← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 109

Sashe 61

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hakanan tunda tashiga motan taji zuciyanta na bugawa bam bam bam amman tadai daure, itadai Mariya tai shiru danne dannen wayanta take abinta itakuma Aneesah sai janta da hira take tana mata nodding kai batare datai magana ba ahaka har sukakai Nile takasa magana, parking direban yayi bude mota Mariya tayi tajuyo takalli Aneesah tace "natafi class" gyadamata kai Aneesah tayi sanan ta taba Du'a tace "tashi muje" kallonta Du'a tayi kaman mai shakkanta takasa cewa komi tafito, Aneesa ma tafito tacema direban "Bala katafi saikuma idan muntashi" to Hajiya yaja motan yatafi, sanan takalli Du'a takama hannunta tace "zomuje kiga school dinmu sai in kaiki office nasan bakisan hanya ba" ahankali tana binta suna tafiya tace "zanyi latti" danjuyowa Aneesah tayi takalleta tace "munma kai" wajen wani red car dake pake sukayi, gani tayi Aneesah tabude mata baya tace "shiga" ahankali ta shiga, sanan itama Aneesah tashiga tarufe kofa takalli kawayen ta wasu classic yammata dake gaba manya, mai tukin na sanye da atampa dayan na sanye da english wears tace "let's go girls" suka kunna motan sukaja, hira duka suka shiga yi suka shareta dayasa taji she's so uncomfortable, matan biyu sai kallon Du'a suke ta mirror, ganin instead of su yanki titi sun yanki dajin wajajen hanyar Nile ne yasa tajuyo takalli Aneesah lips dinta har rawa suke ahankali tace "Aneesah ina zamu" wani irin murmushi Aneesah tayi takalli kawarta dake tuki tace "Zeezee ana tambaya fa wai ina zamu" juyowa yarinyar tayi tana tuki takalli Du'a sanan tai dariya tace "zamuje muci ubanki HOD ne fine girl, sounds fun right" suka wani kwashe da dariya dukansu ukun harda Aneesah, kuka da tsoro dukane taji yazo mata amman tadaure takalli Aneesah dake dariya har lokacin tace "Aneesah dan Allah ki saukeni anan natafi office Ya Asad zaimin fada nai latti" tsayarda dariyan da Aneesah keyi tayi jin yanda tai maganan Asad din batai wata wataba kawai ta kwasama Du'a mari jikake pauu! ihu yammatan gabangaban motan suka hauyi dayan da suke cema Billy tace "Fine girl akama marin nan Zeezee" dasauri Zeezee dake dariya tana tuki tace "ita akamawa fa, kuma kaman ya shigeta those her white eyes kaman gajimare sunyi jajir, welldone Aneesah marin ya shiga" murmushi Aneesah tayi tana hararan Du'a dake kallonta tana shafa inda ta mareta idanunta sunyi jajir, tace "wai har yanzu bamukai gidan bane muyi muje mubama hammata iska" wani irin kara gudu Zeezee tayi tace "in the next 1min ur majesty" murmushi sosai Aneesha tayi tanajin dadin yanda kawayen ta ke hyping nata tana karkada kafanta, daidai nan sukakai wani gida mai kama da gidan gona a tsakiyan dajin babban gida sosai, parking sukai akofar gidan sanan Zeezee tafito itama Aneesah tafito sanan taduka takalli Du'a dake zaune tace "Malama fito ko nasa afitomin dake" dasauri su Zeezee da Billy sukazo gaban kofan datake suna gyara hannun riga sukace "ashirye muke" bude kofa ahankali Du'a tayi tana rikeda riganta tana fitowa kawai da Billy da Zeezee suka ja hannayenta tana kokarin fizgewa amman taki suka bude gate suka shiga da ita babban gidan gonan ga katon compound suka wurgata tsakar gidan mugun fadi tayi milk color riganta yabaci, ahankali ta tashi tamike tsaye tana rikeda jakanta idanunta sunyi ja sosai amman taki kuka, Zeezee tagani da Billy sun zauna kan kujerun katakon dake kan dakali dakeda rumfa, sundauki wasu robobi da cokula sukahau bugawa kaman Ganga sanan sukace "zaki iya shigowa Aneesah" turo gate din Aneesah tayi tashigo sanan tamaida gate din tarufe tasaka sakata sanan tashigo ciki kan dankalin taje ta ijiye jakanta da wayanta sanan tadawo filin inda Du'a take atsaye tace "sabida kinga kinada kyau kinfini kyau kinada nono da duwawu da flat tummy wanda all yammata yanzu sunsan abinda maza keso kenan saisa kika kwashemin saurayi Du'a kikamin snatching" ahankali Du'a da idanunta sukai jajir sunsoma cikowa da hawaye tama rasa mezatace tace "kiyakuri Aneesah" ihu sukayi sukace "one zero, Aneesah kinci this round, the poor girl ta tsorata harta soma baki hakuri" wani irin murmushi Aneesah tayi feeling confident tana karajin kanta na kumbura sabida yanda kawayenta ke tunzurata, hannu biyu Aneesah tasa tace "you are nothing Du'a but a bad luck, bantaba ganin munafukan yarinya that hide behind pretty irinki ba, I regret saninki, Du'a inason Asad kaman raina kinsan shekara nawa nayi ina sonshi? Tun ina yar yarinya, tunda nafara wayau nasan Ya Asad nake sonshi amman tashi daya kin kwacemin shi kin aure sabida kinga kinada kyau u can steal any man eh, to bari kiji wanan kyan dakike tagama dashi sainai buzu buzu dashi yau wlh I will beat u blue black" Du'a na kallonta still har lokacin ahankali tace "Aneesah nidake kawayene fa, nima badason raina na aureshi ba kuma nace kiyakuri, nima banasonsh......" bata karasa maganan ba Aneesah tasake wanka mata mari akaro nabuyi habawa sai dariya da kida wajen su Zeezee sunama Aneesah welldone welldone dayasa Du'a taji kuka yazo mata gadan gadan amman tadaure but saura kiris tasaki kukan, Aneesah ta nunata da yatsa tace "wlh yau nakara yarda munafuka ceke makaryaciya kuma, bayan Dad yacemana kece kika ce shi kikeso shi zaki aura shine yanzu kike cewa baki sonshi, yanzu nake ganin dalilin dayasa yan uwanki basa sonki Du'a, no uwarki da ubanki ma basa sonki, u are just a p*ssy yarinyar nan, banza kina takama kinada kyau bakisan duk wanda yaga kyanki tausayinki yakeji ba sabida ansan this is not a normal kyau aljanna kawai mayya I am sure maitanki kikama Ya Asad kuma yau zan kwanceshi mayya kawai, mayya aljana" fashewa da kukan datake rikewa tayi tana girgizakai tace "niba mayya bace Aneesah kidena cemin mayya kuma Abba da Mami basu tsaneni ba, stop calling me with that name" tsit kakejin kidan dasukeyi sun dena Billy ta kalli Zeezee tace "she just replied Aneesah fa" Zeezee tace "Aneesah tsayawa kikayi kina kallonta ta mayarmiki da magana mai daci haka" kaman jiran maganan su Aneesa take aiko tai wani tsalle saikan Du'a tahau kimar Du'a dake kuka sosai tana ihu, ko kadan Du'a batasan yanda ake fadaba, kidan Zeezee tabarma Billy tadau wayanta tashiga recording tana dariya tace "goo Aneesah yauwa yimata lilis joints dinta zaki dinga duka da wajajen kayan alatun damage her face" ganin Aneesah na neman saka mata hannu a idanu gatada kumban kari datayi na birthday nada ta ture hannunta tana kuka sosai tarufe fuskanta gwanin ban tausayi, ita kanta Aneesah karfinta yakare ma wajen dukanta dan duka ba'a maidamaka da martani is tiring, taji duk gabobin jikinta sun sage amman taki denawa sabida yanda kawayenta ke hyping nata, Zeezee tace "sumarda ita ga tabarya chan" dagudu tasaki Du'a tai wajen tabaryan zata dauka kenan wayanta yashiga ringing dasauri tai wajen wayan tace "wake kirana" ganin yan ajinsu ne yasa tadauka, dagokai tayi takallesu tace "test wlh" dasauri suka yarda robobin kowa yadau jakanshi Aneesah ma tadauki nata duk sukai gate, juyowa tayi takalli Du'a dabata motsin kirki akasa tajuya takalli Zeezee daharta fita tace "wanchan banzan fa" hararanta Zeezee tayi tace "dalla muje muyi test muka dawo masan yanda zamuyida ita" fita tayi daga gate din sukaja gate din da kyau sanan suka shiga mota suka tafi.

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

✍️ M SHAKUR

wa.me/+2347012181461

DUK WACCE TA KARANTA BATA BIYABA BAN YAFEBA, THIS BOOK IS 500 PAY INTO 3107021073 AISHA MUHAMMAD FIRST BANK.

EPISODE 5️⃣1️⃣
Wani kalan gajeren suma tayi tana nishi sama sama saikuma chan tabude idanunta batasan ya akayi ba ita datasan dasafe sukazo wajen nan gani tayi rana yasoma sauka komi najikinta ciwo yake mata kaman ba jikinta ba, kokarin tashi tayi amman taji takasa moving leg dinta hakan yasa da kyar ta karkata kanta takalli kafan dataji takasa motsi dashi jini tagani sosai akasan wajen kafin takalli kafan nata ganin kafan tayi kan wani katako da kusa biyu ke jikinshi kafanta na kanshi kusa biyu sun chaki kafanta sun nutse duka aciki, wani irin fashewa dawani mugun kuka tayi danji tayi tabama kanta tausayi wanan wani kalan rayuwa ne? Eh thought she will forever be happy awanan Abujan, who will save her anan tsakiyan dajin ya taimaka mata ko rarrafene tayi ta tafi gida, da kyar ta iya buda baki tadanyi ihu cikin kuka tace "ataimaka min dan Allah" ko motsi bataji sai kukan tsuntsaye danda alamu gidan gonan ma abandon one ne dan babu wani abin arziki aciki, sake dagokanta tayi kadan ta kwala ihu. "ataimaka min" wani kalan tsoro taji yana shiganta dan tasan a daji take tafashe da kuka sosai...

Wasu gayune su hudu ke tafiya rikeda gorunan coke amman duk maihankali ya kalli goran ya kallesu yasan ba coke bane acikin goran ba idanunsu yay jajir suna tafiya suna layi, gasunan looking neat dan kana ganinsu kasan ba all this almajiran masu shaye shaye bane, kaman daga sama sukaji ihu ataimakenin Du'a duk tsayawa sukayi suna kallon kansu, daya daga cikinsu yace "kai Baaba na kwale ne koko da gaske ihun yarinya naji" atare sauran sukace "baka kwaleba Baaba muma munji" kalle kallen wajen suka shigayi suna layi dan abuge suke dukansu kafin su sakejin ihunta akaro nabuyi nan suka shiga neman saitin inda sukejin ihun.
Chapter 61 · 0% Book details