← Book details Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 38

Sashe 5

Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

❤️❤️KADDARATA😔✍🏼 Story and written by Nanah m shaaban❤️✍🏼 Page 16-17 Kwanan samira biyu bata san wanda yake kanta bah shi kuwa umar tunda yakawota basamu yaje ya dubo mahaifiyar abokinnasa bah sai kiransa yayi yafada masa abinda yafaru yace bakomai kuma zaixo asibitin insha Allah kira mommynsa yayi itama yafada mata abinda yafaru yace harsai ta farfado yamaida ta gidansu sannan zai dawo gida mommy tace bakomai dan allah idan ta tashi kayi mata sannu kaji kuma ka kula d ita sosai yace toh mommy a kwana na uku ne samira tafarfado lokacin abokin umar, usman yaxo nan dukkansu sukayi hamdala umar ya matso yana mata sannu kuma yana tambayarta koh akwai inda yake mata ciwo ta girgixa kai alamar Aa tohm ina ne gidanku dan naje nasanar d iyayanki abinda ya faru nasan yanxu hankalinsu atashe yake Dan Allah karka mayardani tafada tare da fashewa d kuka umar yakalli abokinsa usman cike d mamaki shima usman din matsowa yayi dan shi baa kauyansu samira yake bah yana kauyan kusa dashi sune shiyasa bai santa bah haba kanwata meyasa kike kuka ko bakya so kikoma gida dasauri tace eh bana so fada tana kallo usman wanda shi yayi mata tambayar sannan takomar d dubanta kan umar ta saka gwiwoyinta akan godon asibitin tarike hannuwansa dan allah kawu katafi dani gidanka allah ko menene zan maka na iya wanki kuma harda shara mah duk zanyi maka karka komar dani gurin baba allah kasheni zatayi karki damu kinji kidaina kukan haka ina mahaifiyarki take cikin sauri tace innata ta mutu babbana mah ya mutu a gurin baba haladu nake anan tabasa labarin irin wahalar d baba take bata kuma ta dora da cewa yanxu idan nakoma kasheni zatayi zata yankani umar mutum ne mai tsananin tausayi kuma ya tsani yaga ana wulakanta yara kanana dan haka tuni yafara xubar d hawaye kuma yayi alkawarin bazai taba mayar d samira bah zatafi da ita dan yasan mommynsu zata karbeta hannu bibbiyu shima kansa usman numfasawa yayi tare d dafa kafar umar yace dan allah abokina idan d hali katafi d yarinyar nan gidanku karka ce zaka mayar d ita ay usman ko baka rokeni bah wallahi bazan taba narinta anan garin bah zan tafi d ita dasauri samira tace nagode kawu Allah yasaka a aljannatul firdausi rugumeta yayi tare d cewa amin a ranar aka basu sallama suka dauki hangar abuja bayan sunyi sallama d usman tun a asibitin yakirawo mommy yace zasu taho d yarinyar d yakade yabata labarin d samirar tabashi kan irin wahalar d take sha a hannun facalar babarta ko da suka isa abuja hajiya rahma ta nuna farin cikinta dan bata d yarinyah mace kuma tana tsananin son yara mata ta dauki samira tamkar yarta ta tambayeta yasunanta tace sunana samira bukar tohm daga yau ki daukeni tamkar innarki kinji tace toh tasata a makaranta kudi dake jihar abuja fahid kuwa tun daga ranar dayayi ido biyu d samira yaji ya tsaneta daki guda aka warewa samira sai d bikin ta yaxo mommy taware bangare guda tace na samirane dan taji dedi shiryawa biki mommy tasan irin tsantsar tsanar d fahid yakewa samira amman ita a tunaninta da zarar ya aureta zai ajiye kiyayyar d yake mata a gefe Wannan shine asalin fahid da samira ❤️❤️KADDARATA😔✍🏼 Story and written by nanah m sha'aban❤️✍ Page 18-19 Kamar an tsikareta ta tashi dasauri kyawawan idanuwanta ne suka sauka akan agogon dake jikin bangon karfe 7:00 dai dai na safe adai dai lokacin kuma bugun zuciyarta ya tsananta bugu tasan rayuwar aure d yaya fahid tamkar rayuwar cikin kabari ce kai rayuwar kabari mah tafita dadi dan acikin kabari babu me takura maka sai dai idan kayi abinda bai dace bah Allah ya kiyayemu da sharrin duhun kabari Amin jitayi ana knocking din dakin dasauri tagoge hawayen idanuwanta tare d bada izinin shigowa aunty binta ceh tayi sallama ta shigo zaunawa tayi kusa da ita tana kallonta cike d tausayawa tace samira nasan irin damuwar dakike ciki amman kiyi hakuri insha Allahu wata rana sai labari fahid nasan yayi matukar tsanarki tsanar d bai taba yiwa wani mutum bah amman ina da tabbacin cewa wallahi zakice nafada miki fahid zai soki son da bai taba yiwa wata 'ya mace bah zaiyi miki son da bayan aunty rahma d yaya wallahi kece ta uku da zai so acikin rayuwarsa kisani cewa idan kiyayyah tayi tsanani toh tana rikidewa tazama soyayyah matsanani kidaina kuka kinji ita dai samira kawai jin aunty binta take taya zaay acewa yaya fahid din daya tsaneta ace shine wai wata rana zai so ta bata tunanin wannan ranar zataxo aunty binta kanwar Abba ce uwarsu daya ubansu daya macece mai faran faran da mutane jininsu yaxo daya d samira aunty binta bata bar gurin samira bah har sai d ta tabbatar ta tayi wanka taxo ta shiyata acikin las pink colour tayi mata kwalliya tayi kyau sosai sannan tafita tabarta zaunawa samira tayi akan kujerar dressing mirror tana kallon kanta a madubi zuciyarta fal da tunanin makomar rayuwarta yanxu dai ya tabbata babu makawa sai anyi aurenta d yaya fahid ko minti biyar aunty binta batayi bah yusuf ya shigo dakin da sallama ya gaisheta ta amsa cikin sakin fuska yusuf yarone kwata kwata shekararsa goma amman yana da tsananin hankali d nutsuwa gashi d girmama nagaba dashi aunty samira wai fauziyyah abdulaziz yar makarantarku taxo inji mommy cikin fara'a tace tohm yaron kirki kace ina xuwa yafita yana murmushi fauziyyah kawar samira ceh sunyi makaranta daya inda sukayi karatunsu akan orthopedic fita tayi cikin sauri tana ganin fauziyyah suka rungume juna dakinta suka shiga itama lallashinta tashiga yin d kwantar mata d hankali tohm shikenan fauziyyah nagode karfe 11 dai dai aka daura auran samira bukar dakuma fahid ibrahim bukar akan sadaki 200k nan pha kukan samira yadawo sabo dataji an daura aureta d yaya fahid shikuwa yaya umar tausayin samira yahana shi sakewa da mutane duk dacewa ga yan uwansu na kusa dana nesa duk sunxo fitowa yayi daga cikin dakin bakin dasuke ciki yana neman wanda zai kirawo masa samira kausar yar gidan aunty binta yagani yace taje takirawo mata samira a babban falo yazauna inda yake kusa d bangaren samira tana fitowa ta ganshi akasa tanemi guri ta xauna yace aa ta tashi taxauna akan kujera zaunawa tayi ya kalleta yaga duk idanuwanta sun kumbura nan yashiga yimata nasiha dakuma rokonta da tayi hakuri da tayi hakuri d dukkan abinda yaya fahid din zaiyi mata yadora dacewa nasanki da hakuri tohm kikara akan wanda nasanki dashi kinji kanwata tohm kawu nagode haka ta tashi takoma bangarennata Babban falone wanda aka wadatashi da kayan more rayuwa zaune yake akan tafka tafkan kujerun dake zagaye da falon ransa duk abace yake tunda yaje yadawo daga daurin auren d abbane yasa shi dole sai dayaje kafafuwansa yadora akan center table yana kadasu ahankali fahid neh wanda ya tsunduma d tunanin irin wahalar da zai bawa samira lokaci daya kuma yatashi sai d yacire malum malum din daurin auren sannan yatashi yafita daga cikin gidan gaba daya anyi biki anci ansha samira tasaka suturu masu tsada duk acikin gidan akayi bikin wajen karfe 7:00 nadare motocin daukar Amarya sukayi fakin acikin aharabar gidan haka aka saka samira mommy na kuka itama samirar kukan take tana kankame d mommy dakyar aka iya banbareta daga jikin mommy suka jo motocin suka nufi gidan Amarya samira ❤️❤️KADDARATA😔✍🏼 Story and written by nanah m sha'aban❤️✍🏼 Page 20-21 Bayan ankaita gidanta dake nan abuja suna da dan nisa da gidan mommy shima katafaran gidane sosai falo biyu neh sai kuma bedroom shima biyu sai kitchen sai toilet din baki dan akowa wane bedroom akwai toilet acikinsa sai kuma wani daki daban wanda yake dauke da katon freezer an zuba kayan ciye ciye acikinsa a daya daga cikin bedroom din suka sakata bayan aunty binta takara yimata nasiha sannan aka watse aka barta ita kadai zuciyarta cike da fargaba yau gata ga yaya fahid daman agaban su mommy yana ci mata mutunci yana wulakantata dan mah mommy idan yafara tana dakatar dashi cikin fushi tohm yanxu babu mai dakatar dashi duk abinda zai mata babu wanda zai ceceta sai ubangijinmu Allah zuciyarta tafara raya mata data kulle dakin da makulli dasauri ta tashi tasakawa dakin key........... Tunda yafito daga cikin gidan yahau kan titi yafara wani mahaukacin tuki, tuki yake xuciyarsa kamar tafaso kirjinsa tafito saboda bakin ciki a wani gurin sayar da wuka yayi packing yafito wata sharbebiyar wuka yadauka gayawa jini nahuce sannan ya fiddo kudin dabesan nawa baneh ya dankawa mai sayar da wukar yafada cikin mota yafara tuki ahankali maganar mommy tafara yimasa yawo akunne Wallahi fahid idan kasake kasaki samira zaka gamu da fushina zan cireka daga cikin 'ya'yana inda Abba dake gefeta yadaura da cewa samira tamkar 'yarmu take ina maka da nasiha da karka cutar da ita kasani idan har ka cutar da ita kana ganin bama nan toh kasani cewa Allah yana ganinka kuma bazai taba barinka bah Allah yabaku zaman lpy wani tsaki yasaki xuciyarsa natun xirashi dayaje ya kashe samira kawai kowa yahuta yana isa gidan kai tsaye ya nufi hanyar dayake tunanin anan aka saka samira hannunsa dauke d wukar ya tura kofar dakarfi amman yajita a rufe watau kulle dakin tayi yafada a xuciyarsa nan pha yashiga bugun kofar yana fadin tabude dakin dayaga taki ya nufi hanyar bedroom dinsa samira kuwa dataji alamar takun tafiyarsa taleka ta window ganin sharbebiyar wukar dake hannunsa yasa tayi saurin jaaa dabaya innalillahi wa inna ilaihi raju'un yaya fahid kasheni zakayi Ashe kiyayyar dakake min takai ga har zaka iya kasheni tabbas dolene nasan inda dare yayi min kwance take akan mommynta tana kuka kamar ranta zai fita saudat ceh takalli mahaifiyarta tace mommy yanxu shikenan yaya fahid bazai taba zama mallakina bahh haba daughter karkice haka kinji dolene rahma tayarda da aurenki da fahid kotana so kobata so nayi miki alkawari kekadai ceh zaki zama matar fahid kinsan dai irin kiyayyar d fahid yayiwa wannan shashashar yarinyar nan mommy taya kike ganin mommyn yaya fahid zata yarda da aurena da fahid kinaji dai abinda tace mana dakikaje kika fada mata kina son a hada
Chapter 5 · 0% Book details