← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 109

Sashe 76

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 5 min read

Tunda sassafe aka tashi agidan sai aikace aikace ake itako ko tsinke Grandma tahanata dagawa saima wani special gyaran jiki da akemata nasu dilka da turare, bayan angama wata waxing din dayasa tasha kuka dan saida Grandma ma ta tsaya akanta sanan tahakura, sai wajajen one aka gama komi aka mata wanka Grandma tadauko mata wata sabuwa English atampa cikin wanda tadinka mata milk mai shegen kyau da tsada tasata tasaka, shiryawa tayi ciki aka mata dauri dudda batai kwalliya ba but kana ganinta kaga Amarya to be, dakinta Grandma tawuce da ita tace "Hamad yakirani sun shigo Abuja wai" gyadama Grandma kai tayi ahankali jikinta duk yay sanyi, murmushi Grandma tayi tace "bari nabada nama akawo miki ko kyayi fara'a" murmushi tayi kuwa Grandma tai dariya tafice, tana kitchen tana kokarin debanma Du'a nama aka taji anbude gate, Razika dake kusada ita cikeda murna tace "Hajiya sune" murmushi Grandma tayi tabata naman tace "kaiwa Du'a kiga" sanan tawuce tafita da fara'anta, motoci uku ne, Sienna Abba ce agaba, sai wata karaman mota Honda, saikuma bus din Abba wacce Ya Hamad dake sanye da kayan sojoji keja, sosai Grandma ke murmushi tace "oyoyo oyoyo" yaran ne suka fara fitowa daga mota su Amra, Aneela, Mudasir, da Muhammad suna tahowa wajen Grandma da gudu suna kallon gidan, kafin Mum ta sauko taci wani hadadden atampa fuskar nan ba yabo ba fallasa, saiga Hawwa da Nana dasuka saka kaya iri daya sunyi kyau ba laifi sai kalle kalle suke, saiga Mami itama tadan rake but she is looking okay, sai Hamad daya sauko duk suka taho wajen Grandma, motar tsakiyan kuma wata matace tafito babba ce ba yarinya ba baka tana mika hannunta cikin mota saiga wata tsohuwa tukin tafito rikeda goro a hannunta tana tafiya adudduke ranta abace kana ganinta kasan wanan tsohuwa fitinanniyar tsohuwa ce, ga uban lalitan data daura, saikuma motan Abba wanda yake shine aciki sai kannenshi maza dasuke uwa daya uba daya guda biyu.

Cikeda fara'a Grandma tai gaida dasu Mom da ba laifi basu nuna wani face ba itama ta amsa su, tana rungume su Nana da Hawwa, kana ganinta kaga classic woman sanan takalli Mami dake kallonta asanyaye tace "kaisu ciki daughter" sanan takarasa wajen Kaka cikeda barkwanci tace "kishiyata agidana Allah yakawomin gasasshiyar tsuntsuwa baki barin gidan nan sainasa mai gida ya danna miki saki" tai maganan tana kallon Hamad, hararanta Kaka tayi tace "inkin isa kisashi, kin rabani da jikata wanan ma zaki kwace min shine, nidai ki kaini daki inba sokike kafafuwata su tsinke ba nashayo wanan uban tafiyan" dariya Grandma tayi takalli diyarta data rike mata hannu dake kallon Grandma ganin hadaddiyar mata tace "barni nakaita ciki" takama hannun Kaka sanan takalli su Abba tace "Alhaji kushigo agaisa afalo wanan tsohuwan tagaji" hararanta Kaka tayi tace "dadin abin ban girmeki ba" kwashewa da dariya Hamad yayi tace "zakaci ubanka ne bakin soja kawai" falo suka shiga da already su Mom suna ciki, sun kasa boye kalle kallen dasuke, sunsha jin labari cewa Mami yar masu kudi ne but basusan kudin yakai haka ba, yanzu dama a irin wanan gidan Du'a take, lallai.

Zama duk sukayi dayake falon da girma yaci kowa yaran sai wasa suke, Kaka na zama tace "ina Du'an take" murmushi Grandma tayi tace "zatazo ta gaida ku ku huta kusha ruwa tukkuna ansha tafiya" tai maganan daidai su Razika da Shema'u dasauran yaran suka shiga gabatar da ruwan gora da drinks dabama susan irinshi ba, saida suka gama sanan Grandma takalli Razika tace "Razika kira Du'a" gyadamata kai tayi tajuya tatafi sama.

Duk suna zaune falo harda su Abba duk anyi shiru kaman kowa yakosa yaga Du'a ne, Du'a tafito ahankali kanta akasa tana gyara lullubin babban gyalen da Grandma tabata tasaka, ahankali take tafiya gabanta na faduwa takasa dagokai ta kallesu, daga Mom, Kaka, su Nana da Hawwa sun kasa yarda Du'a suke gani, har shi Ya Hamad ma, kasa rufe baki Kaka tayi tace "jama'a yarinyar nan ce dai wanan koba ita bace"? Hamad dake gefenta yace "Du'a ce Kakus" cikeda masifa tace "yoni wai wagga Y'a kara komawa aljanna take kome" batare da Grandma takalleta ba tace "yarinya tai kyau dai Masha Allah maihadinta da aljanna" daidai Du'a takarasa saukowa, ahankali ta shigo falon takasa kallonsu tsugunnawa tayi atsakiyan falon tana wasa da yatsunta murya chan kasa tace "Abba ina yini, Baffa sannu da zuwa, Kaka ina yini, Inna ina yini, Mom sannu dazuwa, Mami ina yini, Ya Hamad, Ya Nana, Ya Hawwa ina yini, Aneela, Amra, Mudasir and Muhammad welcome" duk maganan nan tayishi ahankali cikin xakin muryanta dayasa jikake dakin yay tsit.

Ahankali Abba dake kallonta yace "Du'a" sai alokacin tadago kanta takalleshi, hannu yamika mata, ahankali ta taso hannunta tasaka kan nashi zaunarda ita gefen kafanshi yayi yana kallon fuskanta yace "how are you Du'a? Ya shirye shirye"? Dan murmushi tayi tana kallon Abban nata ganin yau yamata magana faram faram ahankali tace "Alhamdulillah Abba" hannunshi yakai ahankali yadaura asaman kanta yace "Allah yamiki albarka, Allah yakaimu jibi lpy akaiki dakinki, Allah ya sanyama aurenki albarka" ahankali tace "Ameen Abba" wani irin murmushi Grandma tayi sometimrs rashin wayon Du'a pays her alot, kannin Abba dake kusada ita addu'a suka mata sanan babban cikinsu maibin Abba yace "saiki sanar da mijin naki iyayenki sunzo yazo yagaidamu anjima da daddare, yaga yan uwanki muna muganshi musan wanda muka bama yarmu, ayi zumunci" gyadamai kai tayi, sanan Abba yatashi yace "kutashi mutafi masallaci" tashi mazan Saukayi harda Hamad suka fice dan zuwa mosque.

6️⃣0️⃣

MASU FITAR DA NOVEL DINAN WAJE KUNMA KANKU MARASA AMANA.

PAY 500 INTO 3107021073 AISHA MUHAMMAD FIRST BANK SAIKI TUROMIN EVIDENCE OF PAYMENT TA WATSAPP NUMBER NA 07012181461 SAINAI ADDING NAKI A GROUP DIN DANAKE POSTING.

CHAT ME UP DIRECTLY BY CLICKING ON THIS LINK
wa.me/+2347012181461
Chapter 76 · 0% Book details