← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 109

Sashe 45

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 7 min read

EPISODE 3️⃣8️⃣
Ko breakfast din kirki Aneesah batayiba ta tashi daga dinning, Dad yace "ina zaki" murmushi tayi tace "zanje nakira Du'a ne Dad mufara prep we have alot of work ko Ya Rahima" gyadamata kai Rahima tayi, Turai dake zaune itama tana breakfast tace "nifa banson tarin kawayen nan naki Aneesa and u know that" dasauri Sharif dayake shirye yaariga yasa kayan zuwa office ash color suit yace "Mum jikan Hajiya ce fa yarinyar batada matsala ga hankali" kallon Turai Ammi tayi da murmushi kan fuskanta tace "karkiji wani abu Anty Turai all friends dinsu nasansu so ba matsala" yatsine fuska tayi tace "shikenan" dasauri tace "intafi" kallonta Dad yayi yace "tunda Ammin ku ta aminta da ita yes go and call ur friend" wani irin tsalle tayi tawuce tafita, juyoda fuska Turai tayi takalli Ammi tace "yanzu sabida danki baida tarbiya tun jiya nazo gidan nan amman baisan dayazo yagaidani ba, kowa yazo yagaisheni banda shi" kafin Ammi tai magana Dad yace "kinga karki takurama Asad yaron nan is very busy u know that, probably aiki yake saisa baki ganshi but I am sure zaizo yaduba ki ni kaina tun jiya banganshi ba" kwafa tayi bata kara cewa komiba, tashi Sharif yayi yana goge bakinshi da tissue yace "natafi" murmushi Ammi tamai tace "adawo lpy Allah yabada sa'a Son" Ameen yace yawuce yafita yay hanyar kofa, bude kofa yayi yafita yana tafiya zuwa wajen parking space aka bude gate din, Aneesah ce tashigo tareda Du'a dake sanye dawani black dogon hijabi mai hula da kan hijabin yadan mata yawa hakan ya bayyana gashinta dayake looking so black and silky, ganinsu yasa ya tsaya a wajen tareda folding hannunshi a kirji yana kallon Du'a, dan murmushi tayi ganinshi tadauke kai zata wuce yace "wlh kizo nan inba hakaba nida ke ne" juyowa tayi takalleshi saikuma ta makemai kafada alamun bazata zoba, dawani irin sauri yazo wajen gabanta yasha tareda kama waist dinshi yakalli Aneesa dake kallonshi tana murmushi yadaure fuska yace "Ke wuce daganan" makemai kafada tayi tace "Ya Sharif bafa wajenka tazo ba wajena tazo" hararanta yayi yajuya yakalli Du'a, ahankali tace "good morning" murya chan kasa yace "yaushe zaki dawo office" dan kallonshi tayi saikuma ta turo baki tace "Grandma tace ranan Monday" yana kallonta still ko kyafta idanu bayayi yace "kin bude bank din" gyadamai kai tayi tace "jiya Grandma ta kaini wani wuri akamin national I'd card aka bani awurin shine mukaje bank tasa aka budemin account" dan ajiyan zuciya yasauke yace "good" da juyawa yayi ganin still Aneesah na wajen tana kallonsu yasa yace "lemme go to the office don't let this girl stress u kinji" gyadamai kai tayi ahankali batare data kalleshi ba dan batason kallon dayake mata this days, ahankali yana kallonta still yace "bazaki min bye ba" kallonshi tayi saikuma tadaga hannunta tamai waving alamun bye, juyawa yayi yawuce wajen mota sanan itama tacigaba da tafiya tareda Aneesah, hada ido tayida Asad daya fito daga flat dinshi sanye da singlet da 3quater yanadan lankwasa wuya alamun yagaji, dasauri Aneesa tace "good morning Ya Asad" gyadamata kai yayi yana saukowa daga staircase din gaban dakinsu, ahankali tabude kofan falonsu dasauri Turai ne kawai zaune afalon dan kowa yatafi sama shiryawa, murya chan kasa Du'a tace "ina kwana" batare data kalleta ba tace "lpy" murmushi Aneesah tayi takama hannun Du'a tace "muje dakinmu" taja hannunta ganin yanda fuskanta ba Rahama dakinsu tabude mata suka shiga su Rahima na arranging kayayyakin dazai amfani dasu anjima.

Saukowa Dad yayi kasa yana sanyeda manyan kaya Ammi biyeda shi, kanwar tashi yakalla yace "bari naje office Turai, yau inada meeting daban daban saikun ganni" murmushi tamai tace "a dawo lpy" juyawa yayi yakalli Ammi dake biyedashi murmushi yamata yace "bye sweetheart" ahankali tace "Allah yabada sa'a" gyadamata kai yayi yawuce yafita daga falon, instead of yay wajen motanshi wani gini dayake gefe daban agidan ginin nada fadi sosai, bude kofan yayi ahankali yanajin karan sauti dake tashi, babban gym ne sosai wajen ga all kinds of machines awajen, Asad dake gudu a treadmill ne yana zufa sosai yajuyo jin anbude fuska, ganin Babanshi ne yasa yadauke kai yacigaba da abinda yake, ahankali Dad yamaida kofan yarufe sanan yashigo ciki home theater dake bada duma ya kashe dakin yay tait sai karan machine din da Asad ke gudu a kaine kadai yarage, karasowa yayi yatsaya gefen Asad din yana kallonshi ahankali yace "Morning Son" dan kallonshi Asad yayi yadauke kai ahankali yace "good morning Dad" cikin wani kalan yanayi na damuwa Dad yace "Asad wai ya kakeso nayi da raina ne eh? Nayi nadaman komi, I've asked Ammin ka for forgiveness ko ita ta yafemin, ina gida bana fita inba fitan office ba but still kana ignoring dina bamaka shigowa side dinmu, haba Asad eh, me kakeso" hannunshi yasa ya kashe machine din sanan yakalli mahaifin nashi yace "I was busy working indoors saisa banshigo side dinku ba bawai sabida kai ba" wani irin murmushi Dad yayi cikedajin dadin respond dinshi yace "to maisa bakazo ka gaida Turai ba" yatsine fuska yayi yace "Dad I don't like her tacika fada da surutu" yay maganan yana wani batarai, dan dariya Dad yayi saikuma yanamamakin sarauta da iskanci iri na danshi cikeda lallashi yace "kowa yasan Turai sai ahankali, but baidace ba yanda bakaje ka gaidata ba tun jiya kana gidan nan kuma, kagama kai wanka saika shiga ka gaidata kaji" yatsine fuska yayi, zai kunna machine din yacigaba Dad yace "wait" kallon Dad din yayi da sauri, dasauri Dad dake kallonshi yace "duko kaga kasan kafini tsowo akwai abu akanka ne zancire maka" ahankali yadan duko batare dayay tunanin komiba, peck Dad yasakinmai agoshi ahankali yace "I love u alot Asad, bari naje" yajuya binshi da kallo Asad yayi saikuma yay dan murmushi yakunna machine din yacigaba da exercise dinshi.

Wuraren Eleven suka gama arranging duka kayan, Rahima takalli Du'a tace "Du'a tashi kifara wanka mu bari mukai kayan kasa sai muje wasu dakuna muyi wanka sabida muje shagon hudayya mu amso kayanmu" gyadamusu kai tayi tace "kayana na gida" hararanta Mariya tayi duk suka tsaya suna kallonta Aneesah tace "mu bamuda kayane halan jekiyi wankan karmuyi latti" gyadamusu kai tayi sukuma suka kwashi kayan suka fice itakuma tawuce tashiga bayinsu.

Sauka kasa sukayi suna ijiye kayayyakin a guest room inda nan aka jera all kayan amfani birthday din aciki, fitowa sukayi zasu koma sama daidai lokacin aka bude kofa aka shigo, Asad ne yana sanye da wani 3quater na sojoji green da white riga, sai uban kamshi yake zubawa kana ganinshi kasan yay wanka, ganinshi yasa duk suka gaidashi. "Ya Asad good morning" "morning" ya amsa su atakaice yana shigowa cikin falon, sanan ya kallesu yace "the 3 of you should go to my flat and clean everthing now, kuyi mopping" gyadamai kai sukayi dasauri babu gardama duk suka wuce dudda sunada abinyi, ahankali yahau stairs din yana tafiya ahankali yashigo falon sama yanason yaje yagaida Ammi yabata hakuri finally su shirya dan yagaji da yanda ta share shi ko nemanshi batayi, muryan Turai yaji tana magana awaya zata bude kofan dakin datake ciki tafito hakan yasa yatura kofan dakinsu Rahima yashiga da sauri daidai tana bude nata kofan tana fitowa yana rufe kofan batare daya bari yay making any sound ba, dawani irin sauri takira sunanshi tace "Asad" dakin yashigo dasauri yana kalle kalle ya tsani matar nan baimason hanya tahadashi da ita ko kadan, ganin wardrobe dinsu yasa yawani irin bude yashiga dasauri ya labe ciki dan yasan dole tashigo tanemai daidai lokacin Du'a tabude kofan bathroom tafito daure da pink towel din datagani abayin akirji tana kalle kalle to wani kaya zata saka yanzu, gaban wardrobe dinsu tayi ta tsaya sanan takai hannunta ta bude wardrobe din ido da ido sukayi da Asad daya ware idanunshi dan yazaci Turai ce, daidai lokacin yaji muryan Turai tana kokarin murza handle din kofa tace "ba takadirin yaron nan nagani yanzun nan yashigo dakin nan ba" hannu yasa yawani irin fizgo Du'a tashigo cikin wardrobe din zuwa jikinshi sanan yasa hannu yajanyo kofan wardrobe din yarufesu daidai Turai ta shigo dakin, wani irin matse Du'a yayi ajikinshi yana daura yatsunshi akan bakinshi murya chan ciki yace mata shiiii alamun kartai ihu ko any motsi.

Bin dakin Turai taida kallo wayan nakan kunnenta tace "I thought shina gani ja'irin yaron nan fitsararre, wlh duk family mu babu wanda ya rainani irin Asad" saikuma chan taja tsaki tace "halan mugun haushinshi danikeji yasa nake ganin abubuwa kaman shi, sukuma ina yaran nan duk sukayi suka bar daki haka kaman na mahaukata, daki kacha kacha kaman ba na yan mata ba" tai maganan tanabin komi nadakin da kallo.
Chapter 45 · 0% Book details