← Book details Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 38

Sashe 26

Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

💔❤️ KADDARATA😔✍🏼
Story nd written by Nanah sha'aban✍🏼❤️
Page 106-107

WASHE GARI
Wajen karfe 12:30pm na rana Aisha matar hamxa taxo gidan lokacin Samira bata Dade da dawowa daga makaranta bah suna zaune daga ita sai mommy a falon su Yaya umar suna wajen aikinsu ifteehal kuma bata dawo daga makaranta bah sai karfe 1:30 suke dawowa da yake yanxu a primary 1 take ta tsugunna har kasa ta gaishesar da mommy ta amsa fuskarta cike da fara'a kamar kullum Samira ta gaisheta tare da tambayar fayyad tace fayyad Yana makaranta tashi mommy tayi tana cewa bari in shiga daga ciki indan kwanta kafin wadannan Yan rigimarsu dawowa dariya Samira tayi tare da cewa tohm mommy a fito lpy ywwah Samira ta shige dakin samira ta kalli Aisha tana cewa wallahi aunty Aisha yau nake shiri xuwa gidanki Aa toh na hutar dake maman Yan biyu hmmm aunty kenan
Samira yau fa xuwannaki neh toh aunty meyafaru mijinki neh ya aikoni hmmm watau xuwa yayi ya hadani dake Aa wlh kwata kwata bahaka baneh Samira meyasa kike masa haka yakamata ki bashi dama Koda sau daya neh karki zama mai rikon abu a cikin ranki nasan yayi Miki abubuwa da dama bazama su irgu bah ya dauki karan tsana ya Dora Miki Amman yanxu ya gane gaskiya ya fahimci abinda yayi Miki baidace bah Yana so ki yafe masa Aunty Aisha wlh ni ban taba rikon Yaya fahid bah tunda nake a rayuwata ni nasan hakan duk a cikin KADDARATA neh kuma cikar imanin mutum shineh ya yarda da kaddara Mai kyau da mara kyau Amman aunty Aisha Yaya fahid Baki da Baki ya fada min da kansa cewa shi jikina yakeso taya zan yarda dashi taya zan gane cewa so yake na yafe masa ba yaudarata zai karayi bah yakara tarwatsa min rayuwa kuka tafara yi😢Aisha tayi shuru chabb lallai kam akwai babban aiki a gabanka babban Yaya tafada a cikin xuciyarta shi da bakinsa yafada Miki haka ta gyada kai alamar eh shikenan Kinga ki daina kukannan Kar mommy taji tafito hawayen tashiga gogewa Aisha tadaura da cewa ni ban mah san Kuma Mai zance bah gaskiya nima banji dadin abinda babban Yaya yace miki bah Amman bakomai nidai zan cigaba da yi muku addu'a komai zaiyi dai dai insha Allahu burinmu naganinku Kun xama cikakkakun ma'aurata zai tabbata Samira bata ce komai bah dai nan Kuma suka shiga hirarsu ta mata sai dasu ifteehal suka dawo sannan ta mike tare da cewa Bari in tafi su fayyad sun kusan dawowa karfe 2pm ake tashinsu mommy ta shiga tayiwa sallama ta fito Samira tacewa idi driver yakaita har gidanta yace tohm bakomai sai da suka fita daga gidan sannan takoma gidan.......
Wani irin kururuwa yakeyi dukka dajin sai amsawa yake tunyi babban kuskure sai da nafada Miki ga yanda zaa binne layar kuma yarinyar akeso ta binne Amman kuka Saba abinda nace toh a yanxu Mai kikeso nayi Miki ka taimakamin Dan Allah ka....kee baa ambaton Allah anan kinsan da Allah kikaxo nan kayi hakuri kataimaka min dai tohm zan taimaka Miki Amman sai yarinyar taxo Dan akanta za'ayi aikin murmushi tayi tace bakomai indai wannan neh zataxo tashi tayi ki tafi da baya da baya a haka tayi ta tafiya tafi daga dajin ta shiga motarta ta nufi gida cike da farin cikin tasamu ta shawo kan bokan yanxu tasan babu wani mugun abunda zai faru dasu Kuma burinsu zai cika
❤️💔 KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah M Sha'aban✍🏼🥰
Page 108-109
BAYAN WATA DAYA
Bilkisu ceh a zaune a falo tana turawa Ahmad text kamar kullum duk ranar jumma'a dan yanxu suna dan waya jifa jifa kuma suna chat sama sama dashi dan ga abinda text din ya kunsa Assalamu alaikum yayana dafatan kana cikin koshin lpy ya mommy da Abba dasu bahijja duk kagaishe min dasu ya Allah Ina rokonka kadafawa wannan bawan naka a duk abinda yasa a gaba Allah ka taimakeshi a kowane irin hali ya tsinci kansa ya Allah ka kareshi daga dukkannin sharri na dare da na rana da duk wani mai binshi da sharri jumma'a Mubarak bro Ahmad🥰ta dade tana karanta text din idan tagama takara karantawa sai kuma tayi sending..tana ta murmushi..... daga chan bangaren Ahmad neh zaune ya Yana koyawa kannansa karatun Addini kamar kullum yaji sakon text ya shigo tun kafin ya dauko wayar yake ta faman sakin murmushi dan yasan bilkisu ceh dan a irin wannan lokacin take turo masa sakon jumma'a ya dauko wayar ya karanta sannan ya tura mata da reply dinta kamar haka su bahijja suna nan lpy Ameen Ameen my darling sister nagode sosai Allah yasadamu da Alkhairin dake cikin wannan ranar Ameen ki kula dakanki kinji babyn yayanta❤️ji yayi anyi gyaran murya daga bayansa a dai dai lokacin da yaturawa bilkisu sakon juyawa yayi da sauri tare da saka wayar a aljihu dan ganin auntynsa saudat murmushi take tare da cewa Ahhh lallai Ahmad kace mun kusan samun sirika Kai aunty yafada tare da sunkuyar da kansa toh wa......Aunty saudat Wai Ina mommy taje yau kwannanta uku pha bata dawo gidannan bah tun ranar da Naga ta fito daga dakinta dasauri ta shiga mota ra'isa ce ta tambayeta dan mommyn bata taba fita takai har kwana uku bata dawo bah zama saudat tayi tare da cewa tohm ra'isa wlh nima bansani bah Amman dazu na Kira wayarta tana shiga Amman bata daga bah Amman insha Allahu tana lpy tohm Allah yasa Ameen suka Amsa gaba dayansu..........
Yarasa yadda zaiyi da Samira kwata kwata yanxu abinnata maimakon yaga sauki sai mah wani irin sabon rashin mutunci da wulakanci da take masa gashi Aisha mah daya aiketa ta shawo masa kanta da yaje yaji ya sukayi da ita take ce masa ita babu abinda zata iya tunda shi yajawa kansa yace mata jikinta yake so kwanansa uku ko baccin kirki mah baya samu yayi aikin mah baya xuwa kullum Yana gida abinda Samira ta fada masa jiya daddare ya shiga dawo masa ya shiga gidan ya tarar babu kowa a falon kai tsaye ya nufi dakin Samira yayi saa a bude yake hangota yayi a chan kan gado tana kwance ta lilliba da bargo kasancewar lokacin sanyi neh karasawa yayi ya xauna kusa da ita dasauri ta tashi jin mutum a bayanta dan Daman ba bacci take bah kawai dai ta rufe idonta neh kallonsa take ido cikin ido tare da jifa masa tambaya waya baka izinin ka shigo min daki haba Samira ki tsaya ki saurareni ban shigo miki daki da niyyar nayi miki wani Abu bah naxo neh dan na wanke kaina a gurinki wlh bada wani Abu Ni nace Ina son......dakata min tafada tare da daga masa hannu banson inji komai ka mayar Dani shashasha ceh ko Kuma zaka ce banji abinda kace bah Kai ka fada da bakinka Kai jikina kake so kuma ba kana kusantata bace dan kana Sona ko Kuma kadena tsanata Aa ko daya kana yineh Dan kana bala'in son jikina ko bakai baneh ka fada min bah??tafada hawaye na xuba daga idonta😢
Samira nasan na Fadi haka Amman kiyi hakuri Dan Allah badani bah ko Dan babyna dake cikinki hmmm ko bah baby bah tafada tana masa wani irin kallo Mai hade da harara tohm daga Kai har baby Ina Samira bukar natsaneku wlh fahid bana sonka bana son naji Koda sunanka neh ka fice min a daki tun kafin nayi maka illah ka fita nace kafita tafada cike da masifa da hargagi tashi yayi daga kwanciyar da yayi tare da zabga tagumi da yaga zaman da yayi babu abinda zai kara masa sai mah wani Karin damuwar ya tashi yashiga toilet ya daura alwala ya shimfida dadduma ya tada sallah sai da yayi raka'a biyu sannan ya idar ya zauna Yana jan carbi Yana ta addu'o'i da ya gama ya shafa Yadaga hannayensa sama Ya Allah nasan nayi wa Samira abubuwa da dama wandanda bai kamata nayi mata bah Amman yanxu nagane Ina son ta fahimci dagaske nake yanxu ni Sam ba jikinta nake so bah ita nake so ya Allah ga bawanka nan Yana yi Yana kuka😭Wai Ni kuwa nace yau fahid neh yake kuka akan samira🤔☺️
❤️💔 KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah M Sha'aban✍🏼💔
Page 110-111
Saudat! Saudat!! Saudat Wai kina Ina neh mommy ceh tashigo gidan ko sallama babu tana ta kwadawa saudat din Kira su Yaya Ahmad suna falon suna ta mata sannu da xuwa Amman ko takansu bata bi bah....saudat ceh ta fito dasauri daga dakinta Dan lokacin fitowarta kenan daga toilet tayi wanka hijabin sallarta tasaka kawai ta fito jin mommy tadawo tana kiranta ywwah yanxu kije ki shirya boka Yana son ganinki akan barambatamar da kikayi min nasamu nashawo kansa yace sai kinxo Dan akanki za'ayi aikin taba Baki saudat tayi tare da dauke kanta mommy ta kalli saudat din Wai ke badake nake magana bah......Ni bah Ina zanje nadena xuwa gurin kowaneh Dan iska natuba kema mommy shawarar da zan Baki ita ceh kituba tun kafin lokaci ya kure miki wlh Dan.........wani irin mari mommyn tadauketa dashi tare da cewa ni kike fadawa wadannan maganganun banxan kina cewa wani kin tuba tohm wlh sai kinje Dan bahaka bah zan tsine miki bazakija min matsifa bah Ina zaman zamana kallon mommyn take a firgiceh mommy yanxu kina goyon bayan inje in cigaba da sabawa Allah kenan yanxu.....keh Kinga dakata min ni zakiyiwa wa'axi toh Bari kiji tun kafin a haifeki nake xuwa makaranta xuwa wajen bokaye da malamai da Yan tsibbu tun Ina gidanmu nake xuwa ke bari kiji mahaifinku dana aura baya sona Amman tahanyar bokaye da malamai gashi nan Yana min biyayyah kamar yayi min sujjada mommy!! Mommy Anya ke bah shaidan baceh saudat tafada cikin kuka dariya tayi aini nafi shaidan mah Kuma yanxu umarni nake bari kafin nahawa sama na sauko ki tabbatar kin tafi tana gama fadar haka ta fara hawa step din benan ni wlh bazanje bah sai dai ki kasheni Kuma wlh kika takura min sai naje ai nasan gurin da kikaje kika binneh layoyin da kikayiwa abbah asiri wlh sai naje na tonesu da sauri tajuyo tayo kanta saudat dataga haka tayi saurin shigewa dakinta tasaka key bugun kofar take kamar zata karya tana fadar Dan ubanki karki fasa tonewa shegiyar yarinya wacce tayi gadon tsiyah su Yaya Ahmad kuwa tashi sukayi suka bar falon Dan sun san mommyn zata iya dawowa kansu ........
Bilkisu tana ganin text din Yaya Ahmad murna ta cikata babyn yayanta💔tashiga maimaita sunan tana murmushi ahaka feenarh taxo dafata tayi itama tana murmushi aunty bilkisu irin wannan murmushi haka kodai Yaya Ahmad neh yayi Miki message Mai fasa xuciya duka takai mata Dana fadar yar banxar yarinya🥰 dariya sukeyi gaba daya... tohm yanxu ki tashi mu shirya muje partyn farida kinsan yau neh Ok Allah sarki Amarya wlh namanta bari in shirya din Ok idan kin shirya Ina falon mommy Yaya fauxan neh zai kaimu tohm feenarht ta tashi ta fita ita Kuma ta shiga toilet Dan tayi wanka........
Nishinsa kawai kakeji tun daga kofar shiga falon gashin yauwa tagama masa illah Dan rabon da yaci abinci har ya manta wayarsa yajawo yakirawo number mommy nishinsa kawai takeji sai kokarin magana yake Amman sam yakasa cikin tashin hankali mommy take tambayarsa lapiya mummy..mummy abinda ya iya furtawa dakyar kenan dasauri mommy ta katse wayar ta ta shiga daki ta dauko mayafi bata tsaya ko Ina bah sai wajen dasuke ajiye motocin su ta shiga motarta sai gidan fahid din
Kuyi manage da wannan sai mun hadu a next page
💔❤️ KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah M Sha'aban✍🏼💔
Page 112-113
Mommy na zuwa gidan ko tsayawa batayi ta kashe motar bah ta nufi kofar da zata sadata da tafkeken falon nishin da taji tun daga kofar shiga falonneh ya kara tayar mata da hankali Kai tsaye dakin da take jin nishin ta nufa kwance taganshi rabin jikinshi duk a kasa yahada kansa da katifar gadon karasawa tayi jikinta duk a sanyaye yarona meyasameka bai iya ce mata komai bah sai nishi da Kuma kokarin yin magana dayake yi zama tayi a kusa dashi takomo hannayensa hawaye na zuba daga idanuwanta na tausayi sa...mi..mi..rah abinda yafada Yana wata iriyar jijjiga nan mommy takuma rudewa ta fita dasauri takira ado driver yataimaka mata suka saka shi a mota tashiga motar tajata dagudu
FAHID SPECIAL HOSPITAL tanufa tana zuwa taga hamxa da wasu ma'aikatan asibiti nurse suna tsaye da gadon da ake Dora marasa lpy dan tun suna hanya mommy takira hamxa take fada masa gata nan xuwa asibiti fahid bashi da lpy bata jira Mai zai ceh bah ta kashe wayar dan bata son yin waya tana driving......tun kafin tayi parking hamxa yanufi motar dasauri ma'aikatan suna biye dashi tana yin parking hamxa ya bude kofar baya daya daga cikin ma'aikatan yatayashi dauko fahid din suka dorashi a gadon........
Emergency room suka nufa mommy nabiye dasu a dai dai kofar dakin hamxa yacewa mommy ta tsaya anan yadauko mata kujera yace tazauna mommy ki kwantar da hankalinki kinji insha Allahu fahid zai tashi ba abinda zai sameshi tohm hamxa Dan Allah kayi duk yadda zakayi ka ceto rayuwar yarona tohm mommy zanyi iyakan bakin kokarinah zama tayi tafara Kiran layin abbah shi Kuma hamxa ya shige emergency room cikin mint uku su abbah su kaxo gaba dayansu hardasu Ahmad dan Yaya umar neh yakirashi yake fada masa shineh suka taho gidan... dasu bahijjah saudat kuma zataje gidansu Faisal abbansa ya Aiko Yana son ganinta shiyasa bata biyo su bah.........
Chapter 26 · 0% Book details