← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 109

Sashe 37

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wuraren 1 as usual Sharif yazo floor dinsu rikeda wayanta daya saita mata komi, knocking office dinta yayi tareda budewa duka at the same time, ganin babu kowa a office din babu jakanta yasa yadanyi kwafa yace "yauma ta tafi masallacin bata jirani ba ko" jan kofan yayi yamaida yarufe yafito daidai Asad yadawo shima daga mosque din yana tafiya ahankali yana gyara zaman necktie dinshi yana kallon Sharif din, tsayawa kusadashi Sharif yayi cikeda tsokana yace "how far kamana order pizzan" hararan Sharif din yayi yace " order with ur money" yay maganan yana wucewa office abinshi shikuma Sharif yahau dariya yawuce elevator yashiga zuwa kasa masallaci yashiga yay alwala yay salla sanan yafito yana kallon wajen ganin babu ita yasa yawuce Canteen dinsu, ganin babu ita awajen ma yasa yay fushi kawai baima tsaya cin abincin ba yawuce floor dinsu yace "nizata share yau duk tai abubuwan ta ita kadai" wayanta ya kalla dake hannunshi yace "she will come get it by her self" ijiye wayan yayi agefe kan table dinshi yacigaba da aikinshi...... Wuraren 3 yakasa hakuri rabon daya ganta tun safe tashi yayi yafito yay sama, office dinta yasake budewa ganin bata ciki yasa yafito yabi ma'aikatan wajen da kallo wucewa yayi yakarasa wajen receptionist din gaban office din Asad yace "have u seen Miss Du'a Patience"? Cikeda girmamawa tace "yes sir naga saukanta" juyawa yayi da sauri yashiga elevator yasauka kasa, shi yasan bata yawo iya kanta masallaci sai Canteen kuma duk tare suke zuwa toko tana restroom din mata ne, hanyar bayi yayi ya tsaya gaban macen security dake wajen yace "dan dubamin miss Du'a aciki" tashi matan tayi tac3 yes sir tashiga taduba tafito tace "babu kowa a rest room sir" shiru yayi yana tunani dan this is strange, daga kai yayi yana kalle kalle ganin receptionist din wajen yasa yakarasa yace "have u seen Miss Du'a"? Gyadamai kai tayi tace "yes Sir dazu naga tazo tawuce tafita tana kaman ma kuka take" dan tsayawa yayi yana kallonta saikuma chan yace "around what time kenan"? Dan shiru tayi kaman tana tunani tace "around eleven na safe" juyawa yayi dasauri cikin fushi yace "Assssadd! What have u done this time" elevator yahsiga zuwa 5th floor, direct office din Asad yashiga dake magana dawani employee dinsu daya kawonai report, kallon employee Sharif yayi yace "excuse us Mr Bashir" "sure sir" yafadi yana tashi yafita sauda yarufo kofan sanan Sharif yakalli Asad babu alamun wasa kaman bashiba yace "ina Du'a Asad? Inaka turata" dan yatsine fuska Asad yayi yana jawo MacBook dinshi zuwa gabanshi yace "wace Du'a"? Cikin fushi Sharif yace "you know what am talking about, yarinyar dakai saving daga rijiya, jikan Hajiya, yarinyar da Ammi tasa kabata aiki, ina take"? Typing abu yashigayi a system dinshi abinci cikin halin I don't care yace "batada any means of identity sanan batada account so I asked her to leave my company duk randa tasamesu she can come back" cikin wani irin bala'in mamaki Sharif yace "you ask her to mene?" yay shiru yana kallon Asad dake harkan gabanshi, cikin wani irin bacin rai yace "Asad kakosan mekayi? Did you know that yarinyar nan batasan ko'ina ba a Abuja ko good 3weeks batayi a Abujan nan ba, tayaya zata koma gida? Look her phone is with me" yanuna wayanta dake hannunshi, dan tabe baki Asad yayi yana aikin dayakeyi a system yace "she's an adult she can take herself home" yanda yake maganan ma yafi komi cima Sharif rai irin ko ajikinshi dinan baimasan yayi wani abuba, cikin mugun fushi dabazai iya tuna the last time dayay irinshi ba yace "wlh katashi kanemo yarinyar nan ina gayama" wanan karan ko kalloma Sharif bai isheshi ba saima hannunshi dayakai yana taba screen din system din yana magana ahankali yace "there's an error in this FIFO calculation......" irin baimasan Sharif nayiba, sosai ran Sharif yabaci wayanshi yaciro ya danna ma Ammi kira yadaura a kunne ringing biyu Ammi tadaga kafinma tai magana yace "Ammi kina ina yanzu haka" cikeda rashin fahimtan abinda Sharif keyi tace "ganinan gidan Hajiya, takirani gwuiwanta naciwo shine na shigo" ahankali yace "Ammi Du'a na gidan" dasauri tace "Du'a kuma, Du'a dake office basai 4 kuke tashi ba, wai yau bakaje office bane" wani irin lumshe ido yayi yabude kirjinshi na bugawa yace "Ammi listen to me zangaya miki wani magana amman banson kice komi dan kar Hajiya tagane dan abinda kunya ace mune mukama jikanta haka" nan yakorama Ammi magana daga A to Z, tsabagen tashin hankali batasan lokacin data fito tsakar gida ba, cikin bala'in bacinrai tace "ina Asad din"? cikin bacinrai Sharif yace "yana zaune anan Ammi ko ajikinshi baimasan yayi abu" cikin fushi sosai tace "bashi wayan" cikin bacin rai yace "ni wlh bazan bashi wayataba saidai ki kirashi ta wayanshi bari naje naduba Nabi hanya kozan ganta" yay maganan yana katse wayan yawuce yafice daga office din straight waje yayi yashiga motanshi yabi hanya.

Wayan Ammi tabida kallo tunda take bata tabajin Sharif yayi fushi hakaba duk cikin yaran shi kadaine baida matsala gashida ban dariya, dialing number Asad tayi, yana zaune ganin Ammi na kiranshi yasa yature system din dake gabanshi yana kallon wayan harta katse bai daukaba, akaro nabiyu ne yamika hannunshi kaman mai tsoron wayan yadauka yakara a kunne baice komiba, cikin fushi sosai Ammi tace "aida itama wanan kiran baka dauka ba goga kaji" taidan shiru hakan yasa ahankali yace "Ammi I just told her to go idan tai national ID da bank saita da......""shut up Asad!" Ammi tadakamai mugun tsawan dashi zai iyacewaka tunda yake arayuwanshi Ammi bata tabamai tsawa hakaba, tace "Asad this is not how I train u wlh billahil azim, Asad where is your heart, Asad how can u asked that girl ta tafi gida yarinyar dabatasan ko'ina ba, kasan yarinyar nan kuwa? Kasan wacece ita? Eh? kasan mesa aka kawota wajen kakanta kasan labarin Du'a kuwa? Do you know what that girl has been through? Asad is this how I trained you? Duk duniyan nan banda Maman data wuce Hajiya Asad you know this morethan anyone matan nan babu abinda batamin ba aduniyan nan, Asad jikan ta zaka wulakanta eh?" jin yanda ran Ammin shi yabaci sai maganganu take awaya yasa yaji duk badadi, ahankali yace "Ammi" cikin fushi tace "don't you dare call me Asad, idan wani abu yasami yarinyar nan tayaya zankalli Hajiya nagayamata d'ane sila eh? Mezata cema iyayen yarinyar nan kasan case din dake kan yarinyar nan kuwa, Asad why are u like this? Maisa baka da imani bakada tausayin mata eh? kanada kannai mata idan wani yakorasu haka kaibamai zuwa kayi fada dashi bane, Asad listen to me if anything should happen to that girl wlh wlh bazan yafemaka ba dan bazan taba iya kara kallon idanun Hajiya ba..." dawani irin sauri yace "Ammi!" cikin fushi tace "yes Asad nasan kalman dana gayamaka, katashi duk inda yarinyar nan tashiga aduniya ka nemota kadawo da ita gida nan dakanka safe and sound inba hakaba wlh saina mugun sabamaka Asad dabazaka gane kaina ba mai bakin hali kawai" Ammi ta katse wayanta cikeda bacin rai tana kallon agogo dan tasan hudu nayi direban Hajiya zaitafi daukota.

TOH GGM DINA🥰🥰🥰 ANAN NAKAWO KARSHEN FREE PAGES THIS LABARI NADA TSAYI YANZU NAMA FARA.
SUBSCRIPTION IS 500 PAY INTO 3107021073 AISHA MUHAMMAD FIRST BANK.

KUJI TSORON ALLAH KUBIYA KADA KU KARANTA BATARE DAKUN BIYABA DAN GASKIYA ALLAH ZAI SAKAMIN.

THANK YOU ❤

Assalamu Alaykum, inaso mu gina al'umma masu tsoron Allah da tsoron hakkin dan uwanshi musulmi, I was very kind and generous nayi pages talatin da daya (31) pages awanan littafin as free, dan Allah kudubi Allah badan niba badan halina ba karku karanta idan baki biya kin shiga group ba, dan idan kikai gaskiya Allah zai bimin hakkina.

Kudin karatun this novel is 500 kacal, pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting.

you can chat me up directly a watsapp by clicking on this link
wa.me/+2347012181461

M SHAKUR

EPISODE 3️⃣2️⃣

Kasa komawa cikin gidan tayi hankalinta yawani tashi gabaki daya number Sharif tai dialing ringing daya yadaga, cikeda damuwa tace "Sharif kafita nemantan kaganta"? Cikeda damuwa yana driving yace "Ammi ni banmasan ina zan dubaba gani nan dai akan titi within office dai ina dudddubawa" cikeda damuwa tace "shikenan In sha Allah nothing will happen to that girl In sha Allah, now inaso ka kira Hajiya kacemata Du'a will stay late akwai aiki zaku dawo da ita anjima, Sharif kunyan gayama Hajiya abinda d'ana yama jikan ta nake wlh just do that okay" ahankali yace "Ammi calm down Hajiya taganki ahaka zama ta zargi wani abu, kitafi gida kawai and relax we will bring Du'a back, nothing will happen to her kinji" asanyaye tace "Allah yamaka albarka Sharif" takatse wayan.

Yadade zaune kan table dinshi yana maimaita kalaman da Ammin shi takirashi dashi, yau Ammi ce ke cewa bazata yafemai ba, Ammi ce kecemai mai bakar zuciya, Ammi bata tabamai fada hakaba, ahankali ya fuzarda iska yamika hannayenshi da kyar yature system din gabanshi sanan yawani irin kife kanshi akan table, kaman wanda aka daka, saida yaji ana kiran sallan laasar sanan yatashi, mikewa tsaye yayi yashiga bathroom dinshi dake cikin office din, alwala yadauro sanan yafito ya tsaya gaban hanger jacket na suit dinshi yasaka sanan yadauki wayanshi da car key daga wajen yawuce fita yayi yasauka kasa saida yafara tsayawa yay sallan laasar sanan yafito daga masallacin tsayawa yayi yana kallon entrance door din shigowa company, shi yanzu ta ina Ammi takeso yafara neman yarinyar nan me eh ta ina?.
Chapter 37 · 0% Book details