← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 109

Sashe 68

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ahankali yaturo kofan flat dinsu ya shiga, Ammin shi yagani zaune akan kujeran falonsu tareda Sharif dake zaune agabanta akasa yadaura kanshi akan cinyanta tanamai head massage suna hira, ganinshi yasa tai murmushi tanunamai kujeran dake facing nata tace "zoka zauna anan Son" maida kofan yayi yakaraso ciki yazauna ahankali, cire hannunta tayi dagakan Sharif din tadan bugi bayanshi alamun yatashi hakan yasa yatashi yazauna agefenta, dan gyaran murya Ammi tayi tana kallonshi, anatse tace "Asad bazan tsaya boye boye dakai ba znine mahaifiyar ka kai d'ana ne, the truth is banso kuma bazan taba bari aurenka da Du'a ya rabu ba" kallonta yake Asad ahankali hakan yasa gently tace "yes Asad nasan nashigi rayuwanka da yawa dankai aure baya gabanka, but son u are 33 yanzu going to 34, sai when zakai aure? Eh Asad, abu daya yakawoni nan side dinku, nazone musamman nagayamaka idan akwai yan gyare gyaren daza'ayi agidanka kafadamin nasa afarayi nan da 1 month that's sati hudu masu zuwa kenan za'a taron bikinku akai Du'a gidanka kaima katattara kabarmin gidana kaji" tunda take maganan yake kallonta harta gama yanayin jikinshi ko fuskanshi bai chanza ba, Asad is just somehow da saiyazo kagane mood nashi ne zaka gane, ganin yanda yayi yasa jikin Ammi yasoma sanyi but bataso takaraya, ahankali tamike tsaye taje gabanshi ta tsaya, saikuma yaja stool din gefen kujeran tazauna a gabanshi hannunshi guda biyun ta kalla sanan takalli fuskanshi ahankali tace "Asad nasan koda bakason Du'a kanajin tausayin yarinyar nan dan I see it in your eyes, bazaka iya taimako ba? Du'a yarinya ce mai bala'in hankali da natsuwa, barta dai da rashin wayo, tsoro da saurin kuka shima duk sabida yanda ta tasone nan gaba duk zata watsa dasu ta kile, Du'a yarinya ce da I assure you zakaji dadin zama da ita, d only problem da nasan Du'a nadashi is rashin iya girki which yanzu tafara koya, shima rashin iyawan sabida agidansu ko kasa ba'a bari ta sauko ne anyi banning nata daga shiga kitchen, Asad do this for me, for ur Ammi dakake so kaji" ganin yaki magana yasa ahankali Sharif yace "Asad" dagokai yayi yakalli Sharif saikuma ahankali yacire idanun daga kanshi yakalli Ammi ajiyan zuciya yasauke yace "Shikenan Ammi I will start with prep" tsabagen murna Ammi batasan lokacin datai kissing kumatunshi ba, Sharif yace "I will handle IV, dinner da....." yatsine fuska Asad yayi ahankali yakalli Ammi yace "Ammi tell him banason hayaniya please just low key taro zakuyi awatse I am not gonna be present in anything koda kun gayyaceni" Sharif zaiyi Magana Ammi tadaga mishi hannu alamun yayi shiru subishi ahaka, dasauri tace "shikenan Asad kome kakeso haka za'ayi, yanzu zan fara hada akwati, zan shiga Dubai nama gayama Baban ku inaso naje nai 3days nayi siye siyen kayan akwatin ta" tabe baki yayi yana taba aljihu trying yaciro wayanshi dan in ana surutu dabaya burgeshi waya kadai yake tabawa yaji dadi, jin bawayan yasa yadanja gajeren tsaki ahankali tuna yabarshi agidan, ba yanda ya iya haka yahakura yana jinsu suna shirye shirye har suka gama baikara kulasu ba.
Chapter 68 · 0% Book details