← Book details Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 38

Sashe 2

Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wai har ni bukar zaka dubi tsabar idona kace wai bata d lpy amman tana d lpyr kwanciya ko haladu yafada cikin daga murya yaya haladu indai kunxo kutadar min d tashin hankaline a gida dan Allah kutafi lantana dake gefen yaya haladu da ita d talatuwa suka fashe d kuka yanxu yaya bukar kai d kanka kake korarmu daga gidannan wanda d baka d buri irin kaga munxo gidanka cewar lantana haladu yakatseta d cewar haba lantana karki damu asirine kuma mu baxamu taba yarda bah sai takarya shi kuxo mutafi haka suka tafi cike d jin haushin Aminatou shi kuma haladu yana jin dadi yanxu yasan dole sai sun tilas ta bukar yasaki aminatou domin ya cinma burinsa akanta abangaren bukar kuwa karasawa yayi Aminatou ya shiga rarrashinta d bata hakuri ta dago tana kallonsa daman sai danace maka ka dinga tafiya aikinka karka damu dani tafada tana kara fashewa dasabon kuka amina kinfi min komai mahimmanci banxan bata barin a irin wannan halin bah ina sonki ina sonki yafada yana goge mata hawaye murmushin jin dadi tayi duk da irin yadda takeji zuciyarta na tarasa yanxu dai ki tashi ki shiga daki in karasa wankinnan shuru tayi dan so take tace masa kawai yabar wanki zata karasa amman kuma tasan halinsa bazai yarda bah kamar yasan me take tunani yace ko dai bazaki iya tashi bah na daukeki dasauri tatashi tashiga dakin cike d jin kunya haka yatashi yakarasa wanki yayi wanke wanke dai dai lokacin d yagama yaji anfada kiran sallar magribah alwala yayi ya leka dakin sallah yatarar d ita tanayi yace mata matata mai jin kunyar mijinta zan tafi masallaci sai na dawo takusan yin dariya amman tahadiyeta shi kuma yafita xuwa masallaci ❤️❤️KADDARATA😔✍🏼 Story and written by Nanah m sha'aban Page 8-9 Washe gari bukar yana zaune yana taya Aminatou ninke kayan da suka wanke jiya tadan kalleshi tayi murmushi dan a duk lokacin d suke tare dashi takan ji wani matsanancin farin ciki ko da kuwa ace tana cikin damuwa yau bazakaje gona bah ta tambayeshi kanta a sunkuye yadan dago yakalleta inda sabo yajiga d yasaba Aminatou tunda sukayi aure bata taba kiran sunansa bah ko kuma tace mai gida kamar yadda suke cewa matan garin sai dai tayi masa magana kai tsaye eh bazanje bah yabata amsa yana ninke doguwar rigar d tarage baa ninke bah ta dago takara dubansa akaro na biyu haba meyasa naji sauki pha dan allah kaje kaga yanxu su yaya haladu zafina sukeji suna ganin kamar ni nahana kaje aikin tafada tare d durkusawa a kasa gwiwoyinta na bisa kasa dan tasan idan har bahaka tayi masa bah bazai yarda yaje bah yakalleta sannan ya miki tare d shigewa uwar daki sai d yayi shirin xuwa gonar sannan ya fito a inda yabarta anan yasameta ya girgixa kai sannan yace mata tohm zan tafi gona sai na dawo koh dariyar farin ciki tayi tace nagode sosai sai kadawo Allah ya kiyaye hanya murmushi yayi yace Amin matata yafita achan kuwa wajen gonar haladu, ayuba zubairu duk sun xauna suna jiran suga ko zaixo idan kuwa bai xo bah wllh yau sai yasaki Aminatou ta tafi gidansu tun daga nesa suka hango bukar haladu yace kunga dayake yau taga damar yaxo gashi nan yaxo ay yaya haladu ka kyaleshi wllh mu sai mun karya asirin d tayi masa dan bazamu yarda bah ayuba yafada cikin bacin rai dan yanxu wata sabuwar kiyayyah yakeji a xuciyarsa ta Aminatou tana ratsashi zubairu dan takaici bai iya cewa komai bah bukar kuwa yana xuwa ya tsugunna.har kasa ya gaishesu duk dacewa yana tsananin jin zafin abinda sukaje suka yi musu jiya amman wannan dolene tunda sun girme mishi au ay nadauka da kaxo bazamu samu damar tsugunnawarka bah jiya mah naga korar karen d kaiyi mana saboda wannan tsohuwar najadur matar nan taka inji zubairu kuyi hakuri yaya ayubah ay ba sai kabamu hakuri bah nariga d nasan bah acikin hayyacinka kake bah kutashi muyi abinda yakawo mu haladu yace duk suka tashi suka shiga yin aikin shi kuwa bukar hankalinsa na gurin matarsa yabarta ita kadai gashi bawani samun sauki tayi bah haka yayi aykin a gurguje yayi musu sallama yatafi gida yana shiga gidan d sallama yaganta tana yin shara d sauri yakarasa yana kokarin karbar tsintsiya tace Haba dan allah kabarshi ay nakusa gamawa tafada tana tattare sharar taxuba a cikin bola kamanta yayi suka shiga daki sati biyu d zuwan su haladu gidan bukar suka kirashi yaxo gidan haladune yafara magana bukar tunda wannan abin na Aminatou kara cigaba yake toh yanxunnan basai anjima bah kasaketa wannan umarni nake baka bukar yakalli haladu yace yaya haladu bazan iya sakin Aminatou bah dan baa binda tayi min kuma ina son matata san da ban taba yiwa wata ya mace bah au mu kake fadawa kana son matarka bazaka iya sakin tabah zubairu yafada tare d mikewa ya nufo inda bukar yake gadan gadan ayuba ne yatareshi yana cewa kyaleshi zubairu bah laefinsa bahne asirine ya fada idonsa ya cicciko d kwallah ❤️❤️ KADDARATA😔✍🏽 Story nd written by nanah m sha'aban❤️✍🏽 Cigaban page 8-9 Cikin sauri bukar yatashi yay tafiyarsa gidansa Dan idan ya cigaba d ganin d kuma sauraran abinda suke cewa toh zaa iya batacciyah Kuma baya son hakan yafaru a tsakaninsa shi d Yan uwannasa akwana atashi cikin aminatou ya shiga watan haihuwa koh yau koh gobe farin ciki a gurin bukar baa cewa komai abangaran haladu kuwa bacin rai d takaicin bukar ya ki sakin matarsa aminatou yataru yayi masa yawa gashi tun daga ranar indai ya kira bukar baya xuwa saboda yasan dai akan maganar d baxata taba yiyuwa zaiyi masa bah dan haka ya shiga neman wata hanyar d adole sai bukar yarabu d aminatou ko yana so koba yaso saboda a cewarsa shi yadace ya auri aminatou tun kafin su fara soyayyah d bukar Amman rana tsaka yaje yana fada musu zai aureta wannan shine dalilin da yasa haladu yakeson bukar ya rabu d aminatou shi ya aureta awata ranar lahadi ranar d aminatou bazata taba mantata atarihin rayuwarta bah bashari mai shagon kusa d gidan iyayennata yaxo ya sanar musu d cewa an nemi anni d babbapha anrasa tun ranar jumma'a watau mahaifan aminatou tayi kuka har ta gaji bukar shima yayi kukan ya shiga bata hakuri dayi mata alkawarin zai nemosu duk inda sukaje ta kwantar d hankalinta haka yafita yana nemansu ciki d wajen kauyan amman babu su kuma babu labarinsu haka ya kamo hanya yadawo gida hankalinsa duk atashe yasan irin zafin d aminatou takeji dan shima mah yasan zafin rashin iyaye Amman gwanda shi yasan mutuwa sukayi Amman ita kuwa baa san nata iyayen ko suna raye koh sun mutu bah yana shiga gidan ta tareshi a bakin kofa tana tambayarsa angansu farar fuskarta duk tayi jajahur sabida kuka girgiza mata Kai yayi alamar aa rutsewa tayi d wani kuka koh shi kanshi bukar din kukan yake dan haka yakamata suka shiga daki yana rarrashinta domin a duniya baya son yaga kukan aminatou ko kadan tun ana neman su babbapha d anni har aka dawo aka dena dan har kauyukan dake kusa dasu bukar yaje akace gaskiya babu wasu sababbin fuskoki dasuka shigo Dan haka aminatou tadauki hakan amatsayin kaddararta Kuma tana rokan Allah yasa d rabon zasu gana anan gaba kafin ya dauki ranta a ranar wata alhamis aminatou ta tashi d matsanancin ciwon mara haka bukar ya tashi yaje ya kira innah makobciyarsu dayake suna mutunci d ita sosai tana xuwa tace ay haihuwace tafada masa abubuwan d zaije ya siyo yatafi da tafiyarsa ko minti biyar baiyi bah aminatou ta haifi katuwar yarta mai kama d ubanta sak yayi farin ciki d yadawo ya tare aminatou tahaihuwa innah ta yankewa yarinyar cibiya ta gyarata ta shiryata cikin wasu kayan jarirai d bukar yaje birni takanas ya shiyo su dayawa tamika mishi yar anan take yayi mata huduba yasa mata suna samira dan yana tsananin son sunan basuna kowa bane a danginsa haka mah dangin aminatou ❤️❤️KADDARATA😔✍🏼 Story and written by nanah m sha'aban❤️✍🏼 Page 10-11 Sai kuma taje ta gyara Aminatou sannan tafito zata tafi bukar yana ganin innah ya taso daga kan bancin da yake yana dauke da samira a hannunsa godiya ya shiga yi mata har sai d ta dakatar dashi haba bukar ay Aminatou tamkar diyata na dauketa dan haka karka karayi min godiya dan babu godiya a tsakaninmu yace toh inna hakane daga nan sukayi sallama d ita ta tafi gida a xuwan d yammah zata kuma dawowa dakin ya shiga ya zauna kusa d ita hannuwanta ya rike yana cewa aminata kinyi min abinda bazan taba mantawa bah nagode nagode sosai kadena min godiya kagodewa allah da yabamu ikon kasancewa d juna har muka kawo wannan lokacin d muka fara ganin 'ya'yanmu tafada tana yi masa murmushi ido yakafeta dashi d taga kallon yayi yawa ta katseshi d cewa kaje kagayawa su yaya haladu kar suji awani gurin mukara yin laifi jaririyar ya mika mata yana cewa ay basu damu dani bah babu bukatar kuma na dinga shishshge musu haba hakan bai kamata bah kasan dai cewa su din yan uwanka neh hmm to zanje in fada musu koh d yaje yafada musu babu wanda yace masa barka bare Allah yaraya haka yataso yataho cike d bakin cikin abinda su yaya haladun sukayi masa amman yayi alkawarin bazai kara takawa yaje gurinsu bah haka itama Aminatou zai hanata zuwa toh anyi suna wanda duk yawan cin makobtan su neh sukaxo sunan matan su yaya haladu babu wanda yaxo a cikinsu hakamah su talatuwa watan samira biyu mahaifinta bukar yashiga fama d matsanancin ciwon ciki nan d baya fita aminatou ta rude matuka d ganin irin yanayin d mijinnata yake a kullum maganarsa itace ta kula d samira tasata amakaranta kuma koda ya mutu karda tabari yarsa tayi kukan maraici a duk lokacin d yake fadar haka Aminatou takan fashewa d kuka yanxu idan bukar ya mutu ya zatayi d rayuwarta shi kadai yarage mata a duniya ga iyayanta bata san inda suke bah kwanan bukar goma yana cikin wannan rashin lapiyar allah yayi masa rasuwa awata ranar
Chapter 2 · 0% Book details