← Book details Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 109

Sashe 97

Kyawuna Jarabta Ta Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fita Grandma tayi daga dakin, itakuma takoma ta kwanta akan gado abinta ahankali tana murmushi, duk duniyan nan ayanzu babu wanda takeso yakuma yarda dashi irin Grandma, tadade tana tunani so yanzu Ya Asad na sonta daman da gaske? ita lokacin da Rahima tace haka bata yarda ba saida Grandma tafadi mata yau dinan sanan ta yarda, dan murmushi tayi ahankali tana tuna yanda yake kula da ita at the same time tana tuna yanda yake mata mugunta, wani kalan murmushi tayi ahankali tace "wlh saina rama" sanan takarayin murmushi tawani kwankwale madaran sanan ta kwanta abinta ahankali, tana kwance awajen saida taji ana gyaran mike din masallaci za'a kira sallan la'asar dasauri tamike tsaye, bakin hijab dinta dake kan dadduma tadauka tasaka sanan tasaka slippers tafito ahankali ta sauko kasa Grandma dake cin abinci tace "zakije" gyadama Grandma kai tayi, ahankali Grandma tace "to gyara tafiyan daurewa zakiyi duk zafin ohkay" gyadamata kai tayi tana gyara tafiyan zuwa normal tafiyanta amman ahankali bata iya sauri, murmushi kawai Grandma tayi tadauke kanta tace "ja'irin yaro zakaci gidanku ne Asad" tana fitowa daga Gate dinta takarasa gaban gate dinsu hannu tasa zata bude gate din aka rigata budewa Sharif ne tareda Asad zasu masallaci, ganin Sharif yasa ahankali tasaukar da kanta tace "Ya Sharif ina yini" murmushi yamata yace "Mrs Asad welcome" sanan yabi ta gefenta yawuce yay mosque batare daya kara waigowa ba, dago idanunta tayi ahankali tazubasu cikin na Asad dake tsaye batare daya fitowa yana kallonta, Sharif tadan juya takalla sanan takalleshi cikin wani irin classic voice takalleshi tace "kai bazaka masallacin bane why are u still standing" tamai maganan tana nunashi da hannu, wani irin binta da kallo yake this is the first ta tabamai magana ko tambaya haka without fear ko shakkan shi akan fuskanta, dan ijiyan zuciya yasauke jin antada salla sanan yataho ahankali yafito daga gidan daidai saitin ta ya tsaya faduwa gabanta yayi amman bata nunaba ta dake tana kallonshi, murya chan kasa yace "wait for me a flat dina" kallonshi tayi batare datace to ba, juyawa yayi yawuce saida ta bari yay kaman taku biyu sanan ahankali tace "Asad" juyowa yayi dasauri, ahankali da hannunta da bakin lallen yasoma goge wa tamai alamu dayazo, like kasa boye mamakin shi yayi hakan ma yasa baisan lokacin dayakai gabanta ba, dan yatsine fuska tayi tace "kabani wayanka please nagaji da rashin waya I am bored, I don't even know why kawai fasamin wayana, mutum sai fitinannen kishi" wanan karan saida Asad yadan zaro idanunshi like is she Du'a daya sanni ko junnu sun shigeta ba, sometimes idan abu yay hitting naka unexpectedly bama kasanin what exactly zakayi, situation din da Asad yasami kanshi kenan, kawai yay mutuwan tsaye yana kallonta, hannunta tamika mai murya chan kasa tace "bani wayan, idan kasaimin nawa saina maidama back Husband"! wlh ji kawai yayi yasa hannu a aljihun wandonshi zai ciro wayan tsabagen rudewa yama manta wayan na aljihun gaban riganshi da hannunta ta nunamai aljihun gaban riganshi tace "ga wayanka nan ina gani" zaro hannun yayi daga aljihu yasa agaban rigan yaciro yamika mata karba tayi batare datamace thank u ba tajuya kaman ta amshi nata tashiga gidan tamaida gate din tarufe da karfi, karan dayayi yasa yay firgigit daga dena kallon gate din yawuce mosque dasauri.

Tana shiga gidan wani irin tsalle tayi tana tana bubbuga kirjinta dake neman fitowa sanan tahau rawa so Grandma was right Asad na sonta, sabida ya ganta batada wayau shine yake mata abinda yaga dama gashinan yanzu bai mata komi ba, wani irin murmushi tayi tana kallon wayanshi dake hannunta sanan tajuya tana tafiya ahankali ta tafi gidan, sallama tayi tashiga falon, Aneesah da Mariya ne kadai afalon suna jera kula a dinning, Mariya na ganinta ta taho da gudu ta rungume ta tace "oyoyo Du'a" murmushi tayi, itakuma Aneesah tana inda take ahankali tace "ina yini Anty Du'a" daga Mariya har Du'a kallonta suke saikuma sukai murmushi, Du'a tace "sannu da aiki Aneesah" sanan takalli Mariya tace "bari naje na gaida Dad da Ammi" tawuce sama ahankali takebin stairs din tana runtse idanu sanan tawuce sama, dakin Ammi tafara shiga bata ciki hakan yasa tai dakin Dad, sallama tafara yi dasauri Ammi ta taso bude kofa tayi tana murmushi kafin Du'a tai magana ma Ammi ta rungumeta anatse tace "maraba da my daughter" sanan tasaketa ahankali tai cupping face dinta ta manna mata kiss agoshi sanan tasaketa tana kallonta, duka duka yaune rana na hudu da aurensu amman tai wani unbelievable kyau, ahankali Du'a tace "Mum ina yini ya jiki" murmushi Ammi tayi tace "ni naji sauki ga mara lafiya nan baban ku muje ki gaidashi" shigowa sukayi ciki har gaban gadon Dad sanan ahankali tadago kai takalki Dad dake kallonta kaman zai hadiye ko kadan baiso tasako hijab ba tace "Dad ina yini ya jiki" ahankali yace "dasauki Du'a, ya naki jikin" ahankali tace "dasauki" Ammi tace "ga fuskan kinaan bai gama sabewa ba, koma gida ki kwanta please, ke ciwo babanku ciwo ina zansa kaina, at least ke kihuta naji da wanan" dan murmushi Dad yayi yace "kinga Asad ne yanzun nan suka tafi masallaci" Girgizamai kai tayi, murmushi yayi dadi har ranshi yace "to to shikenan wuce kitafi abinki ki huta agida kafin mu rikeki muhanaki komawa wajen Grandma dinki" murmushi tayi tajuya ahankali ahankali tace "Mum bye bye" Ammi kaman ta cinye ta kallon yar karaman baby takema Du'a ahankali tace "bye bye baby na" fita Du'a tayi daga dakin ta sauka dasauri, bye tama Mariya dakeson riketa sanan tafice daga gidan, dasauri sauri harda dan gudu ta shiga gidansu dan batason anything dazaisa yafito ya ganta.

Sharif na kallonshi ana idarwa yafice, dan murmushi kawai yayi danshi tuni ya karanci yanda Asad ke son Du'a amman wani irin cool love yakema yarinyar nan mai basira kadai zai iya gane cewa Asad na mutuwan son Du'a, yana shiga gidan flat dinsu yayi yay sama da dan sauri ganin bata taredasu Mariya a falo, ahankali yay sallama yashiga dakin Dad, yanadan kalle kalle, ganinshi yasa Ammi tace "yauwa Asad kadawo daga masallaci ga babanku zaiyi fitsari zaiyi alwala kuma yay salla, ni zanje dakina nai salla" gyadamata kai yayi yana zuwa wajen gadon itakuma Ammi tai hanyar fita hartakai kofa tajuyo tace "namanta ban fadi maka ba yanzun nan Du'a tabar nan, kumafa baku dade da fitaba tashigo na tambayeta kota ga ka tace a'a, wlh tazo ta gaidamu" gyadama Ammi kai kawai yayi batare dayace komiba yana dago Dad, komi yama Dad duk Dad na luradashi ko kadan baiji dadi dabai ganta ba, saida yamai alwala sanan yatashi zai fita dasauri Dad yarikemai hannu yace "stay with me son, idan ina ganinka ina rage tunani" dan gyadamai kai kawai yayi badan yasoba yakoma yazauna sai kallon kofa yake kaman yabude tashigo, yana zaune da Dad ko motsi yayi sai Dad yace karyaje ko'ina har aka kira magrib, kiri kiri tsohon nan yahau kuka yana rike Asad wai dare yayi yanzu zai fara tunani, adaki Asad yay magrib yay isha'i , sanan yabashi abinci abaki yaci yay knack, Ammi ma ganin yanda he's all over Asad yasa taje ta kwanta, sai wuraren 1 Asad yasamu yay bacci sanan ahankali yatashi yacire hannunshi dagakan nashi yafito.

8️⃣1️⃣

Dakin Ammi yashiga tana zaune kan dadduma yasa nafila take wayanta dake kan gado kawai yadauka sanan yawuce yafita, dakinshi yaje, baima tsaya yin wankaba yay dialing number shi, Du'a na kwance kan gadonta tana game da wayan nashi hankali kwance taga kira da wayan Ammi na shigowa amman bata dauka ba, katsewa wayan yayi yasake kira nan ma kin dagawa tayi gashi yadage sai kira yake gashi bayan bata silent irin dole saiya tadata dinan, a 5th call din tadauka, murya chan kasa tace "Hello" murya chan kasa yace "I told you kijirani a flat dina baisa baki hakaba" murya chan kasa tace "hakanan" shiru yayi shuuuu yakasa magana, murmushi tadanyi sanan murya chan kasa tace "lafiya katadani, I was having a very sweet dream wlh, what's d matter" daurewa yayi cikin wanan muryan isan nashi yace "I want to see you" ahankali tace "right now, why? what happen Asad" kai hannunta tayi tadaura kan bakinta ita kanta takirashi Asad ba Ya akai wani banbaran takeji, wanan karan yayi shiru yafi na 10min, dazu he thought kunnenshi ne yajimai takirashi Asad gatsai, gashinan yanzu yakara ji, jin shiru yayi yawa yasa tace cikin muryan nan nakaman dole aka sata tai magana "Hello, are you there? nace maisa kakeson ganinta this night" ahankali murya chan ciki yace "I want you" kaman bata gane maiyake nufiba tace "me kuma" murya chan ciki yace "ina bukatan hakki nane, I badly needs sex right now" ahankali tace "oops sex is unavailable, Du'a is temporary unavailable, try next time" kawai ta katse wayan dip, dasauri Asad yakalli wayan kasa rike maganan yayi yace "what's wrong with her" sake dialing number yayi amman harya katse bata daukaba, 10 calls yabata bata fadawa gadon yayi ranshi ya bala'in baci, filow yajawo ahankali tareda lumshe idanu yana kokarin sa kanshi bacci but ina yakasa, jiyake baisami abinda zai sashi bacci ba, ganin sha'awa na neman kasheshi tashi yayi yafice, fita daga gidansu yayi bako kunya sake knocking yayi security gidan Grandma yabude mai kofa yashiga ciki yay kofan falonsu murdawa yayi yaji akulle, jiyayi ranshi yay masifan baci wani abu ya tsayamai awuya juyawa yayi dasauri yafice daga gidan yakoma gidansu yakirata yafi sau goma bata dagaba, mutuwa ne kawai baiyiba, baitaba sanin this is how a man feels bayan yayi aure ba saiyau jiyayi kwana shi kadai is just impossible, wani irin yunwanta yakeji kaman maye, jiyayi gadon ma kamshinta yake, haukane kawai baiyiba idanunshi sukai jajir da kyar bacci yadauke shi wajajen 5.
Chapter 97 · 0% Book details