Sashe 77
Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kaka data kasa daina kallon Du'a ne tace "taho nan naganki yarinyar nan" ahankali Du'a tadago kanta Grandma takalla danko kadan jininta bai hadu dana kakarta ba, gyadamata kai Grandma tayi alamun taje hakan yasa ahankali tamike tsaye taje wajenta ahankali tazauna akasa, hanci Kaka taja agaban kowa jin wani hadadden kamshi da Du'a keyi tace "banda kyau har kamshin fata Allah yabaki ne, lallai nidai Allah ma yasani haryau nakasa yarda ke diyar Muhammadu ce billahillazi" Kaka tai maganan tana kama hannun nata tarike sanan tace "Ya sunan mijin naki" ahankali murya chan kasa tace "Asad" gyadakai Kaka tayi tace "tabbas haka Muhammad Muhammadu ko yafadi mini, dana aiko adaukoki akawomin ke chan Ikara ki zauna dani shine kikace ke aure kikeso, shikuma dayake uban naku wani zubin bakai gareshi ba sai ko ya aurar dake, ai shikenan tunda auren kika zaba, nidai addu'ata Allah yasa karya gano kinada jinin ifiritu ajikinki yasakoki tunda mun samu kin sami miji kin aure" daidai nan Grandma tace "kinga Kaka jikata batada jinin ifiritu jinin danki gareta, kumama bakisan wani abuba, Kakan Babana usulin shi balaraben Egypt ne, yazo naijeriya yay aure, to daganan ne abin yatafi muka duk aka haifomu bakake sabida matayen dasuka aura, Du'a tadauko jinin dangin ne na kakanni" baki Kaka tabude ganin Grandma na taran mata numfashi idan tana magana hakan yasa tahadiye sauran maganan tace "asheee" murmushi Grandma tayi tace "eh wlh, yanzu dai kugamacin abinci ayi salla saimu tafi sama kuga akwati" takalli Mom daketa kallon Du'a dake wasa da yatsunta tace "akwai wani abu dakike bukata akawo miki Maman Hamad" murmushin yake Mom tayi tace "a'a wlh" lafiyayyen abinci aka kawo musu daban daban ga namomi zuku zuku, bawai basacin abinci agidansu bane amman kaga wani abincin sai agidan wane da wane ga gasasshiyar rago, dayan flat din da Grandma tasa aka gyarama su Abba suna dawowa wajen aka kaisu dan su saki sanan aka kaimusu nasu abincin, zuzzuba abincin akayi sanan Grandma takalli Du'a tace "oya tashi kici abinci tareda yan uwanki" tanuna mata su Hawwa dasuka zubo abincin su a plate tare, gyadamata kai tayi tai wajen atsakiyansu tazauna ahankali sanan takalli Nana dake kallonta ahankali tace "Ya Nana" dan murmushi tamata tace "Du'a ya kike"? murmushi tayi tace "lpy lau" sanan takalli Hawwa dake kallonta tace "Ya Hawwa" murmushi taga Hawwa tamata tace "Amarya Du'a" dan murmushi tayi sanan tadau spoon dinta sukahau cin abincin bini bini Mami na satan kallon Du'a da tuni Grandma ta lurada ita kuma tasan bakomi take kallo ba illa girma dakuma kyau da Du'a takara, saida sukaci suka koshi sanan Du'a takallesu tace "kutashi muje dakina kuyi wanka ku shirya" basuyi musu ba suka bita sukai sama duk aka bisu da kallo, akwatinan dasuka gani afalon sama sukabi da kallo kusan set 15, sanan suka shiga dakinta shima kallon dakin suka shiga yi, skirt Hawwa tacire tai bayi dagudu tace "zanyi fitsari wayyo karya zubo" murmushi Du'a tayi sanan takoma kan gadonta tazauna, ahankali taga Nana tazo tazauna kusada ita hakan yasa tadan dago kanta ta kalleta hada idanu sukayi, murmushi Du'a takarayi tasaukar da kanta kasa, ahankali Nana takira sunanta."Du'a" dasauri tadago kanta takalleta, hannun Du'a Nana takama tace "nadade ina neman hanyan dazan kiraki nabaki hakuri, I am very sorry Du'a akan duk abubuwan danamiki akan Muhsin, Muhsin is nothing but a jerk nima daga baya nagane haka, bake kadai yabi ba, infact namaji dadi abinda yafaru badadan keba da yanzu na aureshi ina cikin bakin ciki, kece sanadin dayasa Nagano wayeshi, ashe duka friends dina na school daya sani duk yana dating nasu, mayen mata ne na karshe kuma dan iska, I was so blind by his love bangane hakan ba, kiyakuri kinji Du'a" Gyadamata kai Du'a tayi ahankali tana murmushi, Nana tace "bayan Ya Hamad yadawo daga kawoki Abuja yafadima Abba komi, saiya yakulle Uwani, Mai gadi dashi Muhsin din a police station, akayi case sosai sanan aka bashi hakuri yasakesu da sharadin ko akofar gidanshi yasake ganin any one of them hukuma zasu raba shi dasu ahaka case din yakare" gyadamata kai Du'a tayi daidai Hawwa tafito, tashi Nana tayi tashiga bathroom din, Hawwa takalli Du'a tace "kin kara kyau yarinyar nan, yaushe rabon damuyi fada" dan murmushi Du'a tayi tana mamakin yanda duk suka chanza toko sun kara hankali ne oho, salla sukayi sukahau bama Du'a labarin kano daga tai murmushi saita gyadamusu kai, kwala musu kira da Mom tayi yasa suka fita banda Du'a datai zamanta, duk afalon saman suka taru ana bude kayan Du'a dababu na Nigeria ko daya, daga akwatin har atampopin dakomi ma, Mom duk yanda taso kasa boye bakin cikinta tayi, harsaida Kaka yar bala'i tace "kekuma kowa na tofa addu'a bazaki tofa ba" murmushin yake Mom tayi dan daga ganin akwatin wani mai kudin Abuja Du'a zata aura, itada ta dauka wani mai gadi ne kokuma lebura haka zata aura, amman wanan akwatuna haka set 15, kowani saiti nada 3 dan designers akwati ne ba irin na Nigeria ba, ahankali tace "Kaka yarinya tai goshi Allah sanya alheri" da karfi Grandma tace "Ameen" sanan tanuna ma kowa dakinshi asaman dan suje suyi wanka su huta, kowa yatafi, su Hawwa suka koma dakin Du'a duk suna mamakin akwatin Du'a dan basu saba ganin irinshi a kano ba.
Dakin Grandma Mami ta shiga, waje tasamu kusada Grandma tace "Mama Yaya Muhammad yace jibi zasu shigo ko ranan jumma'a" murmushi Grandma tamata tace "ashe kunyi waya haka yagayamin" shiru Mami tayi tana kallon mahaifiyar nata tasan har yanzu fushi takeda ita, ahankali tace "Mama dan Allah kiyakuri kiyafemin komi dan Allah" juyowa Grandma tayi takalleta kaman tai shiru saikuma tace "naso namiki yanda kikama Du'a yarki ne, nima na nuna miki baki da amfani kaman yanda kika nunama yarki, but I guess bazan iyaba Zainab" sauka Mami tayi daga kan gadon, guiwanta tasauke akasa tana kallon mahaifiyar tata, ahankali tace "dan Allah kiyakuri kiyafeni" hannu Grandma tasa tadagata dan tanason yarta bakadan ba, zaubarda ita kusada ita tayi tace "Na yafemiki komi ya riga yawuce Du'a tariga tai aurenta, ranan lahadi war haka ai tanama gidan mijinta so bakomi, yanzu dai akwai magungunan ta wajen Jummai, kinsan zan shiga hayaniya ba lallai nasa idoba kisamata ido makesure tashanye komi sanan taci abinci dan bata iyacin abinci har yanzu, akwai turaruka ma anan zaku dinga mata" gyadama Grandma kai tayi tace "to Mama" ahankali Grandma tace "kinga yaron daya wahala shi Allah yake kyautatamawa akarshen sabida ya wahala yay hakuri, Allah yabama Du'a miji, idan kinga yanda yaron kesonta dudda yana kokarin boyewa sai kinyi mamaki, ko bani duniya ayau Zainab na yarda da Asad zai kulada Du'a kaman kanwarshi wanan shaidar nimishi ita" murmushi Mami tayi hankalinta nakara kwanciya tace "Alhamdulillah".
Wuraren 4 Dad yakira Asad dabayanan awaya, bai daukaba akaro na biyune yadauka, Dad yace "kana office ne" cikin muryan nan nashi na baison magana yace "ganinan zan shigo gida" katse wayan yayi yashigo yay parking sanan yafito yana kara kallon yanda ake aikace aikace ana decorating gidan for event sanan yay falonsu, Dad yagani zaune da kowa afalon ga wasu kwalaye sweet, goro tabarma da sauransu akasa duk ana magana, ganinshi yasa akai shiru yaran duk suka gaidashi, karasawa yayi yazauna kusada Sharif ahankali yana yatsine fuska danyagaji, harara Anty Turai ta watsamai, murya chan kasa yace "Dad gani" murmushi Dad yayi yace "My Son the latest ango, anyway family din wife dinka gabaki dayansu sunzo suna around, mahaifinta da kannen mahaifinta maza biyu, da macen, sai matanshi biyu da Maman Du'a da kishiyar, dakuma duka yaransu, da mahaifiyar Babanta Kaka su, inaso dakai da Sharif dawani abokinka ku shirya bayan magrib kaje kai gaisuwan iyaye ka gaidasu sanan kutafi da all this, bayan sallan isha'i mahaifinta da kannensu wai zasu tafi masaukin su, nayi nayi dasu su kwana tunda sunada nasu flat din, amman yace bazai iya kwana agidan suruka ba, so ku shirya karka bata musu lokaci kaji" gyadamai kai yayi, Sharif yace "tashi muje mu shirya, nama riga nakira Jabir" yatsine fuska yayi yatashi, Rahima nawani dan murmushi tana mamakin Asad kaga yanda yakeyi ne kaman ana tursasashi Ammi sai kallonshi take da tsoro karyace yafasa saisa wani sabon lallabashi take kwanan nan Allah sarki Ammi batasan danta yafi kowa son bikin nan ba.