← Book details Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 38

Sashe 30

Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

❤️💚 KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah M Sha'aban✍🏼💚
Page 130-131
Ta dade tana kuka bai iya ce mata komai bah sai da yabari tayi Mai isarta sannan ya dagota fuskarsa na nuna tsantsar damuwa cikin muryar rarrashi yake ce mata Honey kiyi shuru ki fada min wai meyafaru hankalina ya tashi pha.....dan naga tunda nace miki gobe zamu koma gidanmu Naga kamar bakyau cikin walwala koh kin dena sona neh dasauri ta girgiza mishi Kai tana fadar Aa darlin wlh I luv uh with all my heart❤️💋Kuma Ina matukar farin ciki da zamu koma gidanmu koh ynx mah kace in tashi mutafi zan bika cikin farin ciki💃 Darling Abbah neh zai kara aure Kuma nice nan nayi hadin auren wlh nasan idan mommy taji zata tsine min shine hankalina ya tashi dan mommy tayi matukar yarda dani😢 subhanallillahi honey kinsan pha mommy bata son kishiya saboda me yasa kika bada shawarar ayi mata kishiya yaushe zaa daura auren Abban??? Yau neh inagama an daura dan 10 na safe suka ceh ynx kuma 11🥴Ajiyar xuciya yayi tare da janta a jikinsa kinga kidena kuka zamu rufe zancen nan babu Wanda zai san ke kika hada auren Abban mah nasan bazai fadawa mommyn keh kika hada auren bah tohm shikenan darling dafatan kin shirya kayanki dan gobe 12 mah muna gidanmu.... murmushi tadan yi eh tun jiya....Masha Allah honey suka dan taba hirarsu ta ma'aurata sannan yatashi ya tafi.....
Zukar tabarshi yake Yana furzarwa hayaki duk ya tunnike gurin rike yake da bindiga tabbas bazai taba barin Samira bah tunda taxo gidansu yaji Yana sha'awarta kuma yanxu lokacin neman kudine ya kyaleta a wanchan lokacin Amman yanxu dole saceta kota wace iriyar hanya ceh domin ya jefi tsuntsu biyu da dutse daya nafarko zai saceta da niyyar kidnapping... nabiyu Kuma yacika dadadden burinsa akanta.duk irin yanayin da Samira take yana sani dan ko motsi tayi sai anfada masa....yatura wata mara imanin da taje tashigewa samirar domin tahaka neh zai samu ya saceta cikin sauki......
Karfe 5:30pm na yammah dai-dai su Anni suka sauka a cikin asibitin dan tun suna hanya aka kirasu a waya akace Samira ta haihu suna asibiti...
Kayi musu jagora har dakin da samira take hutawa tsayawa Anni tayi cak tana karewa yarinyar da aka Kira da Samira kallo tabbas wannan yarinyar kama suke da yarta Aminatou kamar antsaga kara....Aminatou tafada dai-dai lokacin data yanke jiki tafadi...
Samira wacceh take a xauneh Yaya fahid Yana kusa da ita yana bata lbr ta firgita jin Annin ta Kira sunan innarta "Abbah"kuwa Yana jin lbrin kanwarsa Aminatou Dan tun Yana karami Anni bata da lbr sai na Aminatou Amman bai taba ganin hotonta bah Amman meyasa Anni takira sunanta Kuma tafadi ya jijice kwarai dasauri yakarasa gurinta yana fadar Umar kirawo doctor Yaya fahid neh yakaraso ya ciccibi Anni Kai tsaye emergency room yakaita baffah kam bai kalli inda samirar take bah hankalinsa ya tashi matarsa tafadi Dan duk lokacin da taga wata yarinya fara sai tace yarta ceh Aminatou.....Allah sarki😢

Ana zan tsaya sai mun hadu a next page

Taku a kullum a Koda yaushe NAANAH KHADEEJARH MUHD SHA'ABAN

💜❤️ KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah M Sha'aban✍🏼💜
Page 132-133
Kusan Awa biyu kafin likitoci su samu su shawo kan Anni ta farfado Amman tana farfadowa da Kiran Aminatou tafara fahid ya rumgumeta Yana kuka haba Anni so kike murasa ki kinsan dukanmu nan muna tsananin sonki Kuma mun damu dake......Aminatou wlh Naga yarinyata sanda na shigo dakinnan tana zaune kana mata magana....dasauri fahid yadan daga Anni Yana fadar Anninmu kina nufin samirah Ai ita ceh matata Kuma ba sunanta Aminatou bah yafada cikin muryar da take nuna zallah damuwa da yake ciki......Abbah da yake zaune kusa da Anni yace Kai fahid je ka taho da Samira domin taganta Dan itama samirar tadamu sosai......babu musu yafita yaje dakin da samirar take ita da mommy neh da Kuma sauran mutanan da sukaxo asibitin......yakamo hannun Samira suka nufi dakin da annin take harda sauran mutanan "mommy"ceh a gaba itama tana rike da hannun samirar rike da jaririn namiji a hannunta Yaya umar ya dauki jaririyar shi Kuma.........
Suna shiga dakin karaf idanuwan baffah akan Samira Wanda yayi tagumi akusa da gadon da Annin take a Kan kujera....Dan yarasa mah meke yi masa dadi...mikewa yayi a firgice Yana nuna Samira Amintou.. Aminatou kece ..kuka Samira tasaka tana fadar Ni ba sunana Aminatou bah sunan Innah tace kuma tamutu.....Dan Allah Yaya kafada musu ba sunana haka bah😔yahaka yakarasar da ita har inda suke ya zaunar da ita a kusa da Anni.....Yaya umar neh yace baffah tabbas bah sunan Samira Amintou bah sunar innarta ceh haka Dan ta taba bani labarin cewa Anni da baffah iyayen innar an nemesu baa gansu bah tun kafin a haifeta suka bata Kuma babu inda baayi cigiyarsu bah Amman baa samesu bahh....baffah yace umaru ai mune Ashe da rabon bazamu gana da Aminatou bah sai yasaka kuka yarinyar arxiki Mai biyayyah itama Annin kuka take sosai.....ita kuwa Samira farin ciki yakamata kenan wadannan neh iyayen innarta shikenan itama tana da danginta💃❤️ta rumgume Annin tana fadar kidaina kuka kenan yanxu bakwa farin cikin ganina Ai nima bah kamarmu daya da innah tah bah tohm ku dauka tamkar ita ceh Annin ta kamkameta tana fadar Ina matukar farin ciki dakema kuka ganki sosai da sosai kawai muna kukan mun rasa yarinya Mai biyayyah da hakuri Amman dafatan kema zakiyi koyi da halinta..domin idan kikayi koyi da halin mahaifiyarki kin gama dacewa duniya da lahira eh Anni zanyi insha Allah......Abbah yayi murna matuka Ashe Samira yar kanwarsa ceh shiyasa yake jin yarinyar araansa Ashe ita jininsa ceh....fahid mah haka Dan farin cikin da yake bai boye bah kana kallan Kan fuskarsa zaka San Yana cikin farin ciki mara misaltuwa..... BAYAN KOMAI YALAFA...Samira take tambayar Anni....innah ta bata taba ce min tana yaya bah Amman nan kince Abbah mah danki neh Kuma Aunty binta mah haka.. hmmm 'yata ai wannan lbr neh Mai tsaho ki Bari idan mun koma gida zan Baki lbrin komai.....tohm shikenan.....su bilkisu kuwa bayan sun duba Yaya fahid Kuma sukayi wa Samira barka suka fara Shirin tafiya a xuwan sai bayan suna zasu dawo...
Ta rike wuyan rigarsa tana ta zazzaga masa ruwan Ashar da masifa tunda aka daura auren bata sani bah sai yau... Yau din mah kamasu tayi a dakin abban tadawo daga gantalinta take masa ihu tana ce masa mazina ci shine yake fada masa ya aureta matsayinsu daya da inna larabawa shi bah mazinaci bah Dan bah taba xina bah ko kema zakiyii min shaidar haka ganin idan yabarta Zata iya illatasu yasamu yatura dakinta ya rufe da key

Wannan page din bashi da wani yawa kuyi manage dashii plxxxx

Nice dai taku a kullum NAANAH KHADEEJARH MUHD SHA'ABAN

💛💚KADDARATA😔✍🏾
Story nd written by Nanah M Sha'aban🥰✍🏾
Page......🤪
Kuka take sosai Faisal Yana tafaman rarrashinta da yake yau watansu daya da tarewa kankameshi tayi tana tafaman shashsheka cikin shashshekar take cewa darling kaji irin halin da mommy ta tsinci kanta gsky ban kyauta mata bah tayi matukar yarda dani Amman na yaudareta anhada Baki dani anyi mata abinda tafi tsana a cikin fadin duniyar Nan.......
Bubbuga bayanta ya shiga yi Yana rarrashinta da maganganu masu dadi🥰😇tayi matashi da kirginsa sun dade a haka har bacci yayi awan gaba da ita dayake Daman dare neh ya dauketa yakaita dakinsa ya kwantar da ita Shima ya kwanta ya lillibesu da bargo mai taushi😌🤩
BAYAN KWANA DAYA
Abin mommy tun abbah Yana tunanin na dan lokaci neh Amman yanxu mommy abin ya citira dan tunda yasamu ya rufeta a daki abi ya juye yazama hauka.....
Dan ynx har yakai tana cisgar gashin kanta tana ciiii duk ta farfasa kayan dakin gaba daya jikinta kuwa duk ciwo neh Babu komai a jikinta Dan duk ta yayyagasu Abbah yakirawo Asibitin mahaukata bayan yasaka mata Kaya da kokawa tana ta tonawa kanta asiri Kuma tana zagin Abbah Kai abin Babu dadi su bahijjah sai kuka suke Suka tafi da ita Asibitin dan a binciki lpyrta.....Babu Wanda yafadawa saudat Dan Abbah yace karsu sake su fada mata Dan Shi yasan abinda ta shuka Shi tafara girba .....
Yau su Anni Suka koma gida yakama sauran kwana biyu ayi sunan Samira yaron namiji akasa masa shurac macen Kuma taci sunan innar Samira Aminatou Fahid kuwa Rai da Rai suna tare Samira da yaransa Yana nuna musu zallar soyayyah ita kanta samirar tana tsananin jin Fahid din a ranta ga wata iriyar soyayyarsa da take ji a cikin xuciyarta💔 ko dai dai da minti 1 neh Bata ganshi bah sai taji xuciyarta duk Babu dadi😕😟Zahra da fauxiyyah sunxo tun ana sauran kwana biyu su dawo saboda zasuje wani bikin Yan uwansu bazasu samu suxo suna bah🤩
Taji matukar rashin Jin dadin da Basu samu damar xuwa suna bah Amman Babu yanda ta iyahhh..
Zaune suke Dan Anni ceh ta tarasu yau takeson tasanarwa dasu Abbah ko wacece ita da Kuma yanda akayi Basu Suka rabu da Abbah tun Yana karami😧🤕

Yawan comments🤩💔yawan typing✍🏾💚

Taku a kullum akoda yaushe M..Sha'aban💚💜💙
Chapter 30 · 0% Book details