← Book details Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 38

Sashe 35

Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

💔💧 KADDARATA😔✍🏾
Story and written by Naanah M Sha'aban✍🏾💔
Page 160-161
Mommy ta dafa fadeelarh tare da cewa kai kuwa yarta mai yasa kike fadar irin wadannan maganganun akan mahaifinki........takalli mommy kawai tare da girgixa kai aunty shi yaja min duk irin halin dana tsinci kaina ynx saboda son xuciyarsa da kuma kudi bai damu da irin halin da zan tsinci kaina bah burinshi dai kawai kudi...kudi..kudi yafi yarsa kudi yafini mahaimanci a gurinsa takarasa maganar tana kuka😭😭😭
Yaya umar yace duk da haka fadeelarh bai kamata kifadi wannan mugayen kalaman bah ae hannunka baya taba rubewa kayanke kayar......ta dago dasauri tare da yin murmushi takaici hawaye shabeshabe a fuskanta tace Yaya waya gaya maka sai dai idan bai damaika bah Amman lokacin da zagaje asibiti ae yanke maka karabu da kaya bazaka sani bah....Kuma wlh wlh ni nayanke nayar Kuma har abada bazan kara kiranshi da mahaifina bah dan na tsaneshi duk duniya mutane biyun nan nayi matukar tsanarsu usman da kuma Ayuba😒kallonta yayi sosai sannan yace fadeelarh koh zan iya jin labarinki domin har nakagu inji mai mahaifinki yayi miki haka kikayi masa wannan tsanar..........hawaye na zuba daga idonta tace labarinah babu abinda zakaji a cikinsa sai bakin ciki da takaici game da son xuciya.....tafara da cewar da farko dai sunana fadeelarh Ayuba garba muna zaune da kishiyar mahaifiyata da Kuma mahaifina a garin sokoto mahaifiyata ta mutu ranar da tahaifeni a hannun Addah mariii na taso watau kishiyar mamah tunda na taso Addah Bata taba nuna min irin bakin hali bah koh ta nuna tafison yaranta akaina hasalima tafisona akan yaranta Dan komai tasamu ni take Fara bawa sannan tabawa yaranta ragowa....shi kuwa mahaifina yakasance mutum neh Mai tsananin son abin duniya bashi da wani buri irin yaga yayi kudi koh ta wacce hanyaceh.....ni kadai ceh yarsa mace Dan yaran adda duk maza neh sani,bukar da kuma auta khabir Dan haka ya dauki dogon buri ya daura akaina bama ni kadai bah harsu khabir mah a cewarsa ae mune kadararsa da mu zai nemi kudinsa a lokacin nazata kawai wasa neh irin nasa dan nasha jiii ana cewa duk mahaifi bazai so ace yasa yaransa cikin wani hali bah dan har nake bawa kawayena labari sai muyi ta dariya suce kawai fada yake taya zamu zama kadararsa sai kace wasu gidaje....haka dai zamuyi tayi hirar muna dariya dan har suke tsokanata suce kadarar babanta duk sanda suka fadi haka sai dai nayi dariya....... Ranar da bazan taba mantawa bah..ranar danaje na duba neco dinta Naga na ci 6 credit na shigo gida da gudu Ina murna na fada jikin adda nake fada mata na duba exam dina na cinye duka....itama taji matukar dadi burinki ya kusan cika kenan nazama cikakkiyar doctor sai samin aiki dariya nayi nace adda ae sai naje school of health sannan zan sami gurbin zama cikakkiyar doctor tace Awww ynx bayan wannan makarantar akwai wacce zaki kara yiii kenan nace mata ehmn ae dasaura.......shigowar babah neh yasa muka katse hirar nayi masa sannu da zuwa na tashi zan shiga daki yakira sunana fadeelarhtou dawo ki xauna ae yau dawowar taki ceh nayi mamaki sosai dajin abinda yace dan haka nadawo nazauna ina Jin naji Mai zai ceh.......
Anan zan dakata sai Kuma gobe idan Allah yakaimu👏🥰💔
Nice taku a kullum a koda yaushe Naanah Sha'aban💔✍🏾

💚💧 KADDARATA😔✍🏾
Story and written by Naanah M Sha'aban✍🏾😁💔
Page 162-163
Baba ya kalleni sosai dan gaba daya na tattara nutsuwata da hankalina wajenshi domin jin mai yafaru dan nasan babah baya dawowa gida da ranar sai dai idan akwai abinda ya manta ko Kuma muhimmiyar maganar da zai fadawa Addah Amman yau da dawo Kuma yace saboda nii shiyasa na kagu inji mai zai fada.......
Gyaran murya yayi tare da cewa fadeelarhtou sai ki fara shirya kayanki da duk abinda zaki bukata domin anjima da daddare uban gidanki zaixo ku tafiyyy......dasauri na dago cike da rashin fahimtar mai baban yake nufiii......na bude Baki zanyi magana Addah ta rigani da cewar malam bangane uban gida bah dan Allah fahimtar damu Dan kasamu a duhu.... murmushi yayi😊 yace ae Daman nasha fada muku yarana gaba daya kadarata neh Dan haka na siyar da fadeelarhtou gurin wani yaron kirki Kuma wlh ya siyeta da daraja naira million 10 zabura nayi jin abinda baban yaceh Ina jaa da baya Ina maimaita innalillahi wainna ilaihi rajun....babah karka min haka wlh duk abinda kk so indai nayi karatu nasamu aiki zanyi maka wlh inmah dukka albashina kace nabaka zan baka......hmm fadeelarhtou kenan ae kawai ki rike wannan burinnaki lokacin idan na mutu pha ae gwanda ynx nasan inda na dosa so kike kiyi min bakin ciki tohm wlh Baki isa bah....gashi Dan albarkan yaronnan yace duk wata bayan wannan million 10 zan dinga bani million 1 mai na manta....ban iya cewa komai bah saboda wani irin kuka da nake Mai cike da bakin ciki na durkushe a kasa ina cigaba da yin kukana....tashi yayi zai fita Addah da bakin ciki yahanata magana kawai hawayene yake xuba daga idonta ta dakatar dashi da kiran sunansa....juyowa yayi tare da yi mata wani irin malalacin kallo Yana fadar Baki da hurumin da zakiyi magana domin idan kin manta bari in tuna Miki fadeelarh bake kika haifeta bah dan haka ki adana kalamanki Yana gama fadar haka ya juya yafita kamar kububuwa...,..rumgumeni Addah taxo tayi itama tana kuka tarasa mah ta inda zata fara rarrashina........wajen karfe 9pm sai ga babah sun shigo tare da wani muna zaune a gurin da yabarmu Ina cigaba da aikin kukana na kwantar da kaina akan cinyar Addah Dan har wani irin matsanancin ciwon Kai naji na rabin kai😣
Ywwah gata nan alhajii keh fadeelarh kin gama hada kayannaki...banza nayi dashi dan a lokacin nayi masa wata iriyar tsana dan koh ganinshi bana son yiiii......Jin mutumin da yakirawo Alhaji nayi Yana cewa ae babah bana bukar ta tafiyy da komai ita kadai kawai nake Soo......Ahh tohm ae shikenan faduwa taxo dai dai da Zama sai in siyar da kayannata ayi cefa nan gida.......ban ankara bah naji an rike min hannu dasauri na tashi Ina wani irin nishi Kamar wata zakanya na fisge hannunah cikin tsiwa nake ce masa karka Kara rike min hannu Dan wlh zan iya kasheka😡wani irin kallo yake min nakasan ido Yana sakin murmushi tohm shikenan fadeelarhtarh tashi mu tafiyy....bah inda zanje domin baka da hurumin da zaka daukeni Dan bah baiwarka baceh......wata iriyar dariya Suka saki shida babah Addah Kuma tashi tayi ta shige dakinta tana kuka.....hannunah yakama Yana jana Ina tirjewa har muka fita daga gidan ya turani cikin mota ya rufe sannan ya shiga yaja motar mun dade muna tafiyy sannan Naga ya tsaya a wani hotel🏨ya fita ya shiga cikin hotel din inda ni Dana ga yafita na shiga kokarin bude murfin motar domin in gudu Amman inaaa ya kulleni ta waje ya dade a cikin hotel din inda yafito ya shiga motar ya jaaa fedeelarh kenan da zakiyi hakuri kidena kukannan da yafiye miki dan kuwa na riga da na siyeki Kuma mahaifinki neh yaxo har inda nake yayi min tallarki.....Kuma ni nagani na yaba yafada Yana kallona ta mudubin motar dake rataye a jikin motar.......ban iya cewa komai bah sai shashshekar kukana da yake tashi a cikin motar a wani dagiii naga yayi parking yafita da tare da zagayowa nima ya bude min kofar......nayi Kamar mah bansan Yana yin bah dan nayi matukar tsanarsu☹️ ganin banda niyyar fitowa yace wai keh Baki da tarbiyyah neh Baki San girmama nagaba dake bah koh??? Dagowa nayi dasauri tare da jan tsaki yayi matukar kaiwa bango da abinda nayi masa Dan har a fuskarsa sai daya nunah ya fisgoni daga cikin motar har Ina bigewa wata bishiya aikuwa sai ga jini ya wanke min fuska kaina yayi wani irin sarawa na xuba a gurin ban Kara sani halin da nake ciki bah sai farkawa nayi naganni a wani daki duk jikina yayi min nauyi koh motsin kirki bana iyawa......

Ku dakaceni sai Kuma gobe nice dai taku a kullum akoda yaushe Naanah Sha'aban🥰✍🏾
Chapter 35 · 0% Book details