← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 109

Sashe 43

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wuraren 9 event planner da akabama contract din birthday din Aneesa yazo yakawo lodin kayan souvenirs dinta, power bank, water bottle da set na makeup brushes ne da duk aka rubuta happy birthday ajikinsu saikuma hadaddun jakunkunan da zasu saka su aciki, ana kawowa tazura hijabi tafito Ammi dake falo tace "sai ina kuma" cikeda murna tace "Ammi zanje in taho da Du'a ta tayani hada this souvenirs a bags dinsu" haba Ammi takama tace "iyye masu birthday a dawo lpy" dagudu tafita tana murna gidan Hajiya tayi, da sallamanta tashiga falo Hajiya na zaune wani irin gudu tayi tafada jikin Grandma tace "good morning Hajiya Naaa" "jama'a na shiga uku, wlh nakusan hana yaran Ammi shigomin gida hakanan bazaku takaitani ba" dariya tayi ta tashi daga jikinta tace "wlh ko kinsa kwado saimun karya, ina Du'a Hajiya? Ankawo souvenirs dina zamuje gida muyi packaging nasu ajaka ne" tabe baki Grandma tayi tace"jetana sama, ni wlh ku tattara kutafi chan wajen Ammi ma yafimin, wanan hiran birthday naki ya isheni Aneesa" dariya tayi tace "Au haka kikace shikenan aiko bazan bari tadawo na agidanmu zata kwana yau" tai maganan tana hawa stairs, dakin Du'a tabude ahankali, zaune taga Du'a tasanya wani farin Paris t-shirt fari kall ga zanen effiltower tower ajiki, da bakin english skirt mai belt data saka dayawani irin fitoda hips dinta, kanta babu dan kwali amman tai parking kalabanta atsakiyan kai tana zane a drawing book tai bala'in kyau, dayake hankalin ta yay nisa bamataji shigowan Aneesah ba, ahankali Aneesa tamaida kofan tarufe sanan takaraso tasa hannu ta fizge drawing book din dawani irin sauri Du'a tadago kanta, kafin ma tai magana Aneesa takama hannunta taja cikin sauri tace "tashi kigani Du'a" tashi tayi Aneesa tasaketa tashiga waige waige bakin hulanta datagani kan gado tadauko tazo dasauri tashiga samata akai tace "ankawo abubuwan gift muje kitayani muyi paking ajaka" tai maganan tanayin hanyan wardrobe wani karamin dark blue hijabi ta janyo mata tadawo tabata tace "sa muje" kallonta Du'a tayi kaman mai tsoro tace "gidanku" gyadamata kai Aneesa tayi tace "eh" ahankali Du'a tamake mata kafada tace "ni bazani ba kunya nakeji" dasauri Aneesa tace "babu kowa agidan fa dagani sai Ammi daga Ya Sharif har Ya Asad duksun tafi office, su Rahima sun tafi school sunada presentation dukansu, nida Ammi ne kawai kinga kuma babu mai tayani please sa hijabin" tai maganan tana karban hijabin tasaka mata bata jira amsanta ba taja hannunta suka fita daga dakin sukai kasa, a falo suka tarar da Grandma ganinsu yasa ta tabe baki tace "agais nidai bye ku gaidamin da Ammin ku" sosai Aneesa ke jin dadi tace "zataji ai gashinan ma zan kai Du'a gidan mu daman bata taba zuwaba muje kiga gidanmu" Du'a naji tana gani tajata suka fita daga Gate dinsu suka shiga next babban gidan dake kusada su, bin gidan take da kallo gidan Babban gaske dan yamafi na Grandma girma ga tulin motoci ga security daban daban dayawa da abinma saiya bata mamaki saikace gidan yan sanda.

Ahankali Aneesa tabude kofan falo tana rikeda hannun Aneesah, ganin su yasa Ammi dake zaune kan kujera tace "Du'a nake gani agidana wato sabida kawarki ce zakizo gidan nan ba sabida kizo ki gaidani ba ko" akunyace tasauke kanta kasa hakanan take bala'in jin kunyan matan murya chan kasa tace "ina kwana Mum" "lpy lau Du'a, how are u" ahankali tace "Alhamdulillah" tashi Ammi tayi tace "come kin tsaya daga wajen ga kayayyakin nakunan ai am cikamin falo dasu" karasowa ciki Du'a tayi ta tsaya, Ammi tace "bari naje sama na kwanta feel at home ko" gyadamata kai Du'a tayi Ammi tai sama abinta, hijabi Aneesa tacire tana linekwa daga ita sai kayan bacci, karasowa kusada Du'a tayi tazare hijabinta tace "bari naje na ijiye mana hijaban adakinmu nazo kigani mufara" wucewa sama tayi hakan yasa Du'a tazauna ahankali akasa tana kokarin jan hulan da Aneesa tasaka mata gaba dan bai rufemata gaban kai da kyau ba ana ganin kitsonta tagaba da kwantaccen gashin goshinta, saukowa Aneesa tayi tazauna kusada ita tace "kinga wayan nan bags din kowanne zamusa 1 water bottle dinan, da powerbank dinan dakuma set na makeup brush dinan, ke gashima baki makeup ai wlh gobe saikinyi, gobema zamuyi aiki da yawa zanje na karbo kayan da zansaka awajen hudayya, kema harda naki zan karbo" bude idanu Du'a tayi tace "nawa kuma" gyadamata kai Aneesa tayi tace " Ya za'ayi birthday na guda nayi dinki banma best friend dina ba" dan murmushi Du'a tayi ita bata tabayin friend ba saisa idan Aneesa nakiranta best friend saita dinga jin abun wani bambaran.

Hada kayan suka shigayi suna jera jakunkunan anan falon, tashi Aneesa tayi dasauri tana kama cikinta tana yatsine fuska dasauri Du'a tace "menene" hanyar stairs tayi tace "continue ina zuwa lemme use the bayi, cikina na juyawa I guess I am too excited ne" dan dariya Du'a tayi batace komiba tacigaba da abinda takeyi ahankali aka bude kofan falon dawani irin sauri tadago kanta, hada ido tayi da Asad dake sanye dawani dark blue 3quater da farin t-shirt yana wani irin zuba uban kamshi fuskanshi yadan kumbura alamun baidade da tashi daga bacci ba, wani irin faduwa gabanta yayi dawani irin sauri tadauke kanta tana saukar da kanta kasa, gyara zaman kafanta tayi takai hannunta tanajan skirt dinta yarufe mata kafa duka dan yadan tattaro zuwa wajajen gwuiwanta sabida yanayin zaman datayi da jakan datake ijiyewa in between legs dinta tana saka souvenirs din aciki, wani irin ijiyan zuciya tasauke feeling so uncomfortable sabida yanayin kayan datasaka, ahankali taja jakan daga tsakiyan kafanta tadaura kan cinyanta sabida yadan rufe boobs dinta dasukai girma ta farin t-shirt din sanan kana hango shape da komi na bra jikinta sabida very light expensive t-shirt ne, jin shiru bataji sahun tafiyanta ba yasa tadan dago kanta kaman munafuka tana kalle kalle, a dinning din falon taganshi tsaye yadaga flask yana zuba ruwan zafi a mug yana kokarin hada coffee, batasan mesaba amman kasa daina kallonshi tayi shigan dayayi yamata kyau saiyay kaman wani dan gayu, juyowa yayi dawani irin sauri tadauke kanta kirjinta na dukan uku uku, daukan mug din yayi yazo cikin falon kujeran dake facing nata yazauna akai tareda mika hannu yadauki remote yakunna TV yasaka a tashan ball sanan yayi sanan ya ijiye remote din yay crossing legs dinshi yakai mug din bakinshi yayi sipping coffee ahankali yana kallon TV.

Kasa cigaba da abinda takeyi tayi, gabaki daya jitayi she's so uncomfortable, sai gyara nan da nan da nan take na kayan jikinta, daidai nan Aneesah tasauko kasa ganin Ya Asad yasa ta ware idanunta tace "laaaa Ya Asad daman bakaje office ba" ko kallonta baiyiba haka yasa tawuce kusada Du'a zata zauna yace "make me some omelet ki kawomin part dina" dasauri takalleshi cikin wani irin jin dadi jin yakulata tace "tom Ya Asad" sanan tawuce kitchen, tashi shima yayi rikeda mug din yawuce yafita daga falon, wani irin ijiyan zuciya tasauke tacigaba da aikin har lokacin takasa dainajin kamshin dayakeyi.

Kusan 10min Aneesa tadauka a kitchen tana hadamai lafiyayyen Omelet sanan tafito rikeda hadadden tray data daura plate din Omelet din akai, daidai lokacin aka bude kofan falo wata hadaddiyan faran mata tashigo tana sanyeda Abaya tanama Aneesa murmushi, wani irin tsalle da ihu Aneesa keso tayi tunawa da abincin waye ke hannunta yasa ta ijiye kan hannun kujera dasauri sanan tawani kwasa da gudu tafada jikin matan saikuma kuka. "Oyoyooo Mum, bakincemin gobe zakizo ba" kankameta matan tayi tace "I wanted to suprise my birthday girl" tai maganan tana kallon Du'a dake kallonsu tana murmushi dan taga kamanninsu da matan hakan yasa tagane itace Maman Aneesa, sakin Maman nata tayi tajuyo takalli Du'a tace "Mum kinga best friend dina sunanta Du'a" wani irin kallo Turai tabi Du'a dashi, ahankali Du'a tace "ina yini" lafiya ta amsa sanan takama hannun Aneesa tace "muje sama" juyowa Aneesa tayi takalli Du'a tace "Du'a please tayani kaima Ya Asad Omelet dinshi yanzu karyamin fata, kina fita flat dinsu ne a gefen namu kinji please, baiyi breakfast ba" gyadamata kai Du'a tayi ahankali tana kallon yanda sukebinstairs Mum dinta namata magana, harsunkai karshen stairs Aneesa takara juyowa tace "Du'a hurry karya huce bazaici ba" tashi tayi jikinta har bar bar yake tadauki tray data ijiye kan kujera sanan tawuce tafita hakan yasa Aneesa sukai ciki, flat din datagani kusada nasu tayi, ahankali ta tsaya gaban kofan tama rasa mezatayi she's so nervous hakanan, door bell datagani ta danna ahankali, daga taciki taji ance come in.

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

✍️ M SHAKUR
Chapter 43 · 0% Book details