← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 109

Sashe 55

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 7 min read

Motan Grandma tashiga bayan tagaida direban dake tsaye gaban mota, shiga yayi yajasu bini bini yana kallonta ta glass din motar dan arayuwa baya gajiya da kallo jikan Hajiya nan mai kama da balarabiya, shigowa kampanin sukayi yay parking a parking space ya kashe motan fitowa daga motan tayi ahankali sanan tasa hannu tadauki jakanta dakekan kujera sanan takalleshi tace "thank you Uncle" sanan tamaida kofan tarufe tajuya tana tafiya ahankali tana kalle kalle, sanan takai gaban entrance tashiga, tana shiga receptionist din wajen dake kokarin kwasan wasu files jikinta narawa takalli Du'a tace "why are u late Miss Du'a? Anyway there's no time for that kiyi sauri sauri kije hall a 2nd floor, Mr Asad is having a meeting with all staff duk ana wajen hurry" yanda tai maganan jikinta narawa tana parking wasu files yasa dasauri itama Du'a tajuya tai bene Receptionist din tabita da kallo, second floor din takai babuko kowa awajen alamun duk ana meeting ganin wani babban kofa guda biyu haka da aka rubuta hall ajiki yasa tai wajen, ahankali ta tura kofan ganin ko gezau baiyiba yasa tasa duka karfinta tawani irin tura kofan kofan yawani irin budu doors din sukai slamp din bango jikake bam ba dayasa kowa naciki yajuyo yana kallon kofan harda Asad dake magana agaba tashiga ciki tana sauke ijiyan zuciya, Babban Hall ne sosai kaman irin na school dinan kowa na wajen harda security, na gate kawaine basa wajen, ga Asad dake sanye dawani dark blue suit yay azababben kyau ya gyara gashin shi tsaye agaban hall din gaban wani speaker haka dake kan mumbarin yana bada speach sai Sharif dake sanye da suit mai ruwan toka zaune kan wani hadadden chair agaban hall dinma da MacBook akan table dinshi da byro alamun ana aiki ne shima, shigowanta da yanda ta bude kofan yasa yadago yana kallonta, wani kalan rawa jikinta yayi hakan yasa bakinta nadan rawa sosai tabude baki cikin yar zazzakan muryanta tace "Sor.....ry" tai maganan tana saukarda kanta kasa first kujeran dake right side dinta taja tazauna hakan yasa kowa yamaida kanshi yajuya, ahankali Asad yadaga hannunshi fuskanshi babu alamun wasa ko kadan, agogon hannunshi yakalla tara saura kwata hakan yasa yasauke hannunshi bakinshi na saitin speaker yace "Miss Du'a" dawani irin sauri Du'a tadago kanta jin sunanta a speaker da hall din ya amsa tashi tayi dasauri kirjinta na dukan uku uku takalli Asad din dake kallonta fuskarnan ba rahama yace "u are late and in my meeting I don't welcome late comers, excuse us" yay maganan strictly, gyadamai kai tayi tasan menene excuse but batagane kalan excuse din dayake nufi ba anan, ahankali takoma tazauna tana tunani kaman daga sama taji tsawanshi. "I said leave this hall or are u deaf" wani irin firgita tayi batasan lokacin data zabura taja jakanta jikinta na rawaba kanta akasa sabida yanda ake kallon ko kadan bata lurada receptionist data shigo da lots of files da Asad requested for ba, wani irin karo taji taci da mutum tai baya kan kaceme receptionist da dama files din sun mata yawa a hannu hill din kafanta ya turgude tayo gaba kafin tafado files din suka fara zubowa kan Du'a da already tazube akasa, ihunta ma kasa fitowa yayi sabida files din dake kan fuskanta saiga receptionist da itama tafado kanta, dawani irin sauri receptionist din ta tashi jikinta narawa tace "oh my God, oh my God I am so sorry" tai maganan tana kwashe files din dake kan jikin Du'a, ahankali tadaga hannunta tasa hannun ta ture files din idanunta har sunyi ja ga hawaye, ijiye files din reception din tayi takai hannunta kan fuskar Du'a tace "oh my God I am so sorry, are u hurt? Stop crying" ahankali Du'a ta lallaba ta tashi tana share fuskanta da duk kiran files din kekai, sanan tawuce tafita batare data juyoba, 5th floor dinsu tawuce taje bathroom dinsu wanke fuskanta tayi tass sanan ta wanke hannunta ta kakkabe jikinta tana turo baki, kaman tawuce ta tafi gida amman tunawa da maganan Grandma da inyacee get out bawai koranki yayi ba kuma karta sake irin abu da tayi last time yasa ahankali tabude kofan bayin tafito sanan tawuce office dinta, ahankali tabude office din tashiga zama tayi ahankali tana kuyi akan kujeranta saikuma tai murmushi tanason dan office dinan, wayanta taciro tana kallo rabonda tashiga watsapp kotama kunna data harta manta tun kafin birthday din Aneesa dan ita wayan da chatting dinma bawai ya dadata da kasa bane dan bamata sababa daman Grandma ce ma ke kiranta wani zubin yan gidansu babu mai kiranta ko Mami bata kiranta saikuma su Aneesah wanda su yawanci chatting ne, ahankali ta kunna data, ajiye wayan tayi tadauki kukan da Razika tasamata abinci budewa tayi ganin nama asama zako zako yasa tai wani irin murmushi tadau guda daya takai baki sanan tadau wayanta da dayan hannun ta shiga watsapp ganin messages dinta na shigowa, tana shiga taga messages din duka daga groups dinsu na yammata ne wanda su Aneesah suka sata, daman shi kadaine group din datake ciki, dasaurinta ta danna ta shiga group din the first abu datagani shine Aneesah removed you, dan zaro ido tayi tace mistake ne, sanan idanunta suka sauka kan message din Mariya tasa announcement group Du'a is no longer our friend in fact she's even an enemy, dan dariya Du'a tayi dan she always known Mariya to be a bit wild and Crazy, Rahima da Aneesah sunfi sweet da kirki da iyamagana, tacigaba da karanta messages din tanacin namanta, wata daga cikin kawayen su tace "Du'a Du'a wanan kyakkyawan yarinyar damuka gani a birthday dinku dako kallonmu batayiba, metayi muku?" taga yan group din nata fitowa suna tambayan meta musu, Mariya ce tasake fitowa tai reply da "she's a snitch, a hypocrite, and very cruel, kunsan yanda mukeson yarinyar nan kuwa? We share all our things da ita, har saka yayyanmu muke yabata kudi muje shopping da ita shine zataci amanan mu" wanan karan dan fadi gaban Du'a yayi dan she understood this is not more a joke, yan group din sai tambaya suke metayi metayi, saiga Aneesah tafito tace "she stole my boyfriend tama aureshi dazu aka daura musu aure, bayan tasan ina sonshi he mean the world to me this girl knows everything about me shine zataje tabi tabayana ta yaudaran, wlh wlh bazan taba yafemata ba duniya walahira, Allah saiya sakamin yar iskan yarinya Aljanna kawai mayya, barima nabaku labari daga ubanta har uwarta duka nadaman haihuwanta suke basa sonta anma kawota nan Abuja wajen kaman just to save her ass ne, yarinyar that has been bad luck and wahala to her parents uban waye bazata tababama, shegiya mai bakin jini, asararra aljanna kawai" dawani irin gudu tafito daga group din takasa karanta sauran messages din kuka tafara ahankali zaginda Mariya tamata baima bata haushiba na Aneesah ne yamata ciwo harda kawo maganan gidansu, ahankali tasake daukan wayan tana share hawayen da hannun riganta ganin not just group tanada individual messages from different numbers da duk batadasu yasa ahankali tabude na first one wanda shi dasafen nan yashigo. "This is Vee Aneesah's friend, you this bastard girl how dare you kikamata snatching boyfriend eh, wayeke ke yar gidan waye keda ubanki of all people HOD ne, kinsan waye uban Aneesah kinga gidan masu kudi shine kike neman space, bakisan ba'a ma yammatan Nile snatching boyfriend ba, wlh wlh kin shiga uku watch out for your self, mayya kawai mai kamada aljanu duk maitanki kanki kawai zaki iyaci munfi karfinki munbaki 2days kirabu da Asad inba hakaba wlh saimun kasheki" wanan karan sakin wayanta tai akan table ta tashi dagakan kujeran takoma gefe tana kuka ahankali, bude kofanta da akayi yasa tadago kanta dasauri, hada ido tayi da Asad dake kallonta dawani irin sauri tasa bayan hannunta tana share fuskanta lips dinta har rawa suke tace "good morning Sir" dauke idanunshi yayi daga kanta yabi office din da kallo kafin idanunshi yasauka kan table dinta da jaka kekai ga kula abude na abinci, ga naman da aka faraci akan table ga wayanta da screen din ke haske sosai karan messages na shigowa nata shigowa wayan, ganin ya tsare wayanta da kallo yasa dagudu tai table din tasa hannu ta dauki wayan taboye abayanta tanajan hanci trying to stop the kuka kanta akasa.

Hannu yamika mata murya chan kasa yace "give me the phone" girgixa mishi kai tayi ahankali tace "is mine" danta dauka yadauka wayan office dinsu ne, cikin harsh tone yace "I said give me the phone" dago kanta tayi ta kalleshi ganin idanunshi da babu wasa aciki yasa kaman am tsinke mata wani abu ajiki ta zagayo duk yana binta da kallo tazo gabanshi ahankali ta tsaya sanan taciro wayan daga bayanta ta mikamai, karban wayan yayi yana batarai yace "clear this table sort yourself out and meet me in my office in the next 10min" sanan yajuya yafita daga office din.

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

✍️ M SHAKUR
Chapter 55 · 0% Book details