← Book details Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 38

Sashe 33

Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

___________💗💚 *KADDARATA*😔✍🏾
Story and by *Naanah M Sha'aban*✍🏾💗
Page 150-151
Yau yakama zaayi sunan samira kuma a yau bakin labari yaxowa mommy akan irin halin da yar uwarta take ciki.....tayi kuka😭tayi kuka harta gaji ta godewa Allah sumah duk sun sha kuka barin mah samira dan ita akwaita da saurin kuka Abu bai kai yakawo bah sai kaga tana yi masa kuka😧gaba daya suka dunguma suka tafiyy asibitin inda suka tarar da saudat sai birgima take tana rusa uban kuka tana bubbuga dakin da mommy take ciki likitocin sai rirriketa suke da yake itama yau tasamu lbryn rashin lpyr uwarta tah shineh tabaxamo Asibitin koh Faisal bata tsaya jira bah dan yau yana da aiki akan wata shari'a ta yara marayu.......
"Mommy" takaraso ta riketa tana bata hakuri itama kukan take sosai da sosai suka tausayawa saudat din dan sunsan tana bala'in son mommyn ta tah💔
Kiyi hakuri kinga bake kadai baceh bai kamata kina irin haka bah insha Allah zata samu lpy da izinin Allah kinji saudat dinta💚"mommy"tajata suka zaunah tana cigaba da rarrashinta.......
Tayi shuru tare da zabga tagumiiii😔
Bilkisu ceh take fadawa feenarh cewar mommyn yaya Ahmad bata da lpy tana asibiti mah dan haka suka tsayda ranar da zasuje gobe bayan an sauko daga sallar jumma'a idan mamy ta dawowa da jigawa da yake Nan neh garin iyayenta taje kai musu ziyara dan duk bayan wata uku tana xuwa taga mahaifanta🥰
Fahid kuwa yagama gyara gidansa dan daman mommy ceh tace sai anyi suna samira zata koma gidanta......
Saudat tana hango Faisal ta tashi daga inda take takarasa gurinsa tana kara fashewa da kuka riketa yayi sosai yana bata hakuriii.......
Yakaraso rike da hannunta suka gaisa da mommy da Anni😍suka amsa masa yasamu guri ya zaunah Amman saudat taki ta xauna sai faman kuka takeyiiii....
Haba saudat kidena kukannan dame zanji da kukanki koh da rashin lpyr mommy inda kuka zai mana maganin halin da muke ciki da tuntuni yayi mana dan haka kiyi shuru kidena kuka kinji mommy ynx addu'armu take bukata bawai wannan kukan bah insha Allah.....Allah zai bata lpy kinji zo ki zaunah.....ta rakube akusa dashiii tare da kama hannunsa ta rike sosai tana ajiyar xuciya☺️😇
Fadila tunda taxo gidan Alhaji Ibrahim take tazagaye gidan tana tunanin ta yadda zata shiga sanye take da katon hijabi idan ka ganta Kai kace tah Allah bazata iya aikata mugayen abubuwa bah.....kawai ta yanke shawarar da tayi knocking din gate din..,.tana fara knocking daya biyu Mai gadi ya bude kofar karamar gate din....sai da yakare mata kallo yaga bai taba ganin mai kamanninta bah.....yah lpy kuwa baiwar Allah...tadan yi murmushi daman Samira nake nemah koh tana nan....babah Mai gadi kwata kwata bai yarda da yanayinta bah dan yasan duk wacceh zataxo gurin Samira indai bai santa bah tana fada masa tace zatayi bakuwa wata rana har hotonta take nuna Masa yaddah idan taxo xai ganeta.....barantana yasan dukkansu basa nan yauu sunah asibiti......
Yadan yi murmushi shimah tare da cewa Allah sarki samiratuu ae sunyi tafiyah kasar waje yau kwanansu bakwai da tafiyyah babu kowa a gidan......ta cije lebe tare da juyawa bata ceh masa komai bah.... Anan ya tabbatar da hasashensa dan haka ya rufe gate din ya shiga dakinsa ya Kira fahid a waya yafada Masa duk yaddah sukayi dashi tare da ceh masa wlh yallabai ka kula da hajia dan kuwa akwai Wanda yake nemanta da mugun nufiyyy Fahid ya jijiceh sosai tare da yiii Masa godia🙏😇 yace Masa babu komai☺️💔

💔💚 KADDARATA😔✍🏾
Story and written by Naanah M Sha'aban✍🏾💔
Page 152-153
Wani irin rikitaccen ihu tasaki mai hade da kuka tare da xubewa kasa sumammiya da likitan ya sanar dasu mommyn saudat ta mutu😭haka aka dauki saudat ranga ranga aka nufii emergency room da ita don ceto rayuwarta da ta jaririnta...........
"Mommy" kuka kawai take dan tana bala'in son yayar tata gashi yau takoma ga mahaliccinta
Kowa a gurin ya tausayawa Faisal irin halin da ya shiga ga mutuwar mommy data girgizashi ga kuma matarsa da baisan a wane irin hali take ciki bahhhh......
Haka suka nufi gida da gawar danyi mata sallah mommy Kuma tace zata zauna da saudat din har sai ta farfadooo.....
Bilkisu sun xo sun tarar da halin jimamin mutuwar mommy itama tayi kuka sosai dan ita Ahmad kawai take tausayawa😇Allah sarki soyayyah🥰🌹
Ankai mommy an dawo masu kuka nayi masu yi mata addu'a nayi innah mah tayi kuka sosai......tajawo ra'isa ta rumgumeta sosai Allah ya jikan hajia ya gafarta mata annabi yasan da xuwanta🙏 ra'isa ta amsa da Amin tana kuka.....
Fahid kuwa tunda babah Mai gadiii yafada Masa game da fadilah yaje ya sanarwa yan sanda duk abinda yafada masa suka nufo gidan tare dashiiii........
Tana xaune a bakin gate din tayi tagumi tana tunanin yanxu mai zata sanarwa da usman tasan tunda ya furta idan bataxo Masa da Samira bah zaii kasheta tohm zai ae kata😔Bata ankara bah taga Yan sanda sun xagayeta da bindugogiii tashi tayi a firgice wata Yar sanda mace taxo ta daura mata ankwa tana fadar uh re under arrest babu musu tabisu tashige motar Yan sanda shikuma ya huce gurin jana'ixar..........
Saudat kuwa bata san Wanda yake kanta bah
Sai karin ruwa da allurai ake mata kusan kwana uku ana haka

Dan Allah duk mai KADDARATA daga page 120 xuwa 130 ya turo min plx🙏🙏🙏
Anan zan dakata sai Kuma gobe😁✍🏾✍🏾✍🏾

💔💚 KADDARATA😔✍🏾
Story and written by Naanah M Sha'aban✍🏾💚
Page 154-155
BAYAN KWANA UKU DA RASUWAR MOMMYN SAUDAT
Gida ya kwashe ya rage sai Yan uwa........kuma a yau saudat tafarfado daga doguwar sumar da tayi dan da har sun fidda ran zata rayu ganin irin abinda takeyi dan daga baya idan ta farfado sai kuma takara suma.....mommy ceh ta rumgumeta tana fadar haba saudat karki tayi ki barmu kemah Dan Allah ki tashi kicire komai a ranki ae nima tamkar uwa nake a gurinkiii daga yau ki dauka Kamar aunty sadiya cehhh kinji yarinyata😇takarasa maganar cikin muryar kuka...dakyar saudat tafara kokarin magana...mo...mommy karkiyi kuka Dan Allah insha Allah zanyi kokarin incire komaiiii Amman ni gani nake Kamar nice sanadiyar mutuwar mommy tafada tana kara fashewa da kuka.........zaunawa Faisal yayi akan gadooo yace saudat kidena wannan tunanin Allah neh ya riga da kaddara iya kwanakin da zatayi a duniya.....kidena dorawa kanki laifin mutuwar mommy Dan kinsa daddy yayi aure kawai ynx abinda tafi bukata shine addu'a🥰
Dagowa tayi ta xuba Masa ido tabbas duk da irin damuwar da take ciki sai da taga ramar da Faisal din yayi Kuma tasan duk saboda tana kwance bata da lpy da Kuma rasuwar Mommynta........yayanah haka kadawo baka cin abinci koh??? murmushi kawai yayi sannan yace taya zan iya cin wani abinci bayan Ina tsoron karki mutu ki barni🥰
Tohm pha soyayyar ta tashi pha masu karatu😃😜
Tashi mommy tayi dasauran mutanan gurin suka fita Dan su basu guriii.......rumgumeshi tayi tana shafar kansa Shima din rumgumeta yayi tsam a jikinsa bazan iya fada muku irin yanayin da ma'auratannan suka tsinci kansu a wannan ranar Kamar zasu cinye juna.......
Washe gari aka sallamo saudat daga asibiti Kai tsaye gidan aunty rahma suka nufa "mommyn Fahid"shikuma Faisal yahuce gidansu ya gaishe da iyayensa a zuwan da daddare zai xo gidan.......a babban falo Suka yada zango dan su bilkisu mah Basu tafi bah sai anyi bakwai zasu tafii..mommy ta tara su saudat tafara magana.....babban yaya kaineh babbah yau zan shirya ku da Yar uwarku dan na fuskanci har ynx Babu Wanda yakewa wani magana a cikinku.... saboda wani Abu yataba hada kuu abaya sai Kuma ace Kuna gaba da juna Kuma ahaka zaku ceh ku musulmai neh bayan ansan duk musulmin gsky bazai taba yin gaba da Dan uwansa bah koda ace na kwana daya neh.....Dan Allah ku zama abin sha'awa abin kwaikwayo ga jama'a ku manta da duk abinda yahuce a baya ku dauka tamkar bai taba faruwa bahh......Samira ta numfasa tace mommy wlh ni daman ban taba rikon aunty saudat a xuciyata bah Kuma insha Allah komai yahuce indai ta bangarena neh.....mommy insha Allah bazaki Kara jin wani abu yakara hadani da saudat bah Kuma Daman ni nadauketa tamkar ciki daya muka fito da ita..........mommy ta kalli saudat wacce ta sunkuyar da kanta bata dago bah *yarinyata* banji kince komai bah....ta dago tace ae ni daman komai yahuce tuntuni a gurinah....tohm Masha Allah Kuma Shima Faisal din idan yaxo zanyi masa magana ku ynx gaba daya Yan uwan juna neh.........Suka danyi hira sama sama daga karshe kowa yaje ya kwanta mommy tace saudat taje dakin Samira ta kwana a chan dan so take takawar da gabar dake tsakaninsu gaba daya..........saudat taje ta kwanta daga karshen gado ta ja bargo tare da lumshe ido itama Samira ta kwanta daga farkon gadon tare da jan bargo ta lilliba........wayar saudat wacceh take bedside drower kusa da Samira ta hau ringing...hannu Samira tasa ta dauki wayar tare da cewa aunty saudat ana kiranki...ta bude ido tare da karbar wayar Bata ceh mata komai bah....Faisal neh ta daga wayar tare da cewa Assalamu alaikum darling....lpy klau wlh duk ya dameni tohm sai da safe yaya plx ka kula da kanka...abinda kawai Samira taji tafada kenan ta kashe wayar tare lumshe ido baa fi minti 2 bah bacci da dauketa dan daman jiran Kiran Faisal neh yasa batayi baccin bah🥰💔
Chapter 33 · 0% Book details