← Book details Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 38

Sashe 29

Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

💜🤎 KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah M Sha'aban✍🏼🤎
Page 124-125
BAYAN WATA DAYA
Jikin Yaya fahid yayi sauki sosai kamar bai taba yin wani rashin lpy bah....yau yakama zaa sallameshi doctor Salim kuwa da yaga yasamu lapiya yaji matukar dadi Amman yaso fahid din yaxauna ana shida matarsa mommy ta nuna gaskiya bazata iya barin Samira ita kadai da tsohon ciki bah....tunda yanxu cikin yakai watan haihuwa akoda yaushe zata iya haihuwa babu yanda ya iya haka yabarsu suka biii jirgin karfe 3pm na yammah,....Ahmad tun a hanya yayiwa bilkisu text suna hanya...fahid kuwa Sam yaki barin Samira ta xauna kusa da mommy sai dai kusa dashi😊
A bangaren su Faisal kuwa yanxu wata iriyar soyayyah yakewa saudat din wacce bazata misaltu bah ita kuwa mamaki take mutumin da yace mata bazai iya zaman aure da ita bah shine yanxu yake yi mata soyayyah kamar zai cinyeta😂💔Tana zaune a dakin mamy kamar kullum tana Dan daddanna waya zama yayi kusa da ita bayan yayi sallama ta amsa masa honey yau shine ko kixo kiga lpy ta koh???ajiye wayar tayi Kai dear naxo pha Naga dakinka a rufe zan Kai maka breakfast yadafe kansa ohhh sorry wlh naje office neh akan wata shari'a da zamuyi hmmm kawai tace yakalleta sosai honey lapiya kuwa koh nayi laifi neh yatambayeta cikin damuwa😟Aa abinda tace masa kenan☹️Ai daman baka damu dani bah har katafi aiki Amman ko text bazakayi min zakaje aiki bah sai yanxu....yanzun mah zance neh yabiyo yasa har naji kaje aikin..... murmushi yayi Am really sorry honey yafada tare da janyota dasauri ta zame tare da nuna masa bedroom tana fadar mamy na ciki....cikin rada take maganar toh mene tazaro ido ni kam babu ruwana dariya ceh takwace masa matsoraciya kawai ni dai ayi hakuri kaina bisa wuya nah🙏toh shikenan komai yahuce Ni wlh gurin abbah mah zanje nagaji dasauri takalleshi dame kagaji???taje famasa tambaya ohhh tambaya kike mah hmmm da zama ni kadai yakamata akai min kehh Kuma inbaso ake in haukace bah🥰harararshi tayi tohm ai nasan bazaka iya bah Bismillah kaje kafadawa Abban cikin dariya take maganar😁Awww haka kikace zaki Sha mamaki kuwa nan da kwana biyu ki shirya a dakin mijinki zaki zauna baa dakin mamy bah tohm ai ki yanxu mah a shirye nake indai kaje kafadawa Abban tohm zan bika hmmm watau kehhh Naga alama a wasa kika dauki abin koh ehmn tabashi amsa a takaice shikenan honey ni kam Bari in tafi bacci nakeji sau da tadan taka masa xuwa bakin kofa sannan tadawo falon tayi kwanciyarta mamy duk tana jinsu kawai tayi musu shuru neh Kuma daman abban yana da niyyar saudat din ta tare a dakinta.......
Yau su Anni da baffah zasu xo iyayan daddy babu abinda kakeji a gidan yana tashi sai kanshi ana tafaman girke girke samira tana ta dauki suxo tagansu dan basu taba haduwa dasu bah duk xuwan da suke tana makaranta

💜🤍 KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah M Sha'aban❤️✍🏼
Page 126-127
Bahijjah tun da Yaya Ahmad yayi mata text yace suna hanya washe gari da sassafe suka fara shirin xuwa kano da ita da feenarht sai Yaya fauxan sunyi kyau sosai anko sukayi na wani material kofi colour mai rafin fari fari a jikinsa shi Kuma Yaya fauxan shadda yasaka xuwan xumah 8pm takwas nasafe suka gama shiri a motar Yaya fauxan zasuje suka nufi hanyar Abuja.......
Yaya fahid neh zauneh akan kujera Yana bin matarsa da kallo duk inda tayi idanuwansa nakanta ga cikin yayi tirtsetse da kyar take iya tafiya taci doguwar riga tasaka baby pink color da duwatsu akayi aikin rigar tayi mata kyau sosai xuwa tayi ta xauna kusa dashi tana tabe fuska.......baby kin gaji koh??Aa kawai babynka neh ya dameni tafada cikin muryar shagwaba🤗Ayyah tohm ai Kun kusa rabuwa dai kwana nawa neh zakiga kamar baa bah yayi maganar cikin kwaikwayar muryarta😌 murmushi kawai tayi hmm Yaya watau harda kwaikwayata koh??yawwah karfe nawa su Anni zasuxo neh nifa so nake suxo nagansu kasan bamu taba haduwa bah duk lokacin da zanxo ina makaranta Kuma kasan bakwana suke yi bah kafinna dawo sun tafiyy shiyasa nace yau bazanje bah🥰Aww ai kin daina xuwa makaranta sai kin haihu kin yaye min yaro sannan daa a wannan yanayin zan barki kije makaranta nakuda takamaki Ahhh lallai sweetheart😇❤️Kinga ai suna da dan nisa a yola suke ai yanxu sun kusa isowa xuwa karfe 5pm na yammah zaki gansu yau mah aunty binta zataxo😊yakarasa maganar tare da kamo hannunta
Eh yayana nasani ai mommyna tafada min tun jiya harda babbar 'yarta ai su Anni zasuxo da ita kaga itama bansanta bah kawai a gurin mommy naji sunanta Asnamint🤩yeah ai sunanta Asma'u su Anni neh suke kiranta da Asnamint shineh mommy take cewa itama haka🥰Ohhhh nagane yau banga kawuna bah kehhh wannan kawunnaki bansan duniyar da ya shiga bah yafada Yana harararta dariya tayi Ohhh kayi Yaya irin wannan harara haka sai kasaka xuciyata ta tsinke aiii Bari inje in kwanta inajin bacci kuma bayana ya rike min tafada yanayinta ya canxa lokaci guda....kallonta yayi sosai ko nakudarce baby
Wlh bansani bah kawai naji bayana yarike lokaci daya Kinga tashi muje Asibiti ai abin bana kwanciya baneh da taimakonsa ta tashi da kyar dai dai lokacin mommy tafito daga dakinta nufosu tayi dasauri lpy babban yayah mayafaru Samira koh nakudarceh tana yarfe hannu tace mommy bansani bah wlh koh itace mommy nakuda ceh dan muna cikin hira lokaci daya yanayinta ya canxa yanxu asibiti zamuje tohm ai nima biyo ku zanyi muje tare daman da mayafinta a jikinta nufi harabar da suke ajiye motocinsu mommy da Samira suka shiga baya shi Kuma fahid ya shiga mazaunin driver yaja motar da gudu suka nufi asibiti.....
Anan zan tsaya tunda shekaran jiya danayi banga anyi comments da yawa bah. Kuma Daman kunsan yawan comments yawan typing✍🏼✍🏼❤️much love

❤️💜 KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah M Sha'aban💜✍🏼
Page 128-129
Cikin minti 30 fahid ya isa asibitinsa saboda irin gudun da yake yi😇Yana xuwa ga wasu nurses nan suna jiran isowarsu da gadon daukar mara lpy shi ya dauketa ya daurata a gadon.......suka nufi labour room da ita suna shiga room din haihuwa taxowa Samira gadan gadan hannun fahid din takama tana fadin Yaya kataimakeni zan mutu.....tausayin matar tasa yakamashi tabbas Yana tsananin son Samira akanta yasan menene so....yasan dadinsa....Kuma yasan zafinsa😁da dayadda zaiyi yamaido da haihuwar kansa da yayi Dan bayaso Yana ganinta cikin wahala🥰yakasa tabuka komai kawai sai kallon matar tasa yake hannunwansu a rike da juna Yana ta lallabata Amman Ina Samira bata San mah Yana yi bah😟cikin awa daya ta haihu bayan doguwar nakudar da tayi ta tsawan awa biyu da rabi Yan biyu neh mace da namiji murna a gurin fahid baa magana bayan an gyara jariran ya daukesu yafita dasu dan ya nunawa mommy yaransa🤗😇"mommy" tunda ta karbi yaran takura musu ido yaran suna tsananin Kama da fahid har kamar mah tabaci sosai Kai Masha Allah wannan yaran dagani babu tambaya suna tsananin Kama da Abbansu mommy ta fada tana murmushi😊sunkuyar da kansa yayi Shima Yana murmushi wayarta dauko tashiga Kiran Yan uwa da abokanan arxiki tana fada musu Samira matar fahid ta haihu yanxu kafin mint 30 asibitin ya cika da mutane harda su bilkisu dan Basu dade da zuwa bah akace musu su mommy suna asibiti Samira ceh zata haihu......su bahijjah kuwa ai kafin kowa yaxo sukaxo ita da ra'isa
GIDANSU FAISAL
Tana xaune a dakin tayi shuru dan yau zaa daurawa Abbah Aure tare da innah wacceh take yi musu aiki babu Wanda yasani daga ita sai Abban.......innar da ta nuna rashin kin amincewarta Amman saudat taje ta dinga yi mata magiya harda kuka akan ta amince ta auri Abbannata shineh ta amince hmmm tasan tabbas mommy idan da abinda ta tsana a duniya tohm kishiya ceh dan ko wata taji ance mijinta yakara aure bazata kara gaisheshi bah Kuma zata dauki karan tsana ta dora masa tasan idan har taji harda sa hannunta kayi mata kishiya zata iya tsine mata ya dade a tsaye a gabanta amman kwata kwata Bata sani bah ta lula duniya tunani da tashin hankali zaunawa yayi tare da dafata honey dasauri tadago tare da kakalo murmushin yake naam darling meyafaru dake neh kwana biyu naga kamar kina cikin tashin hankali kuka tafashe dashi tare da rungumeshi🥺
Chapter 29 · 0% Book details