← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 109

Sashe 18

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wardrobe din dakin tabude hadaddun karyane wanda mostly abaya ne, dogayen riguna kala kala daban daban, ahankali tadaura hannunta kan wani baki fitodashi tayi daga leda tana kallon rigan kaman Grandma ta aunata shiryawa tayi cikin rigan saikuma dagudu tai wajen madubi tana kallon kanta yanda taga tayi kyau ko Nana su bata taba ganin tasaka doguwan riga mai tsada nan ba, murmushi tayi tadaura dan kwalin saman tadauki hijabinta akai tasaka tafito tasauko kasa Hajiya na ganinta tace "ina gyalen abayan Du'a" dasauri tace "nadaura akai Grandma" dan dariya Hajiya tayi saikuma ta mike tace "zokiga" karasowa gabanta tayi Hajiya ta yaye hijabin dan kwalin ta warware sanan ta gyaramata parking gashin, takalli Razika dake wajen tace "he daukomata handbag a dakinta Razika" da sauri tai sama, taimata rolling gyalen saitai kaman wata balarabiya, saukowa Razika tayi da jaka mai kyau, Hajiya ya karba tabata tace "perfect oya kutafi to driver na waje yana jiranku" takalli Razika tace "stay by her side, saikun dawo, bye Du'a" juyowa Du'a tayi tamata waving hannu alamun bye sanan suka wuce suka fita sai murna take basabamba, mota suka shiga direban yajasu.

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

✍️ M SHAKUR

Free page
EPISODE 1️⃣4️⃣
Bini bini direban Hajiya dake sanye da uniform ke kallonta tamadubi, hakan yasa Razika takalleta, ganin yanda take kalle kallen hanya tana murmushin nan dake karamata wani kalan kyau nadaban yasa Razika tace "is this ur first time a Abuja Du'a?" juyowa tayi tazubama Razika mayun idanunta dakesa mutum yaji wani kwanciyan hankali harzata gyadamata kai ta tuna maganan Hajiya hakan yasa tace "eh" murmushi sosai Razika tayi tace "Abuja ai nada kyau, nima Hajiya tadaukoni daga kauyen mu takawo ni nan, sanan akwai lesson teacher dake zuwa mana karatu duk asabar da lahadi, Hajiya nason yara, kinga tunda nake a Abuja bantaba ganin yarinya mai kyau kaman keba" dan murmushi tayi saikuma tadauke kanta tamaidashi kan titi tana kallon motoci dan kunya takeji taji ance tanada kyau bamataso adinga cemata haka, ahankali tace "thank you" "yauwa munkawo" Razika tafadi ganin driver yay kwana yashiga wani babban Plaza, parking yayi hakan yasa Razika tace "sauka muje" bude kofa tayi ahankali tafito tana kallon wajen yanda akwai mutane kowa na shiga da fita abinshi, ko yanda takebin mutanen datake gani da kallo ne yasa taga suna kallonta itama oho dasauri tarike hannun Razika gam data fito tace "muje" tana rikeda hannun Razika suka wuce suka shiga wani hadadden saloon dake nan first floor, ma'aikatan suka taso suna gaidasu kafin Razika tamusu bayanin me za'amata nan aka shiga yi mata gyaran gashin.

"inje insiyomana ice cream a wanchan shagon Du'a" ta tambayi Du'a da ake wankema gashi, murya chan kasa tace "eh" tashi Razika tayi tafice daga saloon din daidai angama wanke ma Du'a tulin gashin aka nannade mata gashin da towel matar tace "tashi muje dryer" tashi tsaye tayi tawuce taje tazauna ana sliding kofan saloon din aka shigo, juyowa tayida sauri tazaci Razika ce, wani Alhaji tagani yaci babban riga milk na shadda dake kyalli da akalla zaikai 60yrs baki dashi mai kyau ga gemu kadan tareda wata mata kana ganinta kaga yar duniya ga hujin hanci akan hancinta guda uku tana rikeda jaka tana taunan cingum tana sanye dawasu kaya dabasu da maraba da babu ajikinta, suna shigowa masu aikin suka taresu. "welcome Alhaji, welcome Hajiya" gyadamusu kai yayi yanabin matan saloon din da kallo one by one, zama matar dake taredashi tayi kan kujera tawani kamo hannunshi ganin ba ita yake kalloba da sauri yajuyo yakalleta jinta kamamai hannu, kashemaai idanu tayi tace "Baby kagaya musu style din da za'a min" washe baki yayi yace "kai wlh mata kun iya rigima yanzu style ne sai an tambayani, ninasan kan style ne" kallon yar aikin dake gabansu yayi wacce ke jiran bayanin su kafin sufara aiki yadan lashe baki sanan yace "okay bari muga" juyawa yayi yacigaba da kallon yan shagon, Du'a yanuna da akema rolling gashinta a roller za'a sata a dryer yace "how about that fine baby style, Zinariya kinason style din"? yamata tambayan still yana kallon Du'a da akema gyaran gashi wacce ko kallonsu ma batayiba madubi take kallo tana kallon abinda ake mata akai wanda is new to her tabama kofa baya, ganin inda yake kallo yasa Zinariya tace "katafi meeting din dakake dashi Sweet, idan kagama saika biyo kadaukeni" tai maganan tana shafamai hannunshi still datake rikedashi, dan juyowa yayi yakalleta kaman wanda ya manta da abinda ke gabanshi yace "ohh meeting dinan, to,to bari inje, saina dawo" yay maganan yana juyawa bude kofan yayi harzai fita saikuma yadawo dasauri yawuce wajen kujeran Du'a ya tsaya tagaban wajen yana facing nata directly yakare madubin datake kallo yana murmushi yana kallonta kaman yanda takedan kallonshi atsorace yace "nace nawane kudin gyaran kan Zinariya"? Ya tambayi mai gyaran kan Du'a yana kallon Du'a kaman wani tsohon maye wanda baitaba ganin mace ba sai akan Du'a, Mai gyaran gashin Du'a dake kallonshi ne itama cikeda girmamawa tace "all payments are done to Christy Alhaji gatachan the cashier" tanunamai wacce ketare da Zinariyan shi data daure fuska tana kallonshi, yana kallon Du'a still yace "in that case ba matsala, by the way young lady ur hair is beautiful" yama Du'a magana yana wani kalan kallonta, sai alokacin Du'a tadago kanta ta kallai da kyau wanan sa''an Abban tabe hakan yasa tamai shiru, wani irin hadiye yawu yayi yana lashe baki murya chan kasa yace "bala'i Allah yayi mace anan" rasa yanda zaiyi yasa yawuce yawayance yana kallon Zinariya yace "natafi Baby" yawuce yafita ya shiga hadaddiyar jeep din da aka kawosu ciki daidai lokacin Razika na shigowa rikeda ice cream guda biyu tazo inda Du'a take tamika mata tace "gashi" hannu tasa takarba tana murmushi tace "thank u" gajeren tsaki Zinariya tasaki tadauke idanunta dagakan Du'a kishi nawani irin turnuketa kaman taje tashake yarinyar takeji tadai daure dantafi karfin karaman yarinya haka.
*********

Kano!
Tundaga nesa yake hango yanayin Ammin shi dake tsaye achan baya, jiyayi ranshi yabaci sosai, ahankali yakalli Sharif dake tsaye gaban kantar Max Airline yace "collect the ticket" sanan yawuce yana tafiya daidai kaman dan Sarki, yau yana sanye da native kaya dasukamai kyau ba kadan ba, farin yadi yasaka anmai dinki jumper daya zauna ajikinshi chass, kafanshi yasa wani takalmin Dior mai kyau black dakeda igiya, gashin kanshi dinan as usual looking so coily and black, idanunshi yasaka bakin shade dan baison kallo sosai sai kamshi yake zubawa, wucesu Aneesa yayi batare daya kallesu ba yakarasa inda Ammi ke tsaye tana daddanna wayanta tasanya wani hadadden abaya mai tsadan gaske, dayake tabashi baya ko kadan bataji zuwan shi ba dan hankalinta ma yayi nisa dan tunani take, zuba hannunshi yayi a aljihun wandonshi yana kallon screen din wayanta dan yafita tsawo ganin number datake kira da akai saving da Maigidana yasa murya chan kasa yace "Ammi" firgigit tadan waigo ta kalleshi saukar da wayan tayi dasauri gudun kar yaga number datake kira tace "is it time for boarding already son" shiru yayi yana kallonta, saikuma ahankali yakai hannunshi yacire glasses din idanunshi yace "Ammi baki gaji da kiran mutumin nan ba eh?" dan murmushi tayi dakana ganin murmushin kasan na damuwa ne tace "inaso na sanar dashi zamu dawo Abuja ne dama, kaga yakamata yazo yaduba mahaifinshi baida lafiya fa" cikin dan bacin rai yace " Ammi yafiki sanin mahaifinshi baida lafiya idan baizoba ki shareshi shiya sani, Ammi kidena sa kanki a damuwa, what if u fall sick eh? ina zansa kaina" tunda take maganan take kallonshi, ganin ranshi yabaci na damuwa yasa tai murmushi tace "wayagaya maka ina cikin damuwa eh, I'm fine kawai dama sabida Dadda kane nadamu, oya maida glasses dinka kafo kyau ahaka, mata sukaga this ur no nonsense eyes bazasuyi approaching dana sunce suna sonshi ba" dan murmushi yamata daya karamai wani irin kyau saka glasses din tayi tace "oya muje to, come here lemme hold ur hand asan nine maman this handsome boy" turobaki yayi yace "Ammi kindaiga akwai yara anan ko karkisa su rainani" yay maganan yawuce dasauri kafin tarikeshi zuwa wajen Sharif dakechan, binshi da kallo tayi saikuma takarasa inda su Aneesa suke tace "let's go girls gobe sai makaranta" duk dariya sukayi, Aneesa tace "Ammi kince zakicema Ya Asad ya chanza min waya in munkai" gyadamata kai Mami tayi tace "eh dukanku zansa ya chanza muku" ganin Sharif namusu waving hannu yasa Ammi tace "kumuje" wucewa sukayi saba ko 3min basuyiba sukai boarding jirginsu zuwa Abuja.

Suna sauka airport motoci biyu sukazo dukansu, shiga sukayi yayi Ammi takalli Asad dake kusada ita tace "gobe zaka fara shirye shiryen aiki ko" gyadamata kai yayi yace "eh gobe ne, illustrator dinmu Ammi yasami accident a hannunshi I don't know how am gonna start looking for new one, gawanan TV program dinan dazan fara dukshi yabatamin schedule" ahankali tace "don't worry komi zai daidaita I trust my son" harsuka karasa anguwansu, wani hadadden gida aka bude musu shiga sukayi gidan ya bala'in hadu, sassakowa sukayi Security gidan nashiga da kayansu ciki shikuma yay hanyar flat dinsu, binshi da kallo Aneesa data fito daga motansu tayi, fitowa Mariya tayi tace "yarinya kin debo ruwan dafa kanki" juyowa tayi takalli Mariyan cikeda tsiwa tace "mekike nufi?" Ammi dahartai gaba tajuyo ta kallesu tace "to bismillah tsiya zata fara ne" dasauri Aneesa tace "Ammi Mariya ke tsokana na fa" murmushi Ammi tayi tace "barta kinji Aneesa zomuje" dasauri Aneesa tabita tanama Mariyan gwalo itakuma tai dariya zata mata gwalo Rahima ta ture mata meya tace "dalla wuce mutafi" wucewa tayi tana turo mata baki sukai flat dinsu.
Chapter 18 · 0% Book details