← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 109

Sashe 52

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gida Ammi ta shiga, ganin Ammi yasa Asad yayi kaman irin zai tada motarnan yafita ne dawani irin sauri ta bubbuga kofan motan tace "Asad wait wait" saukar da glass din motar yayi yace "Ammi what is it am late fa office zani" dasauri tace "Asad wait kashe motan kaji I have something very important to tell you, kashe kashe kafito" yanda yaga jikinta narawa yasa ya kashe yafito yana kallonta yace "is everything okay maiya faru Ammi"? Hannunshi takama tarike duka biyun tace "look at me Asad we don't have much time but we will go into deep details later,Asad kasan nina haifeka ko, nai rainon cikinka na haifoka na tarbiyantan dakai zuwa what u are today nataba tambayanka kabiyani ko kasakamin"? dasauri yace "no Ammi" ahankali tace "tom I need u to do something for me, taimako zakayi kuma duk wanda yataimaka ma wani Allah zai taimaka mishi, at this point wata yarinya her life depend on u wlh Asad, please Asad dina, and just know this bazan taba saka kai abu mara kyau ba so u should trust me" kallonta yake kaman wanda bai gane komiba yace "Ammi maizanyi" danshiru tayi kaman wacce ke shakkan fadamai tace "inaso ka auri Du'a jikan Hajiya" dawani irin sauri ya fizge hannunshi yay baya dasauri sauri yace "no way! Ammi, kinsan mekike fadamin kuwa" cikeda damuwa Ammi tabiyoshi hannunshi tasake rikewa tace "Asad bamu da time ana jirana naso dakaine dan girman Allah that's just the only thing I need u kamin right now, any other thing we will discuss it later, at this point kawai u need to save her ne please Asad dan girman Allah idan kana kaunata ni mahaifiyarka, Asad dan darajan Allah karka zubamana kasa a idanu, As......" Ammi! yawani irin kirata da mamaki, cikeda damuwa tace "Asad lemme kneel for u toh halan sainai hakan zakayi" takai gwuiwanta zatasa akasa, dasauri yarike mata hannu yace "Ammi don't kneel for me" kaman zatai kuka tace "Asad I have to kneel for u inhar hakan zaisa kayarda ka taimaken ka auri yarinyar nan nagayama we will discuss d matter later yanzu kawai ina bukatan ka ceci rayuwanta ne inba hakaba tafiya da ita za'ayi, gwara na duka maka Asad na rokeka" tai kaman zatakai gwuiwanta kasa dawani irin sauri yariketa yace "ohhh ohkay Ammi naji basaikin kneeling ba" dasauri ta tashi takalleshi tace "zaka aureta"? Yatsine fuska yayi yace "yes Ammi for now just to save her kuma sabida ke" wani irin ihu Ammi tayi ta rungume shi tana kissing fuskanshi tanamai addu'a kafin taja hannunshi sutafi.

Sallama Ammi tayi tabude kofa tashiga Asad biyeda ita kanshi akasa yana cikin suit din aiki, kallo daya Abba yamai yagane yaron dan yaga program din dayayi na youth a channels television news, zama Asad yayi kanshi akasa anatse yace "ina yini Abba" ahankali Abba yace "Alhamdulillah kaine Asad"? Gyadamai kai yayi ahankali yace "tell me about ur self Asad" danshiru Asad yayi sanan ahankali yace "sunana Asad Abdullahi Kitse, I am 33yrs old, nai karatu a UK inada 2 degree my first degree is medicine I am a Doctor, sai na biyun business Administration, currently yanzu bana aiki as a Doctor, business nakeyi inada company kaina" yay shiru daidai nan, gyadamai kai Abba yayi sanan yadaga kai yakalli Grandma dake kallonshi yace "kin yarda da tarbiyan Asad Mama" gyadamai kai tayi tace "a hannuna Asad ya girma nasan waye Asad, na aminta da tarbiyan yaron nan dari bisa dari" gyadakai Abba yayi babu ko alamun wasa tattare dashi yakalli Asad yace "zaka auri y'ata Du'a Asad"? shiru Asad yayi, ahankali Mami tataba Abba, kabarda hannunta yayi batare daya kalleta ba still yana kallon Asad yace "zaka auri y'ata Asad"? kaman Asad bazaice komiba har lokacin kanshi akasa ahankali yace "eh zan aureta Abba" gyadakai Abba yayi yakalli agogon dake daure a hannunshi yaja daya saura, dagakai yayi yakalli Dad dakenan azaune kaman ruwa yacishi yace "bismillah mutashi mutafi masallaci, Asad bismillah" tashi Dad yayi, Asad ma yatashi duksu Grandma na kallonsu suka fita daga gidan, suna zaune nan shiru afalo aka tada sallan azahar akayi sai sukaji sanarwa ana adakata jama'a akwai daurin auren da makocinmu Sanata Abdullahi Kitse yakeson ku shaida, kafin kaceme kawai su Grandma sukaji ana an daura aure tsakanin Asad Abdullahi Kitse da Du'a Muhammad akan sadaki dubu dari.

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

✍️ M SHAKUR

EPISODE 4️⃣4️⃣

Ko minti biyu basu karaba sai gasu sun shigo gidan da Sallama, Amsasu Grandma tayi suka shigo, kan Asad akasa kowa yanemi waje yazauna, Abba yadade ahaka sanan yay gyaran murya yace "Du'a" dago kanta tayi ahankali takalleshi, anatse yace "zonan gabana" gyadamai kai tayi ahankali jikinta duk yay sanyi sanan ta rarrafa zuwa gabanshi ta lankwashe kafa, hannunta yakama ahankali yarike yana kallonta yace "Du'a you always feel am unjust towards you, and kinsan wani abu u are right Du'a" Yaydan shiru sanan yace "koma yaya kike u are my daughter and hakkinki ne nakira sunanta cikin yarana so" yadan sakin mata murmushi for the first time tunda yashigo gidan yace "I hope this time around I am just dan namiki abinda kikeso, kince kinason aure kuma amatsayina na mahaifinki na aura miki wanda kikeso wanda Kakarki tayaba da tarbiyanshi bama ita kadai ba ko a masallacin anguwan yanzun nan mutane dayawa sun yaba halin Asad din hakan yakara samin natsuwa hankalina ya kwanta danhaka" yay maganan yana zare hannunshi daya daga rikon dayama hannayenta yatura hannun a aljihu yaciro wrap na sababbin 1k guda daya yadaura akan hannunta yace "ga sadakin kinan Du'a naira dubu dari, Allah ubangiji yamiki albarka" batasan mesa na hakanan taji kuka yazo mata kodan sabida wanan ne karo na farko da Abba kemata magana mai tsayi haka oho amman dai jitayi kuka yazo mata, dagakai Abba yayi yakalli Asad yace "come Son" wani irin murmushi Ammi tayi, ahankali Asad kanshi nakasa yataho gaban Abba shima, hannunshi Abba yakama sanan yadauki na Du'a daya rike yasa asaman nashi yace "ga Y'ata Du'a nan nabaka amananta, ka riketa tsakani da Allah karka cutarmin da ita, ka kulada cinta, shanta, suturanta da lafiyanta dan yanzu duka sun tashi daga kaina ko kan Kakanta sun koma kanka Asad, zuciyata ta aminta dakai dan haka nabar muku ita, yanzun Du'a matarka ce halak malak sai yanda kace sai yanda kace ayi za'ayi dan haka, idan kunso kuyi biki ko taro duk ba matsala takace Allah ubangiji yamuku albarka, zan koma gida zan sanarda Kakanki tachan cewa na aurar dake zan sanarda yan uwanki, kibi mijinki kimai biyayya Du'a, Allah yamuku albarka" yay maganan yana zare hannunshi dagakan nasu yanadan murmushi sanan yakalli Mami da idanunta sukai jajir yace "tashi mukama hanyan tafiya" sanan yatashi yakalli Dad dakawai binsu yakeda ido dankomi yafaru akan idanunshi kaman mafarki ne yabashi hannu yace "surukina sai munyi waya, Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa" dasauri Dad yatashi yana kakalo murmushi yabashi hannu da fara'a yace "Ameen Ameen, zamuyi waya muje namaka rakiya" gyadamai kai Abba yayi yakalli Grandma dake zaune awajen ahankali cikeda girmamawa yace "kiyakuri Mama dakomi, zamu tafi" dan murmushi tamai tace "babu komi baban Hamad agaidamini da yara dan Allah barinma mijina Hamad" murmushi yayi shida Abba suka wuce suka fice, dakin yarage saura Mami data kasa tashi da Ammi dakuma Grandma dake kallonta, tashi Ammi tayi tadaga Mami ta rungumeta bakinta tadaura akan kunnen Mami tace "I know what u are thinking right now Zainab karki manta nima uwace, but zanmiki wanan alkawarin inhar inada rai Du'a bazata taba wulakanta na, zan kulada ita Asad ma zai kulada ita amana, namiki alkawarin nan Du'a tariga tai miji bazan miki karya ba she is in a good hands I assure u that" wani irin ajiyan zuciya Mami tasauke dan har kasan ranta taji dadin kalaman Ammi kankameta tayi tace "thank u Anty Zainab" sakinta Ammi tayi tace "yima mahaifiyarki sallama" gyadamata kai tayi sanan takarasa wajen Grandma ahankali ta tsugunna, dauke kai Grandma tayi hakan yasa gently tace "Mama kiyakuri kiyafemin kinji dan Allah" juyowa tayi takalli yarta ta ga mamakinta saitaga tasakin mata murmushi takai hannunta kan fuskanta tace "komi yawuce, Du'a tayi aure tana kuma kusa dani danhaka komi yawuce, tashi kitafi tafiyan ku nada nisa" tashi tayi ahankali Sana tajuya zata fice hartakai kofa tadan waigo tasaci kallon Du'a hada idanu sukayi hakan yasa tai sauri tafice Ammi dake murmushi tabita abaya dasauri, Du'a batasan lokacin data cire hannunta dake cikin na Asad ba tawani irin tashi cikeda murna tai kan Grandma tafada jikinta tana wuntsula kafa Grandma basu tafi dani ba wayyooo Allah na wlh dadi nakeji yayyy, tawani irin kankame Grandma da mamaki yagama kasheta tana murna, tashi Asad yayi ta gefen ido yakalleta sanan yay hanyar kofa batare daya kalli Grandma ba yace "bari naje office Grandma" baima jira respond dinta ba yafita daga falon wani irin makirin murmushi yasaki tareda biting lips dinshi ahankali yace "killing two birds with one stone feels good, ranshi fess kaman fresh madara....
Chapter 52 · 0% Book details