Sashe 9
Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yake jin sautin muryar yarinyar natashi Samira kuwa cigaba da magana tayi Kuma duk acikin mutanan sarki barkodi babu Wanda ya iya kokarin dakatar d ita ganin yadda tayiwa yankan baya wanda duk cikinsu shine ogansu daga shi sai Kuma sarkin muna bukatar zamu sha ruwa ina buga kofa kawai kabude kamareni watau Kai bakasan darajar mace bah koh toh wallahi idan ka kara marina sai na maka abinda bazaka taba mantawa bah Kuma bazaka taba tunkarar wata mace bah d niyyar cutar da ita kubani ruwa wata murya taji abayanta ita kanta muryar idan kajita sai kaji gabanka yafadi duk dacewa ta tsorata Amman sai tadake ta juya wani katon mutum tagani idanuwansa duk sun firfito xubinsa kamar wani aljanin Dan ita tayi tunanin mah aljani neh rike yake d zabgegiyar wukarsa ahannunsa ❤️❤️KADDARATA😔✍🏼 Story and written by Nanah m sha'aban✍🏼❤️ Page 38-39 Sarki barkodi yakarewa samira kallo kasancewar lokacin gari ya waye karfe 7:00 na safe kyakkyawace duk dacewar tana sanye d hijabi amman daga ganin yarinyar zakasan bayan kyan fuska da take dashi harda kyan diri niyyar dayake dashi nacewa yana xuwa zai datsewa yarinyar kai saboda ta tasheshi daga bacci lokacin tashinsa baiyi bah tuni ya ajiyesa gefe dan tunda ake kawo masa mata bai taba ganin wacce take d kyan wannan yarinyar bah ita kuwa samira taji tsoronsa matuka amman d ta tuna alkawarin d tayiwa kanta cewar bazata kara jin tsoron wani da namiji bah KO d ace tana jin tsoronsa zata barshi iya kacin zuciyarta bazata taba barin yagane tana jin tsoronsa bah dan a chan baya taji tsoron yaya fahid tamkar wani mala'ika amman yanxu babu wanda ya isa taji tsoronsa dan ta fuskanci maxa basu d tausayi basu san darajar mace bah ko kadan kallonsa take ido cikin ido abinda babu wata yarinya data taba tsayawa a gabansa mah bare tayi masa kallo ido cikin ido muna bukatar ruwa zamu sha tafada tana kara kare masa kallo su kuwa mutanansa yana fitowa duk suka yi masa sujjada da kuma wasu matan d suke aikin daukar buhunhuna Wanda bata san komai nene acikinsa bah sanye suke da wasu kaya wanda zata iya cewa dasu gwara babu yayi mamakin yadda yarinyar bataji tsoronsa bah kuma batayi sujjada kamar yadda bayinsa sukayi masa bah yankan baya sarki barkodi yayi kiransa d kakkausar murya zuwa yayi ya durkusa masa har kasa dan shi yankan baya a tunaninsa sarkin zai ce aje arataye yarinyar bama shi kadai bah har sauran bayin amman sai sukaji akasin haka kaje kadebo mata ruwa wanda zai isheta kabata cikin saurin yankan baya yatashi ya debowa samira ruwa awani dan karamin kofi dan dokar gidan ce ko su mutanan sarkin basa shan ruwan dayafi kofin bayi kuwa sai su wuni basu sha ruwa bah idan zaa basu rabin kofin zaa bazasu sai kuma gobe kamar lokacin zaa kara basu kallo daya tayiwa kofin tace baa wannan kofin bah dan bani kadai zan sha bah kuma koni zan sha wannan yayi min kadan tsawa yankan baya yadaka mata yana shirin yin magana sarki barkodi ya dakatar dashi da cewa yankan baya yakira sunansa cikin daka masa tsawa samira taji tsoro matuka amman sai ta dake shikuwa yankan baya mamaki ya shiga yau sarki barkodi ne yake daka masa tsawa sabida wata yarinya kodan yaganta kyakkyawace jiyayi yana cewa kaje kadebo mata ruwa iya yanda take so idan bai isheta bama ka karo mata yana gama fadar haka yayi hanyar dakinsa sama neh dakinsa kuma kusan matattakala guda ashirinne amman kamar aljani haka ya haura dakinsa xuciyarsa cike d farin cikin jibi kamar haka yana tare d wannan yarinyar bama ita kadai bah har d sauran wadanda aka kamosu tare d ita samira kuwa tsaki tayi sannan takalli yankan baya tace kadebo min ruwa koh bakaji abinda wanchan shashashan yace maka bah xuwa yayi ya debo mata ruwa cikin guga tashiga takai musu kowannansu sai d ya isheshi sannan tamayar da gugar fahid kuwa kusan kullum sai yaje gidan mommy idan ta tambayeshi ya babyna sai yace tana nan lpy yaya umar yadawo daga maiduguri wata rana yaya fahid din yaxo gidan duk suna tare abbane kadai bayanan yayi tafi kasar Uganda ana ta hira sai daddy yace kai gsky nadade rabon d naga babyn mommy Yadai zanje yaganta yaya umar mah yace wallahi nima zanje naganta kwana biyu idan nakirata baba samu mommy tace ay fahid yace wayarta ta lalace shiyasa amman nima ina kewar babynah fahid kuwa da gabansa sai faduwa yake yace eh wllh wayarta ta lalace kuma yau bata gida taje gidan hamxa gurin aisha ok gsky gwanda ta dinga xuwa tunda kuna kusa mommy tafada tadan jinjina kai yana dan murmushin yake amman yakamata yau kahadani d ita gsky idan tadawo tohm mommy sai kuma yamike yana fadar mommy bari intafi tohm shikenan yafita daga gidan watau yafitar d ita daga rayuwarsa bai huta bah tana kokarin kara jawo masa matsala duk da bata nan yanxu idan mommy tagano basa tare da samira yazanyi yasan iya fushi zatayi matukar fushi amman yasan daga karshe dole tahakura tunda shine danta shine dolenta ita kuma babu abinda yahadasu da ita ko iyayenta basu sani bah dan haka bai wani takurawa kansa akan tunanin bah yawatsar dashi ya shiga yin harkokinsa shi kuwa yaya umar bai san meyasa bah yaji xuciyarsa taki yarda da maganar da yayannasa yayi bah wai samira ce zaa ce wayarta ta lalace meyasa lokaci guda yatashi yatafi yasan lallai akwai abinda yaya fahid din yake boyewa kodai yakashe samira neh dasauri yadauki makullin motarsa sannan takalli daddy yace xo karaka ni mommy ta tambayeshi ina zai je yace mommy zanje gidan ahmad neh ok tohm sai kun dawo daddy yatashi yabi bayan yaya umar din har sunyi nisa daddy yaga umar yahuce hanyar da zata kaisu gidan ahmad abokin umar din yace yaya ay mun huce hanyar gidan yaya ahmad din eh ba chan zamuje bah gidan yaya hamxa xamuje daddy ina tunanin akwai abinda yaya fahid yake boye mana shuru yayi sannan kuma ya nisa yace kana tunanin babyn mommy bata gidan aunty aisha kawai yaya fahid yafada neh eh daddy haka nake tunani kuma akwai dalilin dayasa nake tunanin haka suna isa gidan sukayi packing din motar suka fito yaro suka aika sukace yaje yayi musu sallama d mai gidan yace su umar d daddyne kannan fahid koda yaron yaje aisha tace bayanan amman yace su shigo shiga sukayi ita kadai suka gani dukkansu sai d gabansu ya fadi daddy yayi saurin kallon aisha yace aunty aisha ina samira samira kuma tafada cike d mamaki ay samira tun ranar d muka kaita gidanta rabon d kaganta daddy ya zube kasa yana sakin kuka shikenan yanxu maganarka yaya umar ta tabbata inajin yaya fahid ya kashe samira shima umar xubewa yayi akan kujera yana kuka aisha duk tabi d daga hankalinta tana cewa ku fahimtar dani bangane abinda kuke cewa bah nan umar ha zaiyane mata duk abinda yaya fahid din yace yau dakuma abinda yake cewa idan an tambayeshi Ina samira yadaura da cewa kila aunty aisha yakashe mana samira idan shi ya tsaneta ay mu muna santa yakarashe. maganar cikin kuka itama din kuka take tadauko wayarta tashiga kiran mijinta dan tasanar dashi abinda kefaruwa ❤️❤️KADDARATA😔✍🏼 Story and written by Nanah m shaaban✍🏼❤️ Page 40-41 Aisha tana gama fadawa mijinnata abinda su umar suka fada mata baa fi mint 10 bah sai gashi ya shigo gidan dayake bah wani nisa yayi bah daman hakuri yabasu umar shima hankalinsa yatashi yanxu kiyayyar da fahid yake mata takai ga haka toh ina fahid yakai samira kodai kamar yadda suke fadar kasheta yayi innalillahi wainna ilaihi raju'un yashiga maimaitawa haka su umar suka tashi har bakin mota hamxa yaraka su yana rokarsu karsu gayawa kowa wannan maganar har sai sunyi magana da fahid din kawai jinsa suke amman daddy ya kuduri niyyar a yau dinnan sai yafadawa mommy tayama yaya hamxa zai ce wai kar a bari kowa yasani chabb ay wannan abune mara yiyuwa shima umar abinda ke xuciyarsa kenan motar suka shiga dukkansu suna isa gidan daddy ya bar umar acikin motar yanufi falo ya kiran mommy fuskarsa duk hawaye sharkaf mommy tafito daga dakinta a dai dai lokacin kuma umar yashigo falon shima anan take daddy yashiga zai yane mata komai yadora da cewa mommy yaya fahid ya rabamu d babynki shikenan yakasheta hankalinsa ya kwanta mommy kuwa yanke jiki tayi tafadi dasauri dukkansu suka nufota bata numfashi kuka suka saka dan sun san irin shakuwar dake tsakaninmu mommy da samirar abisitin cikin gidan suka nufa d ita zaune suke acikin dakin wata baiwar sarki barkodi ta kawo musu abinci har ta tashi samira tayi saurin kiranta baiwar Allah dan allah tsaya juyowa tayi batare da tace komai bah tashi samirar tayi takarasa har inda take tace tambayarki zanyi ina fatan zan samu dukkan amsoshin tambayata eh insha Allah duk dacewar nasan tambayar taki bazata huce akan gidannan bah tohm bari in baki dan takaitaccen labarin gidannan..... Gidannan dai duk wanda ya shigo shi karma yayi tunanin zai fita a raye dan sai sarki barkodi yagama amfanin dazaiyi dakai sannan zai saka ayi bikin mutuwarkun dan yasan baku wani mamora nayi mamaki kwarai dagaske danaga kin tashi kina ta ihu wanda naga koda sarki yaxo bai yimiki komai bah kinsan idan aka tashi sarki barkodi daga bacci koda kuwa daya daga cikin mutanansa neh kawai katabbata lokacin mutuwarka yayi yanxu ku babu abinda zakuyi masa nadaga aikin wahala dan kune amarensa na jibi wanda kuma a jibi zaayi bikin mutuwarsu lantana sai kuma tafara kuka duk da cewa samira ta kidima da jin labarin gidan amman dataga tana kuka sai zuciyarta takarye wacece lantanar daya daga cikin yammatan ta tambaya yar uwata ceh tare aka kawomu kenan yanxu kina nifin idan ya kusancemu yaga bamu d mamora sai yasaka aka kashemu kuma yasaka akawo masa wasu matan takara tambayarta samira tajuyo ta kallesu tana cewa yan uwana yakamata muhada karfi da karfe domin mukubar dakanmu da kuma su lantanar koh ta halin yaya dole Mubarak gidannan hakane mun goyi bayanki Dari bisa Dari dukkansu suka fada baiwar sarkin ta kallesu tace taya kuke