← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 109

Sashe 7

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dasauri Mum tace "idan duka zakayi Alhaji ni zaka daka danni nasa Nana tama shegiyan makiran yarinyar nan duka tacire mata riga kannenta sumata ihu" wani irin kallon Mum yake kafin yabi kowana dakin one by one da kallo sanan idanunshi suka sauka kan Mami dake dining tana arranging kula cikin kakkausan murya yace "Zainab kina nan wajen kina tsaye zasu kashe Du'a can't you intervene, wani irin banzan hali ne wanan" juyowa tayi takalli Abba idanunta sunyi ja sosai cike da tsananin kunci tace "Dadyn Hamad mekakeso nayi eh? mekakeso nayi? Ya zanyi da raina?Tun ranan dana tsugunna na haifo wanan yarinyar duniya nake shiga bala'i kala kala? Babu kalan shairin da ba'a yimin ba kan haifo yarinyar nan, tunda na haifi Du'a ban kara samin kwanciyan hankali ba, kome yasameta ita tajama kanta kahanata fita waje ubanme yakaita garden? Gasu gatanan idan suka kasheta kaga kowama yahuta daman tun ranan dana haifota tazamema kowa kashi a wuya ankasa taunata, ankasa fitoda ita, ankasa hadiyeta, nima nagaji I am tired of everything, I'm tired" kawai saiga kuka yazo mata dasauri tabar dinning din tawuce sama tabude dakinta tashiga abinta.

Juyoda kanshi Abba yayi yakalli Mum da Nana dake kuka itama yace "kuwuce kuje kujirani adakina" wucewa sukayi sama, sanan ya kalli yaran yawani daka musu tsawa yace "to your room dukan ku" dasauri kowa na falon ya watse, Abba yajuyo yakalli Hamad yanunamai riganta yace "bani riganta" wucewa yayi yadauko rigan shikuma Abba ya tsugunna yatallabota zuwa jikinshi yana kallon fuskanta yanda goshinta ya kumbura ga bakinta jini, gefen fuskanta yay ja sosai, bashi rigan Hamad yayi Abba ya karba sanan yakama hannunta yasamata rigan kafin yarufe mata kirjinta dashi sanan yaja throw pillow data rufe kanta dashi ya yar sanan yasamata dayan hannun rigan yadagota zai saka mata zip tafashe dawani wahalallen kuka sosai ahankali Abba yace "ina ke miki ciwo"? Cikinta ta nunamai, daga riganta yayi yakalli cikin ga alamun naushi nan duk sunyi jajja, Hamad dake tsaye kansu yace "Abba bazamu kaita hospital ba kuwa what if tanada internal bleeding" girgiza mai kai Abba yayi yace "get me a towel and hot water da rob" wucewan kitchen yayi dasauri yakawo ruwan zafi da towel.

Karba towel din Abba yayi sanan yasa a ruwan zafi yaciro yadaura kan cikinta yana matsamata fashewa da mugun kuka tayi tarike Abba tace "wayyo Abba zafi, Abbbaaaa" sosai ran Abba yabaci kuma yay alkawari saiya mugun sabamata, tun tana kuka yana fitowa harya dena saidai hawaye, saida yagasa harda goshinta da bakinta sanan yashafa mata rub din tass, sanan yakalli Hamad yace "kaje phamarcy and get drugs for her she can't go to hospital" gyadamaikai Hamad yayi sanan yawuce yafita shikuma Abba yatashi daukanta yayi tana jikinshi dantamayi bacci kwantar da ita yayi kan gadonta sanan yasa bargo ya lullubeta yadade tsaye akanta sanan yawuce yafita daga dakin.

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

✍️M SHAKUR

Free page
EPISODE 5️⃣
Dakinshi yawuce, bude kofa yayi yashiga dakin Mum na zaune kan kujera itakuma Nana tana zaune akasa tana share hawaye danhar lokacin kuka take ganin Abba yashigo yasa gabanta yacigaba da faduwa dan gabaki dayansu suna tsoron mahaifinsu danko kadan baida wasa sanan yanada zafi.

Maida kofan yayi yarufe sanan yashigo ciki har lokacin kanta nakasa sanan yawuce yazauna kan kujeranshi yana facing bata, cikin kakkausan murya yace "maiya hadaki da kanwarki Du'a Nana"?Hawayenta tashare cikin sheshekan kuka tace "Abba dazu Muhsin yazo na shimfida mai dadduma a garden shine nakoma nadauko zobo ina zuwa naganshi tareda Du'a....." yanketa Mum tayi tace "fadama Babanku komi kina bobboyemai kikaga dai Du'a ajikinshi" wani irin kallo yama Mum sanan yace "kika kara magana batare danabaki izinin kiyiba wlh saikinyi mamakin abinda zan miki" yajuya yakalli Nana yace "ina jinki" sake share hawaye tayi tace "Abba tarena ganshi da Du'a babuma dan kwali akanta yarikemata hannu yana kokarin tabamata gashi, shine Du'a na ganina tahau kuka wainace yasaken mata hannu, sakinta yayi ta tafi shine yacemin waishi bazai aureni ba wai Du'a yakeso ita zai aura yanzu bayasona waizaije yagayama babanshi" shiru tayi takai bayan hannunta ta goge wasu sababbin hawayen dasuka zubomata.
Gyara zama Abba yayi ranshi amugun bace yana kallonta yace "dago fuskanki ki kalleni nan" girgixa mai kai tayi takasa, hakan yasa yadaka mata tsawa yace "I said look at me" dasauri tadago kanta takalleshi jikinta har bari yake tsabagen tsoro da shakkan Abban ta yace "so sabida namiji ne kike neman kashe blood sister ki, da Allah bai kawoni gidan nanba dayau kinyi kisan kai eh!" yasake dakamata tsawa kana ganin yanda yake maganan kasan ranshi abace yake, yace "to the extend kina ciremata riga exposing your fellow sister body kannenku su ganta, Nana is that how I train you eh answer me" fashewa tayi da kuka sosai tace "Abba kayakuri bazan karaba" girgixa mata kai yayi yace "kece y'ata mace tafarko yau idan namutu I believe kece zaki kula dasauran kannenki u will be their mother but look at what you did today, sabida namiji eh? sabida yace bazai aureki ba and so what zaki kashe yar uwarki ur blood sabida wani eh? Saina hukuntaki sosai Nana, stand up jeki kawomin wayanki, your laptop ki kawomin ATM card dina danabaki" fashewa tayi dakuka sosai dan babu abinda yafi tadamata da hankali irin wayan dawani wayazata kira Muhsin su shirya, ita karan kanta Mum saida ta girgixa amman takasa magana dan taga ranshi inyay dubu yabaci. cikin kuka Nana tace "Abba dan Allah kayakuri nayi kuskure amman namaka alkawari bazan karaba" wani kallo yamata yace "you know my principle bana dukan yara, but kika bari natashi daga wajen nan batare dakinje kin kawo what I asked for ba sainamiki jina jina" wani kallo Mum tamata na alamun taje takawo hakan yasata tashi tafita bata bata lokaci ba tadawo takawo komai kujera yanuna mata yace "keep them there and leave this room, sanan dagayau!" yajuya yakalli Mum yace"ki sallami Uwani duk wani aikin Uwani ita zata dingayi bazatabar gidan nanba saita gama kodako zatai lattin lectures get out" dasauri tajuya tafita tarufo musu kofan.

Wani kallo yabi Mum dashi yace "I am so disappointed in you Hajara, halinki nabani mamaki and ki sauraren kiji bazan zauna inaji ina gani ki rabamin kan yarana ba, wlh duk randa kika kara attempting abinda kikayi yau kinasa anacirema yarana mata kaya kina kiran yara suyi ihu wlh wlh saina rabu dake take this as a warning" cikin kwantar da murya tace "kayakuri Alhaji na yarda nasan nai kuskure I know I took everything far, but raina abace ne maganan da Kaka keyawan fadi duk yadawomin kai, wlh Alhaji da gaske Du'a yar aljanu ce to inba hakaba ya za'ayi Muhsin dake tareda Nana kusan sjekaru biyu kenan yau kawai daga ganin Du'a yace ita yakeso yafasa auren wacce yasani for years, dududu bikinsu saura wata daya, tuntuni Kaka tace ka tattara yarinyar nan ke korata chan duniya inba hakaba bala'i da masifu iri iri sundinga samunta gidan nan kenan, yanzu maganan Muhsin baiwani dadani da kasaba amman what if dagaske yake eh? da gasken gaske yake shi yafasa auren Nana Du'a yakeso bahakan ya tabbatar mana itadin yar Aljanu bace ba kenan, wlh indai aka fasa auren nan saina kira Kaka na sanar da ita komi gwara tun yanzu nagaya maka sabida kar bayan kaji nayi kaga kaman na yaudareka ne" "tashi kifita daga dakin nan" Abba yay maganan cikeda fada, tashi tayi tace "narasa me kakeyi da yarinyar dakai karan kanka kasan bataka bace agidan nanba saisama baka ambato sunanta cikin y'ayan ka, hakanan wlh koma mezai faru saidai yafaru I am a mother bazan zauna inada zankada zankadanyanmata ba sukasa aure ba sabida yar aljanun da aka haifa maka agidan nan, gaskiya nake fadi I can go to any limit dannai protecting yarana, grounding nata adaki doesn't solve anything dan gashinan fita take causing trouble, the best thing is tabar family mu takoma chan family su na aljanu" tai maganan tana bude kofa tafice abinta, gabaki daya duka abinda tafadi yajisu.
Chapter 7 · 0% Book details