← Book details Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 38

Sashe 22

Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

💙🧡 KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah M Sha'aban✍🏼🧡
Wannan page din sadaukarwa neh ga fan's din littafin KADDARATA kuyi yadda kuke so Amman banda wadanda basa karantawa Kuma Ina son ayi min comments da typing bana son stickers yawan comments yawan typing🥰
Page 94-95
Saudat tunda Mai gadi yakawo takarda bahijjah mommy ta karba tabawa bahijja tare da cewa karanta muji meh wannan matsiyacin ya rubuta bahijja tayi dariya sosai da tagama karantawa a xuciyarta sannan tace mommy bari in karanta muku da karfi Ni fahid Ibrahim bukar nasaki saudat asanadiyar kamata da wani fasiki da nayi saki uku sai taje ta aureshi Dan shineh dai-dai aurenta Dan Ni bah mijin maxinaciya baceh takara fashewa da dariya mommy yau abinda kuka shuka shi kuka fara girba Kuma yanxu akafara idan Kuma tunanin biye-biyen bokayenku shineh yake sa ku Sami duk abinda kuke son wahala baku fara Shanta bah mah Kuma keh aunty saudat Daman nasha Miki iskanci bashi da Rana ta fada tare da shigewa dakinsu ita da ra'isa Daman su uku neh a dakin saudat kuwa suma tayi jikin mommy na rawa taje ta dauko ruwa a cikin fridge ta yayyafa mata a fuska ajiyar xuciya tasaki tana fadar mommy na shiga uku yanxu shikenan Yaya fahid ya sakeni bazan kara komawa gidansa bah cikin bakin ciki da takaici mommy tace wallahi saudat fahid bai isa yayi Mana haka bah ko zanyi yawo tsirara wallahi sai ya mayar dake zanbi duk wata hanya domin naga kin koma gidansa da zama murmushi tayi mommy kinyi alkawari eh nayi ita Kuma bahijjah zanci ubanta Bari Mai Basu goyan bayan suyi min rashin mutunci yadawo mommy ki kyalesu Daman nasan ai su kwata kwata basa sona tafada tana kuka kidena kuka ai ni Ina sonki Kuma Ina tare dake a kowane irin hali nasani mommah🥰
Sallama tayi tare da zaunawa a daya daga cikin kujerun dakin mommy ta kalleta lpy kuwa kike Samira yau naga ko makaranta bakije bah mommy wallahi mommy bani da lpy zazzabi nake Kuma ga amai da jirin da nake ji Ina jin xuciyata na tashi kuma subhanallillahi Kuma shineh kika xauna bakixo kin fada min bah tuntuni muje asibiti Kinga yanxu tashi ta dauko hijabinki muje asibiti ta tashi ta dauko hijabi ta fito falo Dan har mommy ita ta shirya ita take ji asibitin gidan suka je bayan anyi mata gwaje gwaje doctor Hashim yaxo da murnarsa Yana yiwa mommy albishir da Samira tana da ciki wata daya da sati uku wani irin ihu Samira tasaka tana fadar na shiga uku ya cuceni ya cuci rayuwata Allah ya isa tsakanina dakai mommy duk da ta gigice Amman bata Bari ta nunawa doctor din bah taja hannun Samira suka shiga gida xuciyarta cike da tambayoyi iri iri ya akayi Samira tabata tarbiyyar da sukayi mata har ta Bari wani yayi nasara akanta har yayi mata ciki gaskiya Samira tabata kunya Kuma tabata wayonta

💙🧡 KADDARATA😔✍🏼 story and written by Nanah M Sha'aban✍🏼💔
Page 94-95
Hajiya ummah ceh ta shigo dakin alhaji Dan yau taxo ayi ta takare ko sallama batayi masa bah tunda yadago yaga ita ceh Daman yasan bazai samu arxikin sallama daga gurinta bah Dan koda suna tare bata taba yi masa ladabi bah sai dai ta dinga yi masa magana cikin isa da ixxah tsayawa tayi akansa tana fadar alhaji naxo yau natuna maka baya irin yaudarar dakai min ka nuna min cewa Ni kadai ceh matarka Usman mah shi kadai neh Danka Ashe yaudarata kayi kana da wata matar harda 'ya'ya baka taba fada min bah sai da mukaxo kano ka kawoni gurinta kace itama matarka ceh duk da irin kishin da nake dashi na yarda zan xauna da ita Amman shineh yanxu xakayi min butulci kamanta irin taimakon da mahaifina yayi maka kana rana ya daukoka ya maidoka inuwa shineh yanxu xaka fara yi min rashin mutunci kayi min alkawari agaban waccen jahilar matar taka bazaka Kara cin komai nata bah kadena kwana a dakinta 'ya'yanta kabar mata su nata neh ita kadai Usman neh kawai Dan kah Kuma..........keh ummah you min shuru ban taba tunanin jahilcin naki har yakai haka bah yanxu bakiji kunya bah da kike Kiran mamyn fauxan jahila bah ai wannan sunan dake yadace Dan ita bazata taba xuwa gurina tayi min irin wadannan maganganun wadda suke nuna min alamar a gidanku baa Baki tarbiyyar yadda zaki dinga yiwa mijinki magana bah Kuma da kike cewa mahaifinki ya dakoni daga Rana ya maidoni inuwa inajin bai Baki labari bah da yabani dukiyarsa na fara juya masa na maidar masa da kudinsa sanadiyar ganowar danayi duk dukiyar daya tara haramce shi din Dan safarar miyagun kwayoyi neh wannan dukiyar danake juyawa gumi nah neh bawai da arxikin ubanki na neh ciyar daki bah kuka saka yanxu har takai da kayiwa babana kazafin dukiyarsa bah ta halac baceh Kinga fitar min a daki idan baso kike nayi miki tabon da bazaki manta bah kin para kaini karshe fita tayi Dan tasan halinsa tunda yace ta fita idan bata fita bah zai ita yi mata rashin mutunci da bazata taba mantawa bah duk Yan gidan sun taru a babban falo Dan mommy takira alhaji tasanar masa abinda doctor yace musu bayan an gwada Samira a ranar yadawo daga tafiyar da yayi danshi kwata kwata baya xama Yana kasuwarcinsa a Dubai inda yake siyar da gwala gwale shago guda neh dashi inda yadora Dan abokinsa safwan Dan yafuskanci yaro neh Mai Amana yakanje Dubai yaga yadda har kokin kasuwancin nasu yake tafi daga nan yawuce kasa Mai tsarki makkah Samira kuka take kawai Yaya daddy da Umar duk sun damu Dan da mommy tace Samira tana da ciki basu yadda bah sai da suka Kara dauko wani likitan Shima ya tabbatar musu cikinneh da ita cikin muryar rarrashi da kwantar da hankali daddy yafara magana Samira Ina so kidena wannan kukan ki fada Mana waya Miki ciki muryarta a sassarke ta fara magana shineh shineh abinda take cewa kenan sai Kuma tasaka kuka shineh wa? Mommy ta tambayeta Yaya fa..fa ..fahid cikin tsananin mamaki mommy ta maimaita sunan fahid Kuma eh shine lokacin da naje gidansa naduba ko lpy bai xo bah sai shineh....
Kuka tasaka Dan bazata iya fada musu wannan labarin bah idan tana tunanoshi wani irin bakin ciki take ji Yaya fahid dinneh ya shigo Dan kowa yakasa magana mommy takallesa cikin kallon mamaki Kai fahid Kai kayiwa Samira ciki mommy cikineh da ita ya tambaya cikin mamaki bansani bah Dan ubanka tabashi amsa cikin tsananin fushi mommy pha ita takawo kanta har gidan har dakina Dan haka Ni bani na mata dole bah Daman haka take so ai ace...wani Mari mommy tasakar masa a kuncinsa hagu da dama sai da daddy ya riketa sannan ta dena marinsa yanxu duk wulakancin da kakewa wannan yarinyar bai isheka bah kayi mata ciki kaxo kana cewa ita takai kanta tohm Ni nan rahma Ni na aiketa ta duba lpy bakaxo bah shineh....kuka tasaka daddy ya matso kusa da ita haba rahma kidena xubar masa da hawaye yanxu mu fuskanci abinda ke gabanmu bawai ki tsaya kina kuka bah Kai fahid yaxauna xaunawa yayi akasa inda daddy ya fara yi masa magana haba yarona meyasa kake yi min haka neh Ina matukar alfahari dakai amman yanxu kana so ka watsa min kasa a ido Samira ko babu aure a tsakaninku bai bakamata ace kana yi mata irin haka bah Dan kamar kanwa take a gurinka barantana da aurenka akanta yanxu wannan cikin da take dashi so kake idan ta haifeshi yaron ko yarinyar suga irin abinda kakewa mahaifiyarsu bazasu taba jin dadin ace mahaifinsu Yana yiwa mahaifiyarsu wulakanci da tozarci bah gashi nan mahaifiyarka tana xubar da hawayenka saboda kai....kaima so kake 'ya'yanka su sa kaxubar da hawaye???Aa daddy bana so to ka gaggauta bata hakuri mommy Dan Allah kiyi hakuri shikenan komai yahuce daddy Kuma cikin da Samira take dashi nawa neh bansan meyafaru Dani ranar bah saudat ceh sila Dan ita taxo ta bar badamin wani gari Ina kwance Dan lokacin bani da lpy nidai kawai bansan maiyafaru bah Amman Ni wallahi bansan Samira baceh shikenan wannan kuma matarka zakaiwa bayani kuma tunda Kai da kanka kace Dan Samira naka neh ai shikenan Alhamdulillah Daman haka muke so nakusan samun jika yafada Yana murmushi Yaya fahid kana nufi wannan shedaniyar ceh ta barbada maka garin magani hmmm ai gwanda da aka ceh samirar ceh Dan da ita ceh take da ciki zan ji bakin ciki daddy fada cike da farin cikin Umar kuwa cewa take yar kawu kiceh kawu ya kusan samun dan ita dai shuru tayi tabbas ta yarda da maganar da Yaya fahid yayi na saudat ceh ta barbada masa wani gari Dan da ta shigo falon taga saudat tafito ta nufi dakinta hannunta rike da wata leda baka tana kullewa Ashe ita sahun barawo ta taka😂💔
Chapter 22 · 0% Book details