyadama Ammi kai, rungumeta Ammi ta tashi tayi sanan tasaketa tace "Hajiya tabani assignment na musamman tace in tabbatar kina shan magungunan ki suna jaka, bari a shigo da jakan kina na dare, yanzu tashi kije kiyi wanka kizo kiyi salla sai muci abinci ko" gyadamata kai tayi sanan ta tashi tawuce bathroom.

Wasa wasa haka Dad ya kanannade Asad adaki yaki barinshi fita ko nan da chan, abinci adaki sukaci, salla adaki yayi, bawai yagaji dakula da ubanshi bane a'a inyace haka ai yazama butulu kuma shima nashi yaran zasumai haka, but he just needs a little time da matarshi dan sosai he lacks focus, he lacks peace, baida natsuwa ko kadan, at least ko kadan ma yabarshi yafita yaje yadan tattabata and feel her ajikinshi hakan zaima bashi karfin kula dashi da kyau, but all this thing yasa bayama gane komi da kyau maneji kawai yake, kiri kiri yakasa bacci duk kuma Dad nasane dan yana ganinshi dudda wutan dakin akashe yake but yanajin saukan ijiyan zuciyan shi duk 1min, shi kanshi Dad mamamkin Asad din yake, dan yaga yamafi shi sha'awa dason mace sosai, yaushe duka duka yasan yarinyar amman baya iya bacci, shi wani zubin yana 2days baici mace ba, 3days nedai baya iyawa, kuma yana iya yay bacci shi kadai batare da mace ba amman jibi wanan JJC danshi dinan aiko yaro kashirya bawai zan rabaka da matarka bane but kaida kwanciya tareda yarinyar nan sainaji abinda kaji yasa kamutu ka haukace akanta dinan sainaji dadi da wanan zagin gaban nan nata tukunna, da kyar wajajen 5 bacci yay awon gaba dashi, dagashi har uban nashi sai wajajen 9 Ammi ta shigo ta tadasu da kanta tace "wai ba asibiti zaku ba" wanka sukayi suka shirya sukaci abinci Du'a ko saukowa batayiba Asad sai kallon sama yake, suna gamawa aka tafi dashi asibitin daga Ammi sai Du'a aka bari agida.

Koda sukakai asibitin daga Dr sai Dad suka shiga consulting room din, dan Dr Dady yasan baturen Dr din, akabar Asad da Sharif awaje agabansu aka gungura Dad aka wuce dashi wani daki, ana shiga Dad yace bari nai bacci da kyau abina dariya Dr shi yahauyi, saida yay baccin awa daya cur sanan aka tadashi suka fito, Dr yace "akwai improvement, gobe result zasu su koma gida" tsabagen yanda Asad was totally baya hayyacin shi bayama iya any tambaya regarding ciwon Dad din kawai binsu yake da ido, baima gane abinda neither of the Dr's kefadi haka suka gama suka juyo suka dawo gida Dad yasa shi kaishi daki.
Chapter 99 · 0% Book details