← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 109

Sashe 75

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ahankali tabude gate din gidansu da akai decorating ga kujeru ga abinci ga mutane ana hayaniya sabida akwatinta da aka kawo yasa tafito dasauri ta tsaya a kofar gidan ita bama tasan inda zataba, gajiya tayida tsayuwan ta shiga gidan kanta akasa tana tafiya kaman daga sama taji anja hannunta dasauri tajuyo Aneesah tagani hannunta daya daure a shoulder kaman wacce takarye kafinma alura dasu janta tayi suke shiga dakin security gidan dake musu gadi, suna shiga sukai zamansu akasa sabida shi yanachan tsakar gida, ahankali Du'a dake kallonta tace "maiya sameki a hannu" murmushi tayi tadauke kai dasauri tace "bakomi Anty Du'a" bude idanu Du'a tayi tana kallonta, hakan yasa tajuyo takalli Du'a tace "naga fitanki daga gidanmu, naga yanda kika shigo nan kika kuma fito daga window dakinmu nasama, shine nace bari nafito nasameki ina fitowa kina shiga ciki, ke bakisan ba'a ganin Amarya ba Allah yasa basu lurada ke ba, duk fa danginmu ne anan da yan uwan su Daddan mu, da kawayen Ammi, thank God basu ganki ba Anty Du'a, but how comes batare dasu Rahima kika fita ba"? Tama Du'a tambayan saikuma dasauri tai murmushi tace "ohh natuna maybe Ya Asad ne yadawo dake" tasake murmushi dakana gani kasan she's hurt, ahankali Du'a takama hannun nata tana kallo sosai fa ta karye, dan da igiya awuyanta ma take supporting hannun, ahankali tace "Aneesah what happen to your hand? Dama karyewa kikayi saisa ban ganki ba maisa babu wanda yafadi mini danazo na gaisheki kuma saida na tambaya ina kike, what happened?" Du'a tasake tambaya cikeda bala'in tausayinta, dan murmushi Aneesah tayi sanan ahankali tace "kwana na 5 a hospital ma" hawaye Du'a taji yazo mata tana kallonta sabida ta rame tai wani iri, kafin ahankali tace "Ya Asad ne, dagani harsu Zeezee da Billy" saikuma ta girgixa kanta dasauri tace "amman nima nasan nina jama kaina, nai laifi so I deserve his punishment" kallon Du'a tayi dataga hawaye yacika mata ido tace "kema is because I trust u please karki gayama kowa he made everything look like an accident" dan murmushi tayi takalli Du'a ahankali tace "Du'a Ya Asad na sonki sosai wlh" tai murmushi sanan tace "I thought kece kika kwacemin shi but after yanda yadawo dagani har kawayena, ba su Zeezee kadai ba har wayanda sukai chatting naki up suna zaginki yahada mu duka yaci ubammu sanan yasa mukai signing under taking if anything happens to you to sune, all my friends hate me now sunce nasasu a trouble da kullesu ma zaiyi kinga kukan damuka dinga yi sabida yanada evidence zamu iya zuwa gidan yari ko bamu jeba barin ma kawayena sunbata sunan gidansu, so da kyar yahakura fa, Ya Asad almost killed me sabida abinda namiki Du'a da ace baya sonki dabazai taba rama miki, yanzu bayamamin magana and yace zai karbi transfer later a school northwest zai maidani a kano yakomar dani gidan ubana, wai he don't wants me anywhere near you because I am toxic and ke bakisan komiba kar yazo watarana na kashe ki, har gidan nan shiya hanani shigowa ma" takashe maganan bakinta narawa sanan ahankali tace "Du'a please ki rokeshi karya komar dani wajen Babana, kinga Babana baida kudi kaman Dad, kuma a family mu Dad ne kawai mai kudi shike kula da kowa harda su Rahima da Ya Sharif da kakanmu Dadda dake kano da Mamana Anty Turai, shine komi namu, saikuma Ya Asad dashima yake bamu kudi sosai, wlh I cannot leave agidan mahaifina, kuma kowa yasani idan Ya Asad yace saiya maidani wlh ko Mamana Anty Turai bata isa tai wani abuba Ya Asad taurin kanshi yasa yafi karfin kowa har Dad shakkan shi yake, Du'a please nasan hala baki saniba wlh yana sonki kome kikacemai zaiyi, Du'a please Anty Du'a I am so sorry, kiyafemin, wlh wlh bazan kara miki abinda nayiba, all what I've said nafadi ne out of jealousy I didn't mean anything, Du'a please" ahankali Du'a ta rungume ta, dan ta bala'in bata tausayi, yanzu Asad muguntan shi yakai yaci uban sister shi, cousin dinshi, his blood haka? harda karyata, to ita waye dabazai iya mata sama da hakaba, tadade suna kuka sanan tadago hannunta takai tasharema Aneesah hawaye ahankali tace "Aneesah I am sorry kiyakuri please, dukni najamiki, I am sorry" sharemata hawaye itama Aneesah tayi tace "Anty Du'a stop telling me Sorry, ni yanzu kanwar kice, kece big brother wife dinmu" wani iri Du'a takeji ahankali tace "dan Allah kidena cemin Anty" makemata kafada Aneesah tayi tana tashi tsaye tace "bari natafi gida karki fito fa saisun tafi, zan fadama security kina nan" bata jira amsanta ba tafice, security dataga yana kokarin shigowa dakinshi tagayana Du'a na ciki sanan tafito daga gidan daidai Asad na fitowa a motanshi daga gidansu, chak ta kame awajen a tsaye tama kasa koda motsin kirki saida yazo daidai wajen sanan taga ya saukar da tinted glass dinshi kasa, wanan karan kananun kayane ajikinshi idanunshi sanye da bakin glasses ahankali yasa hannu yazare bakin glasses din yazuba mata mugayen idanunshi dayasa tafara shaking, bakinta narawa sosai tace "Ya Asad is not what u think wlh kallo naje nayi nakai akwatin, dan Allah kayakuri" wani irin kallo yamata wani mugun kalan wulakantaccen kallo dayasa saida taji hanjin cikinta yakara sanan yadauki glass dinshi yamaida a ido yamaida glass din motar sama sanan yaja motar, dasauri tajuya tashiga gidansu tanajin wani kalan bakin cikin dabata tabaji ba arayuwanta barinma na komarda ita Kanon dazaiyi_babu randa zatai salla dabazata roki Allah yasa ya hakura ba.

5️⃣9️⃣
DUK WACCE TAKARANTA LITTAFIN NAN BATARE DATA BIYABA BAN YAFEBA.

THIS BOOK IS 500 PAY INTO 3107021073 AISHA MUHAMMAD FIRST BANK SAIKI TUROMIN EVIDENCE OF PAYMENT TA WATSAPP NUMBER NA 07012181461.

YOU CAN CHAT ME UP DIRECTLY BY CLICKING ON THIS LINK
wa.me/+2347012181461

Sai wajajen 6 aka waste daga gidan Grandma har kawayen ta duk suka tafi yan aiki ne kawai suka rage, kaga Grandma ko ubar Amarya albarka, kawo akwati kawai amman tayi gayu kaman adauketa, karan kiran sallan magrib yatada Du'a daga bacci datayi anan kasan dakin security, jin gidan yay shiru yasa ta tashi ahankali tabude kofa tafito tashiga ciki, taga aike aketayi gidan ya kacahme ga akwatuna ko'ina afalon su Razika nata aiki da matan dake mata gyaran jiki itama tana tayasu, ganinta yasa Grandma tajuyo tai wani murmushi tace "oyoyo taho nan yanaganki wani irin, zonan zazzabi kike ne" Grandma tajata jikinta cikeda so tana taba fuskanta da wuyanta jin na zafi yasa taji dadi tace "bacci kikayi ne" gyadamata kai tayi tace "eh adakin security a kasan falonshi nadawo gida yacika kuma banso a ganni" baki Grandma takama tace "shine bakisa ankirani na nema miki waje ki boye ba, oya wuce kitafi sama kiyi wanka kizo kisha magungunan ki amiki turare, gobe su Maman ki zasuzo, jibi za'a fara shagalin biki" gyadamatakai kawai tayi ahankali sanan tawuce sama, dakinta tabude tashiga ganin yawancin kayanta an kwashe barinma na amfanin ta yasa tafito ganin Grandma natahowa yasa tace "menene"? Ahankali tace "Grandma kayana ina suke"? Murmushi Grandma tayi tace "daga gobe a side dina zaki dinga kwana saisa nai clearing abubuwan dakike amfani dasu nakaisu chance, wanan da yan gidanku zasuzo I don't wanna take any chances wata ta takuraki ko aci zalunki, so u are staying with me all through, tafi kije kiyi wanka kizo" juyawa tayi tashiga dakin nata Grandma tabita da kallo sanan tawuce tana duba sauran dakunan sama datasa agyara sabida bakin dazasu fara zuwa ganin ko'ina fess fess har dakinda Asad ke zama yasa tafito takoma kasa wajen abincin Du'a.

Bayi tashiga zata fara wanka saikuma ta tsaya tai shiru tanason tai wani tunani amman tunanin nabata kunyan yi, wankan tsarki nadaga cikin abubuwan data iya lokacin kafin ma a dena hanata fita, kuma lokacin data fara MP Mami takoya mata wanan, banda haka kwanan nan duk idan lesson Ustaz malamin ta yazo suna fiqihu yana fadamata dalilan dakesa ayi wankan tsarki ciki harda abinda Asad yamata dazu, runtse idanunta tayi taji wani kalan shock tuna abin kafin ahankali tai wankan, wanan uban gashin nata saida tajika, fitowa tayi daga wanka tadaura towel akirji tadaura karami akanta daidai Grandma na shigowa dakin dawani kopi da kula a hannunta, baki tasaki tace "keda za'ama gyaran gashi jibi maisa kika jika kanki" juyawa tayi tai wardrobe dinta tace "kaina ke ciwo" ijiye abincin Grandma tayi tace " bari naje nakawo miki panadol" kaya tasa sanan tai salla karfi tazo tazauna karfi dayaji Grandma ta sata agaba ta shanye abubuwan data kawo mata tass, tana zaune adaki an hanata komi daga anata magunguna sai azo amata wani abu wankan turare daga baya bacci yay awon gaba da ita.
Chapter 75 · 0% Book details