← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 109

Sashe 50

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 6 min read

Akofar Gidan yay parking hakan yasa ahankali tajuyoda kanta takalleshi kaman yanda shima yake kallonta, ajiyan zuciya tasauke ahankali sanan tabude kofan motar tasa kafa tasauko kana ganinta kaga wacce keda damuwa sosai bude gate din gidan tayi tashiga, security zai tsareta tace "please I don't have time for this, wajen mutane gidan nazo" yanda tai magana yasa yakasa cemata komi tashiga, ahankali tai sallama tabude kofan falon tashiga, Dad ne yana sanye da manyan kaya dan fitowan shi kenan zai fita aiki ganin Asad da yanzu ma yashigo side din yazauna a dinning yana hada coffee yasa yay dinning din, jin sallama da bude kofa yasa atare dukansu biyun suka juyo suka kalli kofan, turus Ammi dake saukowa kasa rikeda hulan Dad tayi ta tsaya, cikeda mugun mamaki tace "Zai.....nab....kece ko gizo idanuna kemin" tai maganan tana saukowa da sauri tai hanyar kofa batai watawata ba ta rungume Mami tace "oyoyo saukan yaushe" tai maganan tana sakinta tajuya takalli Dad da Asad tace "Alhaji don't tell me baka gane Zainab ba Yar Hajiya ce Maman Du'a" dawani irin sauri Asad yadago kai yakalleta, tahowa Dad yayi yana murmushi sosai yace "Zainab ido kanga ido dama bakida zamunci" murmushi tayi na dole saikuma hawaye, hannu tasa tagoge hawayen dasauri zatai magana kuma saita fasheda kuka sosai, dawani irin sauri Ammi tarike mata kafada tace "subhanallahi Zainab menene come, sit" tazaunar da ita kan kujera tana kallonta tace "menene" cikin tsananin damuwa tace "Hajiya nazo wajenku ne sabida nasan Mama zataji maganan ku zata saurareku cemin tayi nazo mata gidama bata yafemin ba, mutanen nan sunaso su karbi yarsu Kakan su ta matsa a dawo da ita gida, nama Mama bayani namata namata taki ta fahimceni, i don't know what to do, Baban Du'a ma na waje" dasauri Dad yace "assha maisa baki shigoda shi ba, je dauko mayafinki Wife mutafi wajen Hajiya" gyadamai kai Ammi tayida sauri tawuce tai stairs tana kallon Asad da kanshi ke kasa kaman baimasan me ake afalon ba, ko 1min batayiba tafito, Dad yace "kutaho to" dagata Ammi sukayi suka fice.

Cikin mutunci sosai Dad da Abba suka gaisa sanan yamusu jagora yace "bismillan ku muje" shiga gidan sukayi Abba na gaba, da Sallama yabude kofar falon yashiga, Grandma na zaune kan kujera tasanya glasses dinta a idanu tana aiki a sysyrwm dinta, jin sallama yasa tajuyo, ganin Mami da Abba tareda Dad da Ammi yasa ta ijiye system dinta agefe tamike tsaye zatai magana dasauri Abba ya tsaya agabanta yace "Hajiya aikin daukeni amatsayin danki ko, sanan kina fadi naji, inason sabida ni ki sauraresu dan Allah Hajiya kinji" Mami Hajiya ta kalla da kanta ke kasa takasa hada ido da ita, sai Abba dashima kanshi ke kasa cikeda girmamawa sanan tadauke kanta takalli Dad tace "Baban Asad kasan ina bala'in ganin mutuncin ka and kaman yanda kafadi nadaukeka amatsayin d'ana dan haka listen to me and obey me, kaga mutanen nan biyu" tanuna Abba da Mami tace "inhar maganan Du'a yakawosu gidan nan ai nariga nafadamata awaya, bazan bayarda yarinyar nan ba, Du'a tagama rayuwan datayi agidansu har abada, na gayamata nakuma gayama yayanta Muhammadu yakara sanarda ita bazan bada yarinyar nan ba bazan bayarba" dasauri Ammi ta tashi ganin Hajiya tadauki zafi sosai tace "Hajiya calm down" cikin fushi sosai tace "don't tell me to calm down, sunason yarinyarne suka azabtar da ita, yarinyar dabaya lissafata cikin yaranshi, sun kulle yarinya, Du'a became so depress, sunyi depriving yarinya of her right, na education, bata iya komi an yaa mace ba, bata iya girki ba, yarinya sun maidata doluwa mara wayau, yarinya yar 15yrs yanzu zata iya saida Du'a, sun cutar da Du'a shine yanzu sukeso su dauketa su maidata gida sabida wacce tace akoreta da farko tace yanzu adawo da ita to wlh wlh kura yay kadan afadan giwa" Ammi karan kanta saita taji tsoro tunda take da Hajiya bata taba ganin bacin ranta da bala'intaba sai yau......

Sosai Du'a kejin hayaniya wanda tunda tazo gidan bata tabajin irinshi ba, tashi tayi dagakan gado gabanta nafaduwa hakanan ahankali tabude kofanta muryan Grandma taji dasauri tafito, jin maganganun da Grandma take duk akanta ne yasa tai hanyar stairs din tana tafiya ahankali, hango Mamin ta da Abban ta, da Ammi da Dad, saiga Grandma a tsaye tana masifa sosai yasa taji jikinta yafara rawa, su Mami sunzo su komarda ita, wani irin kuka ne yazo mata dasauri tasa hannu ta toshe bakinta tahana kukan fitowa, saikuma tajuya da gudu tai dakinta kaman mahaukaciya tana wani irin kuka kaman wacce ke hauka, memory gidansu yahau flashing akanta, rawa jikinta yafara sosai tace "no....no oooo" wani irin bude kofan sip tayi jakan goyonta na makaranta sabo da sum sayo ta fizgo kome tagani turawa take ajakan, gyalen abayan dake jikinta tadaura ta yana akanta sanan ta goya jakan tana kuka sosai, fitowa daga dakin tayi tana kalle kalle saikuma tasake komawa dakinta tai wajen window dakin, bude window tayi tana kallon kasa dan abene take, wani irin fashewa tayi da kuka tana goge idanunta da bayan hannu tace "bazan koma gidan nan ba, bazan koma ba, nooo" kawai tahau kan window kaman wanda aljanu suka shiga, runtse ido tayi kawai tai jumping tundaga saman nan har kasa aiko tafado timmm kan grass carpet din dake wajen wani irin bugewa tayi ahannu da kafa amman bata damuba ta tashi tana kuka sosai tana wani irin dingishi tana tafiya da gudu gudu sauri sauri ko kallon maigadinsu batayiba tabude gate tafice, tana fita tawani irin kwasa dagudu rikewa kafanta yayi hakan yasa tai kara, da kyar ta tashi bamatabi takan kakkabe jikinta ba ta kwasa da mugun gudu tana dingishi, Asad da fitowanshi daga Gate kenan da motanshi zashi office lokacin itama tafito ganin tafadi tasake mikewa tana gudu still tana kuka yasa yatabe baki, saka sit belt dinshi yayi ya danna waka yaja motan yana gudu ahankali.

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

✍️ M SHAKUR

EPISODE 4️⃣3️⃣
kafin yakai gate din estate dinsu harta wuce tayi titi tana gudu sosai, fita yayi daga estate din yana jiran traffic light abashi go ahead yawuce, kaman ance yakalli side din left dinshi, ganin yanda take gudu tana dingishi tana kuka sosai yasa yadanyi jim kaman mai tunani, maganan Ammi ne yafadomai rai datamai ranan nan what if kanwar kace su Rahima da Aneesa, yatsine fuska yayi ya karya kwana yaja motan dawani irin mugun gudu, saura kiris yabugeta akan titin hakan yasa ta tsaya chak ganin mota yasha gabanta tana goge hawayen fuskanta tana kallon motan dayake tinted dan bata iya ganin naciki, saukar da glass din motar yayi yana kallonta fuskanshi babu ko alamun strictly yace "get in" girgixa mai kai tayi jikinta ko'ina narawa saikuma tafashe da mugun kuka sosai akan titi tace "dan Allah dan Allah kabarni natafi, Dan Allah Dan Allah Dan Allah narokeka Ya Asad" tunda take bata taba kiran sunanshi ba sai yau, jin yanda ake bugamai horn akan titi yasa azuciye yabude marfin motan dawani irin gudu tajuya zata tafi sabida dingishin datakeyi yasa taku daya yayi ya dauketa tana ihu ko kallon mutanen dake titi baiyiba yabude baya ya jefata ciki yay locking car, sanan yashiga gaba yaja motan dawani irin mugun gudu.
Chapter 50 · 0% Book details