← Book details Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 38

Sashe 13

Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ay kuwa bari in kirata yanxu tasata tafitar min a gida Aa Alhaji karka kirata kawai kataho daga Paris kaxo da kanka kakoreta tohm gobe ki saurareni karfe 10 ina gida ywwah tafada tare d kashe wayar shi kuwa usman murna yake tunda yasan samirar bata d kowa idan an koreta shi kuma zai bita sai ya mayar d ita dadironsa har ya kama gidan da zai kaita a chan bangaren mommy kuwa shiri suke sosai na xuwa kano mommy har ta sanarwa d abba anga babynta shima yayi murna sosai yace goben ajirashi tare zasuje daukota mommy tace to shikenan babu wanda ya sanarwa d fahid labarin ganin samira abba kuwa karfe 6 agarin abuja tayi masa nan suka shirya abba d mommy da yusuf motarsu daban sai yaya umar da daddy da jafar suma motarsu daban sai aunty binta d yaranta uku su kausar motarsu daban suka dauki hanyar garin kano shi kuwa abbansu usman bai taho da wuri bah karfe 10 yashigo gidansa a dai dai lokacin motarsu abbah tashigo gidan samira dasu bilkisu duk suna farfajiyar gidan dan mommy takira fauxan tace sun taho mommy na fitowa a mota samira ta tafi da gudu ta rumgumeta tana kuka mommyna ni banyi tunanin zan kara ganinki bahh dagota mommy tayi tana cewa tohm yi shuru mana maiye na kuka ba gani nan naxo bah gurin abba taje ta tsugunna har kasa tagaisheshi ya amsa cike da farin ciki karawa tayi gurin aunty binta ta rumgumeta shi kuwa umar gurin abokinsa fauxan yaje yana masa godia ❤️❤️ KADDARATA😔✍🏼 Story and written by Nanah M Sha'aban✍🏼❤️ Page 58-59 Haka suka rankaya suka shige gidan har alhaji Ibrahim babu Wanda ya kula da abbansu fauxan dayake jikin motarsa yayi mutuwar tsaye hamdala yake Yana godewa Allah dayasa bai ruga su alhaji Ibrahim zuwa bah mutum da bai taba ganinsa a fili bah sai a t.v yarsa taxo har gidansa ay yasan zai sha kudi dan yasan irin kudin dayake dashi bazasu taba kwatantuwa bah mutum da kasar waje mah sun san da zanshi sai gashi yau a cikin gidansa lallai yau da hajia ummah tasashi yayi abinda bah shine bah shiga gidan yayi a babban falo ya tarar dasu dasauri fauxan yaxo ya rumgumeshi Yana fadar abbah sannu da xuwa murmushi yayi tare da cewa sannunka yarona dafatan kana lpy fauxan yayi mamaki kwarai Dan duk sanda Amman yadawo ya rumgumeshi tureshi yake ya zazzabga masa mari Dan shi Usman kadai yadauka a matsayin dansa dagowa yayi Yana murmushi jin dadi lpy klau feenat itama taxo da gudu ta rumgume abban nata Dan suna sonshi sosai Amman irin hantar da yake musu shiyasa suke jin shakkar yi masa magana myy nayi missing dinki pha nima daddyna fauxan yadago da feenat toh karki karya Mana shi dariya abban yayi sannan ya kalli bilkisu dake gurin mamy yace uwata ke baxakixo ki tari abban naki ba kodai fushi kike dashi dariya tayi takaraso gurinsa ta rumgumeshi tana fadar aa abbana baka laifi chan Kuma yakalli su alhaji Ibrahim da suke kallonsu cikin murmushi manyan Baki mukayi kenan yau a gidannamu kamar alhaji Ibrahim bukar mistan kudi a garin abuja bilkisu tace eh ay aunty Samira sukaxo dauka yau kwanta biyu a gidannan Allah sarki tashi alhaji Ibrahim yayi sukayi musapaha sannan Shima abban yaxauna mommy ceh ta kalli jaririyar dake hannun mamy tace wannan mah yarki ce ya sunanta Aa ba yarinyata bace ta Samira ce mommy ta tashi a firgice dasauri hajia ummah takaraso gabanta ganin duk sun mike gaba dayansu ba Ina nufin Samira ce tahaifeta bah Aa Ina nufin Amana ceh a gurin Samira anan tabasu labarin da Samira tabasu sannan ta Dora dacewa kunji ta yadda tasamu jaririyar ajiyar xuciya sukayi gaba daya sannan mommy takarbi jaririyar taxauna suma duk suka xauna Samira takalli mommy tace mommy yanxu ko suna bata dashi murmushi tayi tace indai Dan ta suna ne zaa samata yanxunnan kuwa sunan mahaifiyarta kawai zaa mayar mata dashi sannan takalli alhaji Ibrahim tace abbah gata kayi mata hudu bah murmushi yayi tare da karbar yarinyar yayi mata Kiran sallah a kunnanta bayan yagama yace toh yau idan muka koma gida za'ayi bikin sunanta gobe mommy tace Allah yakaimu goben hajia mama dafatan duk zakuxo dai goben insha Allah zamuxo dukanmu Abban fauxan yace Allah yaraya yayi mata albarka duk sukace Aamin sai a sannan yasan cewa lallai shi kwata kwata ba yayiwa matarshi da yaransa adalci wadda Kuma ita yafara aura gashi yanxu a gabansa alhaji Ibrahim ya dauki dawainiyar yarinyar daba su masan asalinta bah harda bikin suna zasuyi mata shikuma yaran cikinsa da matarsa abin alfaharisa mah yakasa kula dasu saboda wata banxa mara tarbiyyah kallon hajia mamah yake Yana jin hawaye kamar zasu xubo masa hannu yasa Yana gogewa Dan karsu subo karab idon mamy yakai kan alhaji tabbas tasan danasani yake yi Amman indai itace ta riga da ta yafe masa karyawa sukayi sannan alhaji Ibrahim yakarbi number abbah sannan mommy mah takarbi number mamy suka tafi feenat tana tsokanar Yaya daddy da cewa ay Yaya idan naxo duka abincinka zai cinye sai dai pha ka kwana d yunwa dariya yayi Dan yarinyar tana matukar burgeshi yace haba my feenat karki Bari su Yaya umar suji pha zasuyi Mana dariya dariya sukayi tare da cewa ay mun riga min ji mota suka shiga suna dagawa juna hannu har suka fita daga gidan ❤️❤️ KADDARATA😔✍🏼 Story and written by Nanah M Sha'aban✍🏼❤️ Page 60-61 Sai da su mamy suka daina ganin motar su mommy sannan suka koma falo hajia ummah suka gani fuskarta a murtuke da Usman a gefensa Shima babu walwala a fuskarsa gurin abbah taxo Kai tsaye tafara yi masa fada kamar ita ta haifesa Kai alhaji haka mukayi da Kai munyi idan kadawo zaka kori waccen karuwar Amman saboda tsabar rashin cika alkawari shine ka biyewa wannan dakikiyar matartaka da......bata karasa abinda zata fada bah sai ji kake tas tas tas ya dauketa da mari hagu d dama bah hajia ummah da Usman neh kadai sukaji tsoron Marin da yayiwa umman bah hatta mamy dasu Yaya fauxan sunyi matukar mamaki yau ace alhajine ya Mari yar lelen matarsa wadda komai tafada ya zauna Kuma haka take bashi umarni saboda irin son da yake mata dakuma cewa ita tayi zurfi a karatunta ita Kuma mamy iya kacinta secondary shiyasa a cewarsa yake fifita hajia ummah akan mamy Ni zakixo kina fadawa wadannan maganganun saboda kawai Ina sonki toh daga yau kisaka a ranki yadda sakina take agidan a matsayin matata haka kema kike a matsayin matata Kuma idan na karajin kinyi mata makamanci irin gorin nan wallahi sai kin tafi gidanku Kuma karki saka ran zaki dawo Kuma danki wannan Dan iskan mara tarbiyyah bashi da aiki sai lalata yammatan mutane matsayinsu daya dasu fauxan daga yau idan nakarajin kunyi musu wani abu da baiyi min bah to sai dai ku nemi gurin xuwa bakina ikirari babanki Yana da mahaukacin kudi bah kawai kin aureni abisa kaddara Amman duk sanda akace yau bani da kudi zaki gureni Dan bazaki iya zama da talaka bah koh toh ni daga yau zan fara kyautatawa wacce Koda ace bamu da inda zamu kwana da ita da yarana bazasu taba guduna bah sakina muje babban falon hajia sakina suka shiga sukuma su fauxan kowa yahuce dakinsa yasa masa key Dan sun san haukar umman sai ta huce akansu anan ta durkushe tana wani gunjin kuka Usman da bakin ciki ya kamashi gashi burinsa bai cika bah akan Samira gashi Kuma daddynsa dayake saran idan yadawo zai karbi wasu Yan kudade yau zasuyi casu a club Kuma yammatansa duk sunce zasuje gashi wannan mommy taje tayi abinda bai kamata bah ai data bari yakarbi kudinsa sai tayi masa duk abinda zatayi tsaki yaja sannan yahuceta Yana fadar idan kinyi kukan kin gama kyama tashi da kanki Dan ni Banda lokacin jin wannan kukan duk kin lalata min shirina aikin banxa kawai bin shi da kallo tayi tabbas tasan da hajia mama ce abbah yayi mata haka sai fauxan ya daga ta Kuma ya rarrasheta bazai taba barinta cikin halin da take ciki bah yanxu sai ta dada fashewa da wani kuka a bangaren daddy da mamy kuwa yana rike da hannunta har sai da taxauna akan gado sannan Shima ya xauna kallonsa kawai take Shima din kallonta yake fuskarsa dauke da damuwa sakina kiyi hakuri nasan nayi miki abubuwa da yawa dabasu dace ace nayi miki bah kina matsayin matata dasauri tasaka hannu ta rufe masa baki kadena bani hakuri karka manta Kai pha mijina neh Kuma Ina tsananin sonka Dan haka na hakuri tuntuni kadena dawo da abunda yariga ya huce takarasa maganar tana murmushi murmushi Shima ya mayar mata yakama hannun da ta rufe masa baki ya sumbaceshi wannan ranar sunyi bacci Mai dadi tare da nunawa juna soyayyah Samira kuwa Basu isa garin Abuja bah sai karfe 4:45 kasancewar motar su mommy ta shiga Mai gadi ya bude musu makeken gate din suka shiga mommy ceh tafara shiga cikin gidan dasauri Dan har walima suka hada ta dawowar Samira gida kawayenta fauxiyyah da Zahra a farfajiyar gidan suka tarar dasu suna jiransu suna ganin Samira suka rumgumeta gaba dayansu suka ranka duka suka shiga babban falon irin yadda aka kawata falon baa magana ga Kuma babban cake har guda biyu daya an rubuta welcome home Samira daya Kuma an rubuta welcome to d world ifteehal dayake tun suna hanya mommy tayi waya take a ciyo wani cake din ifteehal Kuma Yusuf neh yace a dinga cewa kanwarsa ifteehal anyi party sosai Samira ta shiga tsananin farin ciki ganin yadda kowa yake ta ta babu abinda zata cewa mommy sai dai Allah yabiyata da gidan aljanna ♥️♥️KADDARATA😞✍🏼 Story and written by Nanah m shaaban✍🏼♥ Page 62-63 Yau yakama zaayi taron sunan ifteehal su mamy sunxo anyi taro masha Allah in shirya iftee cikin wasu kaya wanda mommy tasa yaya daddy yayi mata siyayyah mai tsada neh kwarai dagaske dan zai kai kimanin 250k ga wata siririyar sarkar gwal da dan kunne da aka sa mata tayi kyau sosai samira kuma suna tare dasu bilkisu su ta hirar duniya duk wannan abin da ake
Chapter 13 · 0% Book details