← Book details Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 38

Sashe 38

Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

❣️❣️ KADDARATA😔✍🏾
Story and written Naanah M Sha'aban✍🏾❣️
Page 174- 175
Kowacce aka kaita gidanta babu wanii nisa tsakaninsuu Rayuwar Amaran tazama abin shaawa kowannansu Yana ganin yaga yah kyautatawa Dan uwansa ga wata tsaftatacciyar soyayyah da suke nunawa junah....Kai yah Allah kahadamu da masoya wadanda zasu so mu badan wani abu namu bah.....Ameen ya rabbil'alamin🙏💖
A bangaren Samira kuwa nan mah Babu saukii dan fada suke da Yaya fahid akan cikin da take dashiii ita Kuma tace Bata son ta haihu ynx saboda suu iftee koh shekara daya basuyi bah Kuma ace ynx tana da ciki........saudat ceh ta kirata a waya take shaida Masa ta haihu tayii murna sosai dan haka tayi Masa text kamar hk Assalamu alaikum ynx aunty saudat ta kirani take fada min ta haihu zan shirya ynx naje nayi mata barka........tana gama rubutawa ta tura daman Bata dade da yin wanka bah Dan hk hijabi kawai ta dauka ta tarkata yaran suka nufii gidan saudat din.......hira suke sosai da ita wannan yaro dai kamanninsa daya da babansa.....wlh kuwa kowa hk yake cewa mamah da taxo sai da tace kamar Yaya Faisal lkcn Yana karamii.....hmmm kinsan menene kuwa Aa sai kin fada ynx pha Wai ciki garenii kaiii haba Masha Allah kice Ana da Yan watanni zamu Sha suna......mtsww sisi kenan nifa bana son nakara haihuwa ynx Kuma akan hk mukayi fada da Yaya ynx mah baya yii min magana Nima Kuma bana kulashiii.......wa'iyaxubillahii saudat tafada tare da tashi daga kishin gidan da tayiii Samira menake jii Yana fitowa daga bakinki sai kace bah musulma bahh kehh da nake tunanin idan kika jii wata tana fadar makamancin irin wannan magana zaki hanata Amman keh kike fada....mutane nawa kika san suna neman haihuwa Ido rufe Amman basu samu bah keh kin samu Amman kike kokarin yiwa Allah butulcii akan abinda yabakii Kuma bayan hk har kika barii mijinki yake fushiii Kuma Baki damu bahhh kinsan kuwa tsinuwar da take tare da kehhh Kuma kinsan tsinuwar mala'iku bawai irin tamu baceh Dan hk tun wurii kije kisamu mijinki kibashi hkr akan abinda kikayiii😇hawaye neh kawai yake xuba daga cikin idanuwanta tabbas ita dahh a tunaninta akan dai dai take sai ynx tajii nadama ta shigeta tabbas nayi kuskure aunty saudat Amman insha Allah a yau dinnan zan gyara komaiii zamu koma kamar dahhh......ywwah Kinga ynx mah ki tashiii ki tafiii murmushi tayi tace aww watau korarmu kike Ahhh bah dole bahhh tunda kina kokarin yii Mana bakin cikin samun baby tafada tana dariya😀tashii Samira tayi ta hada kayansuu tohm mu kam mun tafiii😊ywwah gwanda ae tajaaa suka nufii inda tayi parking din motarta tana xuwa gida taganshi har ya dawoo ta shiga da sallama sai da takai suu iftee dakinsuu sannan ta dawo ta hada Masa abinci Mai saukiin sarrafawa ta daukeshi ta nufiii falon dashii a cikin tiraiiii Yana Nan inda tabarshiii sai da ta ajiye abinciii sannan ta tsugunna har kasa ta kamoo hannayensa tana xubar da hawayeeee Dan Allah Yaya kayi hakurii wlh sharrin shaidan neh Kuma nah yarda zan haihu idan kullum kace inyiii wlh zanyii ka yafe min🙏🙏🙏dagota yayi ya rumgume shikenan komai ya huce Samira tunda har kika game gsky Kuma ae niii Daman bai taba rikonki a cikin zuciyata bahh.....ngde yayanah❣️❣️sai da ta xuba Masa abincii ya cika cikinsa sannan tajaa shi suka shiga dakiii.........yau Yakama za'ayi sunan saudat suu bilkisu duk sunxo fadeelarh kuwa a gidan ta kwana A gidan mommy saudat tace zaayi sunan ae kuwa gida ya dinke da jama'a koh tahh ina....... fadeelarh ceh tafito waje neman ifteehal saboda taxo ta ciii abincii kamar ance ta juya wahh zata ganiii addarta ceh a tsayee suna gaisawa da wasu mata duk da irin yadda ta chanxa Amman wlh koh a ina ta ganta zata ganeta ae kuwa tasakii farantin abincin da yake hannunta ta ruga da guda ta rumgumeta tana fadar addahta sai Kuma tasaka kuka😭😭 fadeelarh addah takira sunanta cikin muryar jin dadiii Ashe zamu Kara haduu fadeelarh nii a tunaninah shikenan wannan azzalumin yarabanii da keh bazamu Kara haduwa bah kaiii Alhamdulillah Allah kadawo min da yarinyata🥰 ita sai fadeelarh tana rumgume da ita gani take kamar idan ta cikata zasu Kara rabuwa............Yaya Umar neh yazo hucewa Dan ya manta abu a dakinsa shine ya dawo ya dauka yaga fadeelarh ta rumgume innah matar abbansu saudat ya shiga mamakii meya hada fadeelarh da innah Kuma yakarasa tare da yin sallama fadeelarh da tajii muryarsa ta kamashiii ta rike kam tana fadar Yaya addata ceh yau naga addah Dan Allah kace Maya karta Kara barinah murmushin dadi yayi tare da cewa kaiii Alhamdulillah kuxo mu shiga ciki ae Babu Mai rabaku suka shiga suna man cike da farin ciki Yaya Umar ya zaiyanawa mommy komai ae kuwa murna kan murnah ranar fadeelarh a jikin innar ta wunii da daddare kowa ya watse suu saudat da Samira sun koma gidansuu ya rage sai suu bilkisu da Kuma addah da mommy yayah Umar neh yace tohm addah ina abbah da Kuma suu aliyu hmm Ayyah ae bayan tafiiyar fadeelarh sai Kuma ya dawo kan suu alee a lkcn sun girma sosai ni kam naki yarda domin a lkcn fadeelarh ya nuna min cewar ae bah yata bace kaiiu magana har takaimu gah kotuu da yaga alkali Yana neman ya daureshii sai ya hkr ranar Nan na fita anguwa na barsu aleeyu sai dawowa nayi naga gidan ya kone harda abbannasu.....
Ayyah Allah ya jikansu mommy tafada cikin tausayawa... Ameen hmmm Allah yajikan suu Aliyu da Dan karamin kananinah nayi rashi babbah tafada cikin muryar kuka Ameen ae ni ynx Banda wata damuwa tunda gakii☺️😊Ana dai suka Dan taba hirar sama sama sannan kowa yaje ya kwanta kwana daya sukayii suka koma gidajensu Yaya Umar neh yasamu ya lallaba fadeelarh har ta yafewa mahaifinnah Amman ya shafama da ita kafin ta yarda.....abin farin ciki a cikin satin da suka koma suka fara laulayii lkcn da akaje aka gwadasu sunyi matukar farin ciki da doctor yafada musu suna da ciki............yau suna kallon t.v kamar kullum labaran dare aka Nuno wani mutumi Yana kuka tare da hoton wata baiwar Allah a hannunsa kamar ance Samira ta kallii t.v wazata gani surayya ceh kenan wannan neh baban iftee tafada arazane meyafaruu honey Yaya abban iftee neh pha ga hoton surayya a hannunsa itace mamanta
Number da mutumin yabada yaaya fahid ya dauka.......... Ya Kira ae Kuma ringing daya biyu aka dauka da sallama Kaine mijin surayyah.....cikin sauri muryarsa nah rawa yace eh nine abdulhakim.....ok ina son kaxo akwai magana Mai mahimmanci da nake so muyii....... Ok tohm shikenan A ina kake so mu hadu Anan yayi Masa kwatance Ae kuwa washe gariii da sassafe sai gashi ya dauka a gidan mommyn fahid a falon saukar Baki aka saukeshi.......Daman Samira tun karfe 6am sukaxo daga fahid sai shii abdulhakim din suke zaune bai boye Masa komai bah daga haduwar Samira da surayyar har ixuwa mutuwarta da Kuma wasiyyar da ta barii kan cewar kar asake a bashi yarta.......yayi kuka sosai sannan ya kalli Yaya fahid din yace ngde maka sosai Kuma duk abinda surayya ta yanke akaii nah bazanga laifinta bah Amman ina neman wata alfarma ina son duk bayan satii daya zanxo ina dinga ganin yarinyata, murmushi yayi sannan yace indai wannan neh karka wani damu.....sun dade suna hira sannan aka kawo masa ifteehal ya ganta sai wajen la'asar ya tafiii........tun daga ranar abdulhakim duk bayan satii daya sai yaxo yaga ifteehal din sun Saba da ita sosai Dan kullum idan zaixo cikin soyayyah yake mata Dan Yana matukar Sonta sosai.........Rayuwar su haka ta cigaba da tafiya cikin farin ciki.....ina dasu bilkisu cikinsu yakai watan haihuwa koh yau ko gobe........feenarh ceh tafara haihuwa inda ta haifii yarinyata mace tacii sunan mommy rahmah suna ceh Maya nihal.....sai asma'u inada Rana daya suka haihu da fadeelarh Kuma duka Maza suka Haifa yaron fadeelarh yaciii sunan abbah Ibrahim suna ceh Masa khalifa......ina da yaron asma'u ya cii suna usman.....bilkisu Kuma Yan biyu ta Haifa inda dayan yaxo Babu Rai aka sakawa yarinyata sunan mommyn Ahmad Sadia.....anyii shagalin suna Babu karya kamar bazaa dainah bah bayan suna da wata biyu Samira tahaifii yarinyarta mace inda kasa Mata sunan Anni radiyatu saudat mah takara haihuwa namiji akasa sunan baban Faisal.....
RAYUWAR YAN UWAN TAZAMA ABIN SHAAWA DA SON JUNA
Alhamdulillah!
Alhamdulillah!!
Alhamdulillah!!!
Anan nakawo karshen wannan littafin..... KADDARATA❣️❣️❣️❣️❣️WhatsApp 08122188717
Instagram:Nanah M Sha'aban
Facebook:Nanah M Sha'aban
Wattpad:naananciey
Telegram:Pinky's gyaran jiki nd more

BABANA NEH SANADI COMING SOON💞💞✨
Chapter 38 · 0% Book details