← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 109

Sashe 51

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wani irin mahaukacin kuka take a motan shi kaman yana yankata, takasa shiru, saida yay tafiya mai nisa sosai sanan yakai wani filin kwalo dake kan titi yay kwana ya shiga dan babu kowa ciki, parking motar yayi awani irin zuciye yabude motan yafito yabude bayan motan hannunshi yasa yawani irin fizgota waje sanan yabugata dajikin motan yasaka mata mugun tsawa. "shut up!" ko tari bata karaba gabaki dayan kukan datake daya kusan taushemai kunne hadiyeshi tayi jikinta na bala'in rawa, rasa yanda zatayi yasa kawai saita zube agabanshi tai kneeling looking so helpless and pitiful da zakaji kaman ma kamata kuka, kaman karaman yarinya harwani jiniyan kuka take cikin muryan bala'in tsoron shi tace "Ya Asad dan Allah kayakuri kataimakeni allow me to run, dan Allah Ya Asad karka bari su komar dani kano, dan Allah karka bari su komardani kano, dan Allah dan Allah dan Allah ya Asad dan Allah karka bari su komarda ni kano, dan Allah kataimakeni" yanda take rokonshi jikinta narawa kanta akasa dan tsoron shi ma yahanata ta kalleshi yasa yabitada kallo saikuma yay shiru still kallonta yake, yakai kusan 1min ahaka bazaka taba iya tantance yanayin shi ba yace "stand up" tashi tayi tana sauke ijiyan zuciyan kuka tana kuka, gaba yabude mata yace "shiga ki zauna" shiga tayi batare datai musu ba ta zauna, maida kofan yayi yarufe sanan yazagaya ta side dinshi yabude yashiga yazauna yadade yana kallon filin kwallon yanajin yanda take rera kuka ahankali tana sauke ijiyan zuciya sanan yajuyo ya kalleta yanda riganta yay budu budu duk kasa sabida faduwan datayi, dauke kanshi yayi yamaida gefe yana kallon filin kwallon yace "maisa bakison komawa gida" kaman jira take tafashe da kuka tace "Abban mu baya sona, Mum bata sona, su Ya Hawwa da Ya Nana duk basa sona, Kakan mu bata sona,Ya Hamad kadai kesona agidan" murya chan kasa batare daya kalleta ba yace "waye Ya Muhsin waye Ya Hamad, maisa kowa baya sonki" gabaki daya tabashi labarin gidansu dudda in a childish way ne but he understood everything, sosai take kuka tace "Ya Asad dan Allah kataimakeni kaji, dan Allah karka bari su Abba su koma dani kano dan Allah kataimakeni" tafashe dawani irin kuka mai tsuma rai tana daura kanta akan cinyoyinta, yakai kusan 2min kallon football field din dasuke ciki yake sanan yajuyoda kanshi wani makirin murmushi yasaki for the first time sanan yace "kinason in taimaka miki"? Dawani irin sauri tadago kanta da jajayen idanunta takalleshi dasuke cikemda hawaye, gyadamaikai tayi ahankali tana goge hawayen da bayan idanunta, yana kallonta still yace "are you sure kinaso na taimaka miki"? gyadamai kai tasakeyi cikin muryan kuka tace "eh" tabe baki yayi sanan yadauke kanshi daga kallonta yace "idan kinaso na taimaka miki dole ki koma gida and face ur father and ur Mum" girgixamai kai tayi wani sabon kuka yana zuwanmata tace "wlh zaku komar dani gidan nan dan Allah Ya Asad kayakuri kataimakeni karsu tafi dani" dan juyoda kanshi yayi yakalleta, zubamata mayun idanunshi yayi dayasa taji tahadiye kukan datakeyi tana kallonshi cikin wani irin murya yace "do you trust me"? hakanan taji idanunshi na compelling nata dan batasan lokacin data gyadamai kai ba tace "eh" ahankali yana kallonta yace "I will help you, I have a plan but dole ki koma" gyadamai kai tayi badan tasoba, juyawa yayi yasa hannunshi abayan yazaro wani rag, jefa mata ajiki yayi yace "first thing first clean ur body" dasauri tadauki tsumman ta goge jikinta tass dashi, wani kalan earpod taga yadauko dabatasan na mene ba, gani tayi yayi connecting nashi to wayanshi sanan yajuyo ya kalleta yace "saukar da this thing kasa" yanuna mata gyalen kanta baki, kallonshi tayi ganin yamaida hankalinshi kan wayanshi da abin daya rike a hannu yasa gently takai hannunta taja gyalen abayan kasa, yan kananun kalabanta suka wani bayyana, ga kwantaccen suman gaban goshinta, juyowa yayi ahankali yakalleta, murya chan kasa yace "come closer" matsowa tayi kusadashi ahankali hartanajin saukan numfashin shi kan fuskanta, dauke idanunshi yayi dagakan fuskanta yadaura kan fararen kunnuwanta, ahankali yadauko abin guda daya yakai kunnenta yasamata aciki yana kallon yanda takeda gashi har akunne a kwance, murya chan kasa yace "the other ear" juyoda kanta tayi fuskanta yataba kafadanshi ajiyan zuciya tasauke, gently yasaka mata sanan yakoma sit dinshi yazauna hakan yasa itama yakoma tazauna, ahankali yace "I will help you, namiki alkawari baza'a tafi dake ko'ina ba inhar u do what I will tell u, idan kuma bakiyiba u are on the own, I have one condition koda wasa karki sake kafadama wani ko wata cewa nine na taimakeki understood" yay maganan yana kallonta dasauri ta gyadamai alamun eh, yace "duk ranan da kika fadima wani what happen ranan nida nataimakeki ni din still zansa amaidaki Kanon" dasauri ta girgizamai kai, kunna mota yayi yaja yace "zanuje yanzu, I will drop u outside zaki shiga direct wajensu zaki ki gaidasu, daganan I will be telling you kome zaki fada musu sanan kome sukace zan baki amsan abinda zaki fada musu, remember say exactly what I said kingane" dasauri tasake gyadamai gabanta na mugun faduwa dan gani take kaman wayau yake mata, har gaban gidan sanan yakashe motan yajuya yakalleta yace "gyara gyalen karsu hango abun nan, and don't show them any sign cewa magana ake miki a kunne" sake gyadamai kai yayi, ahankali yace "sauka kitafi" kallon fuskanshi tayi hawaye taji zasu zubomata murya chan kasa tace "Ya Asad dan Allah karka bari su tafidani kano dan Allah kataimaka min" yadade yana kallonta kafin ahankali yace "I will help u Du'a, now go, remember kome nafada miki repeat my words exactly" gyadamai kai tayi tabude kofan tasauka ahankali tabude gate tashiga gida bayan tabar jakanta a motan shi, saida yaga tashiga gida sanan yaja motar shi zuwa gidansu horn yayi aka budemai yay parking awajen parking lot dinsu sanan yay locking motar yana gyara zama ya kara wayanshi saitin bakinshi yanajin sautin karan bude kofan datayi dakuma hayaniya dake tashi afalon.

Binta kowa na falon yayi da kallo, ahankali Grandma da ranta ke abace tace "me kikayi anan" hawayen daya zubomata ta share tana gyara tsayuwanta tanajin maganan da Asad yayi sanan takalli Grandma tace "nazo wajen Abba da Mami ne inason magana dasu" kowa kallonta yake, barinma Dad dako kyafta ido ba yayi yana kara kallon halitta irin na ubangiji Baba baki Mama baka, y'a balarabiya, zama tayi ahankali agabansu ahankali tace "Abba ina kwana, Good morning Mami" anatse Babanta yace "Du'a ya kike? Maganan me zakimin bazaki iya bari anjima ba idan mugama magana da kakanki" girgizamai kai tayi ahankali sanan takalleshi tace "Abba Grandma batada lpy sosai, banson sabida ni wani abu yasameta" tsareta da ido Abba yayi sanan ahankali yace "okay to ina jinki menene" shiru tayi kusan 2min takasa magana hakan yasa Abba yace "speak up Du'a, yauzan koma kano" bakinta duk suka gani yafara rawa sosai kaman tana kokarin fighting abinda zata fadi, saikuma ta runtse idanu gam kaman daga sama duk sukaji maganan kaman saukan aradu. "Abba ni aure nakeso!" ba Abba kadaiba da Mami har ita Grandma saida tadan jinkirto daga kujera tana kallon Du'a jin maganan daya futo daga bakinta, tadauki kusan 1min idanunta a runtse sanan tabude idanunta ahankali tadago kanta takalli Abba dake kallonta asanyaye murya chan kasa hawaye na taruwa a fuskanta tace "Abba wlh ni aure nakeso, da inkoma Kano gwara nai aure" tai maganan ahankali dayasa Abba kasa koda motsin kirki hakama Mami dasu Ammi daduk ke falon, ahankali Mami tace "Du'a! Aure kikeso?" Tamata tambayan da mugun mamaki, gyadama Maman nata kai tayi ahankali tace "aure nakeso Mami" Abba da yaji ranshi yasosu sosai da kalamanta yace "Du'a kinsan mekike fadi kuwa? Aure kikeso, wazai aureki? wakikeso to ki aura eh"? Wanan karan shirun datayi yamafi nada sosai lips dinta kerawa takasa fadin maganan dake bakinta hakan yasa Abba da ranshi ke abace yadaka mata tsawa yace "I told you I don't have all day I still have to go back to kano yau, wakike so Du'a!" Yasaka mata tsawa dabatasan lokacin da maganan tafito ba. "Ya Asad!" Tai shiru tana wani irin sauke ijiyan zuciya kaman kirjinta zai fito sanan tace "Ya Asad nakeso Abba!" Wani irin kwalalo idanu Dad yayi, Ammi batasan lokacin dawani irin kayataccen murmushi ya kufce mata a labba ba, surprise look Grandma kemata danyau Du'a takasheta da mamaki, Abba dake kallonta yace "waye Ya Asad" ahankali tanuna Ammi tace "ga Babanshi da Maman shi anan" wanan karan saida Grandma itama tai murmushi bama tagama kai karshen murmushin ba tace "Abba dan Allah ka auramin Ya Asad ina sonshi sosai" wanan karan Abba jiyayi duka karfinshi yakare Du'a humiliated him to the core dabaisan lokacin daya dago kanshi ahankali yakalli Dad ba ahankali Akuma natse yace "waye Asad"? hada idanu Grandma da Ammi sukayi kafin Abba yamayi magana Ammi ta mike zumbur dasauri tace "I think har yanzu baitafi office ba, bari naje gida nakirashi kaganshi Baban Du'a" tafita daga falon dasauri batare data jira amsansu ba Abba da kowa na falon yazubama Du'a idanu.
Chapter 51 · 0% Book details