← Book details Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 38

Sashe 4

Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by nanah m sha'aban❤️✍🏼
Page 14-15
Anan take tasa danta lawalli yakirawo mata kanwartata tana xuwa tafada mata abinda boka yace mata tadora dacewa nasan ke kadai zaki iya yimin wannan abin dariyar mugunta safara tayi tace haba aunty ay ki kaddara dacewa wannan yar iskar aminatou ta mutu kawai ki bani kullin magungunan zanje na dinga shishshige mata har sai na tabbatar da cewa bata yin sallah zan zuba mata a abinci kuma na samata a ruwan wanka ahaka sukayi sallama tun daga ranar safara take xuwa gidan aminatou sai yamma wani xubin dare take tafiya aminatou duk da cewa bata yarda d safara bah amman haka ta batarta akwai ranar d su ayuba sukaxo sukayiwa aminatou rashin mutunci safara tana nan wai acewarsu tayiwa dan uwansu bukar asiri yanxu kuma ya mutu shine tadawo kan babban yayarsu haladu ita kuwa aminatou bata iya cewa komai bah har suka tafi dan inda sabo yariga da ace tasaba d halin su yaya ayuba ita kuwa safara suna tafiya ta fashe d kukan munafirci tana cewa yanxu aunty aminatou ahaka kike zaune agidannan kullum sai su yaya ayuba sunxo suyi miki rashin mutunci gsky bazan iya tsayawa ina ganin ana wulakanta mace mai sanin darajar mutane mace mai hankali da nutsuwa kowa a kauyannan yana shedarki ni nasan baxaki iya yiwa kowa asiri bah yakamata suma su san haka matsowa aminatou tayi kusa d safara tana taba hakuri samira dake hannun safara tafara kuka aminatou ta dauketa ta zaunar d ita tadauko mata abincinta tasa mata agabanta wani irin kallo safara tayi mata azuciyarta tana fadar lokacin mutuwarki yakusa kin isa ki auri mijin yayata ay kinyi kadan ita kuwa aminatou tun daga ranar tacire duk wani shakku d take akan safara Allah sarki baiwar Allah toh su safara basu samu sunyi galaba akan aminatou bah har sai d samira takai shekara 7 aranar jumma'a safara taxo gidan tasamu aminatou kwance take tambayarta lpy kuwa tace ciwon mara take Alhamdulillah yau burin aunty zai cika tafada acikin zuciyarta amman dan ta tabbatar tace ayyah ay inajin bakonki na wata ne zaixo eh wllh aminatou tafada samira dake gefen aminatou tace sannu innah to samira allah yayi miki albarka bari inxo inkawo miki abinci koh inyaso sai inje insiyo miki magani to nagode safara tana fita taxubo mata abinci ta kunce zaninta data kulla maganin d boka yabasu dayake kullum dashi take xuwa gidan ta sa maganin sannan takaiwa aminatou sai d tabbatar tafara ci sannan tafita acewarta ta siyo mata magani amman tana fita gidan auntynta taje take sanar mata yaufa aminatou zata sheka duniya tadora d cewa wai nan acewarta magani zan siyo mata dariyar mugunta matar haladun tayi tace ay bata d wani magani dan daga yau bazata kara kwana a duniyar bah abangaren aminatou kuwa safara tana fita tafara wani aman jini duk samira ta rude dan haka tafita d gudu tashiga gidan inna tana fada mata innarta tana aman jini kafin su shiga gidan har aminatou ta mutu Allah sarki rayuwa kenan babu wanda bai ji mutuwarta bah haladu kuwa lokacin d yaji mutuwarta faduwa yayi ya suma sai d aka yayyafa masa ruwa sannan yafarfado haka aka shafe zaman makoki aka gama haladu yace zai dauki samira haka aka tattara kayan samira ita kuwa matar haladu tayi alkawarin ganawa samira a zaba tunda taje gidan wanke wanke shara har wanki tana yi abinda innarta bata taba sata bah ga kuma tallah safe d rana duk yayanta takoya musu musgunawa samira bata bata abinci sai dai ragowa awani xubin kuma haka zata fita waje idan makobta sun xubar d abinci xata diba taci duk abinda ake labari yana xuwarwa inna amman bata d halin taimakawa samira dan akwai ranar d taje takai mata abinci haladu yana xuwa matarsa tace ay tana xuwa tana xiga samira tayi mata rashin kunya har gida yaje yayiwa inna rashin mutunci d gargadin ko ahanya taga samira karta kara nunawa tasanta duk irin wahalar d matarsa takewa samira shi bai sani bah akwai ranar d tadora mata talla d safe haka ta fita tana tafe tana kuka dan yunwa takeji wajen kauyansu ta nufa inda zai sadata d bakin titi umar ne kannin fahid yake tuki cikin nutsuwa dayake yaxo duba mahaifiyar abokinsa bata d lpy dasuke service tare dashi dan yau suka gama yau kuma yake sa ran tafiya abuja kiransa akayi awaya wanda yayi dai dai d xuwan samira wajen mortar shi kuma yana tayi mata hon duk tabi tarude tarasa yazatai ta kaucewa matar garin yakauce mata ai kuwa tabigeta haka ta fadi sumammiya dasauri ya ajiye wayar d take ta ruri yafita yadauki samira sai asibin dake wajen kauyen wanda akauyan indai aka kaika wannan asibitin toh ansan babanka mai kudine sosai
Chapter 4 · 0% Book details