Sashe 3
Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
litinin da safe aminatou tayi kuka har tagaji lokacin d labarin mutuwar bukar ta isa ga yan uwansa sun rude hatta haladu mah kuka yake sosai duk d cewar a yanxu xai sami damar cika muradinta na auran aminatou bayan sadakar bakwai aminatou tana rike d samira saboda kuka tasaka domin sai a yaune mutuwar ta dawo mata sabuwa wani yarone ya shigo tare d yin sallama kallo yaron tayi batare d ta amsa masa bah wai haladune yace a sanar dake zai shigo cike da mamaki ta dago yaya haladu kuma tafada cike d mamaki sannan tamayarda dubanta ga yaron tace kace ya shigo yaron ya amsa d cewa toh yafita tashi tayi tasa hijab tafita xuwa tsakar gida dan taji dame yaxo a bangaren haladu tunda yaro yaxo yafada masa abinda aminatou tace ya shiga gyara malum malum dinsa wacce tasha guga yana shiga yatarar d ita a tsaye bayan sun gaisa bai boye mata bah yasanar d ita abinda ke tafe dashi wani malalacin kallo tayi masa sannan tace yaya haladu wa kakeso ka aura murmushi yayi yace kemana Kinga ana arba'in sai a daura mana daure saboda bana son ko...... cikin masifa ta dakatar dashi kadauka bani d hankali bani d tunani bansan me nakeyi bah toh karka manta d aminatou kake magana wacce a kullum baka d buri kai d yan uwanka irin kuga kun rabani d bukar toh yanxu ya mutu shine zaka kwaso min wasu gajiyayyun kafafuwanka kace min zaka aureni tohm bazan aureka bah kai ko mafarki nayi na aureka wlh wlh sai nayi tir d allah wadanshi kafice min a gidan tun kafin natara maka mutane ❤️❤️KADDARATA😔✍🏼 Story and written by Nanah m shaaban❤️✍🏼 Page 12-13 Duk dacewa haladu yaji zafin maganar d aminatou tafada masa baisa ya yaga bakinta bah shi abinda yasa yake nunawa yan uwansa su tsaneta shine yasami damar auranta da bukar yasaketa idan suka tilasta masa haka yaja jiki yatafi duk jikinsa babu laka ita kuma takoma dakinta ta dauki samira dake shan baccinta ta dorata akan cinyarta bayan ta zauna akan gadon tunanin mijinta bukar tashiga yi tana kuka tamkar ranta zai fita awani bangaren kuma tana ta kokarin ta kuntatawa haladu ada ta yadda sunyi mata wulakanci amman yanxu bazata yadda bah a kwana atashi yanxu shekarar samira biyar ta girma sosai ta debo kamannin babanta bukar sak amman farin aminatou tayi yarinyar kyakkyawace gata d hakuri duk yara d manyan yan kauyen suna sonta sosai har gida suke zuwa su dauketa dayake kullum yarinyar tsaftsaf zaka ganta abangaren haladu kuwa kullum sai yaxo gurin aminatou amman bata fita wani lokacin idan ya aiko yaro ya kirawota haka zata kora yaron sai dai yaga yaro ya fito da gudu yahuce shi ranan nan daya gaji sai ganinsa tayi a tsakar gidan tana yiwa samira wanki tana sanye d hijabi dayake bata rabo da hijabi dan wani lokacin harda shi take kwana ita kadai ce dan ma'u yar gidan innah taxo ta dauki samira tun daxu dasauri ta mike tana kallonsa ranta abace watau abin haladun yakai har ya shigo mata cikin gida batare d ixini bah yanxu d awani yanayi yaganta pha kiyi hakuri na....... Cikin masifa tace kaga dakata yaya haladu kai baza'ace yayan bah haladu karka kara cewa komai kawai fitar min a gida ni bansan kai wane irin maye bane na rabu dani bazan iya aurenka bah fita ko nayi maka ihun kwarto ta bude baki zatayi ihu yace kinga yi hakuri karki yi ihu zan fita haka ya fita xuciyarsa cike da son aminatou wani uban ashar ladidi matar haladu tayi dan safara kanwarta takawo mata gulmar taji ana kuskus din cewa haladu yana son aminatou ay wlh aminatu bata isa bah ni danake d boka dukusau ay yau dinnan Aminatou bazata kwana araye bah nan safara tasaka shewa yawwah aunty shiyasa nake sonki kwai ki kawar da shegiya ki nuna mata ke ba sa'arta bace murmushi tayi wanda kana ganinsa kasan na mugunta ne ko da taje gurin bokan yabata kullin magani yace daya tayi wanka dashi daya kuma ta tabbatar d cewa aminatou bata sallah sai ta xuba mata a abincinta daya kuma a ruwan da zata sha haka ta dawo gida tana tunanin toh taya zaay tasan aminatu bata sallah bayan ita da ba xuwa gidanta take bah sai kuma tayi murmushi d ta tuna kanwarta safara dan tasan ita kadai ceh zata iya yi mata haka akwai ta d makirci da kuma iya tuggu