← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 109

Sashe 34

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 4 min read

Zaunar daita Razika tayi akan gado sanan takoma tarufo kofa dagudu tanadan zaro idanu tace "naga mutumin jiya a falo Du'a biyomu yayi ne" cikin tsoro muryanta dabai gama washewaba sabida yanda tai kuka tace "nima shina gani bansan lokacin da kofi yafadi daga hannuna ba yanzu idan yafadi ma Grandma Yaya zanyi? Wai waye shi? Ya akayi yasan Grandma sosai har yafito daga lungun flawas din falon saman nan eh" hannu Razika tabude itama alamun oho cikeda damuwa tace "oho amman kaman Shemau tasanshi naga ta gaidashi da sauri tana ganinshi kinsan ita tadade tana aiki agidan nan ni ba'a dade da kawoni ba" shiru Du'a tayi har lokacin gabanta faduwa yake, zama kusada ita Razika tayi murmushi tayi takalli Du'a tace "sonshi kike ko Du'a"? wani irin kwalalo idanu waje tayi tace "so kuma" gyadamata kai Razika tayi tace "eh naga yanda kike ta kallonshi jiya ana koranki kinki tafiya kinata cemai thank you for saving my life keda bakima sanshi ba, sonshi kike ko? Yanada kyau sosai wlh gashi dan gayu gashi mai kudi har ana nunashi a TV, sonshi kike"? Girgixamata kai Du'a tayi tace "a'a kawai nasanshi ne tun a kano, shine yataba cironi daga rijiya saisa dana ganshi nace sainaje namai godiya" gyadakai Razika tayi da gamsuwa tace "to Allah sa shiyace yana sonki wlh danaji dadi" dan daure fuska tayi tace "ni banson maganan nan" yatsun kafarta dahar jan dasukayi yasoma washewa takalla tace "bazakije office ba? naga yatsun harsun washe kinga yau Monday fashi ranan Monday is a serious offense" Yatsun itama takalla tace "yadena zafi, tayani zabomin kaya kinga banda lafiya saina shirya natafi" hannu Razika tasa ta dungure mata goshi tace "kewai mai wayau ko" tai maganan tana zuwa gaban wardrobe dinta wani ja da bakin abaya taciro mata sabo fill tana kallonshi tace "wowwww abayan nan yay bala'in kyau, Hajiya tasai miki"? murmushi tayi tana girgixa kai tace "Aneesa tazaban min ranan damukaje shopping yay kyau" warware rigan Razika tayi tace "wlh kam yayi kyau kai yayi bala'in kyau ma, oya tashi kizo ki shirya" tashi tayi tana kallon yatsun nata jin sundena mata zafi, wucewa Razika tayi tafice daga dakin tace "saikin fito" tom Du'a ta amsata tana kokarin cire rigan dake jikinta sanan ta ijiye ta shirya cikin rigan kafin tazo gaban madubi tatsaya tana kallon kanta for the first time yau taga kyanta da ake fadi ja da bakin color ya bala'in mata kyau, zama tayi tana daukan ribbon parking kitsonta tayi a tsakiyan kan yay kaman acucu gashin goshinta sun wani irin bala'in kwanta, sanan tai rolling gyalen abayan, man baki talakata ta shafa a lips dinta dayay wani pink sanan ta tashi tana hada jakanta tadau pad tasaka dakomi da Grandma takoyamata sanan tazura wani flat takalmi mai budadden sama daya bayyana fararen cute kumbunan kafanta, ahankali tasa hannu tabude kofarta tana lekawa gabanta nafaduwa ganin babu kowa yasa takarasa karasawa wajen bene tashiga tafiya ahankali, Grandma kadai tagani zaune tana fere apple dawani karamin wuka, dago kanta tayi jin sahun tafiyanta, kasa daurewa tayi sabida yanda tai kyau tace "Masha Allah tubarkalla Du'a kinyi kyau sosai har kafan ya warke ne"? murmushi tayi tana zama kusada ita tana gyadamata kai, Hajiya tace "to dama banda shegen shagwaba naki ruwan lipton wani konewan kirki ne, kedai kawai rakin ki yay yawa, tashi ki tafi aiki yau Monday aka ciki taran latti baruwana wanan da Ogan ku yadawo ai kunbani" dan zaro idanunta tayi sai yanzu ma ta tuna Sharif yacemata this Monday Ogan su zaiyi resuming office, zumbur tamike tace "bye Grandma" murmushi Grandma tayi tabita da kallo sabida yanda yarinyar tai kyau tace "ayi addu'an fita daga gida Allah tsare" tsalle tayi kaman yar yarinya tace "tom" "kidena tsalle" Grandma tafadi tana murmushi ganin yarintarta.

Motan Grandma tashiga zama tayi driver yajata sai alokacin ma ta tuna batai breakfast ba, har campanin yakaita, yau kawai taji tana having wani irin wired feeling kaman tace sujuya su koma gida kartazo aikin.

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
Chapter 34 · 0% Book details