← Book details Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 38

Sashe 10

Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ganin zaku iya fita daga cikin gidannan bayan irin hatsarin dayake dashi yar uwa zamu fita daga cikinsa koma tayayane ko so kike yabata mana rayuwa kuma daga karshe yamana mutuwar wulakanci Aa bana so nima na goyi bayanki amman yanxu menene mafita numfasawa samira tayi tare da cewa akwai mafita amman duk yadda zaa daga yau xuwa gobe zamu bar gidannan gingina kai sukayi gaba daya mommy ce kwance likitoci sunfi goma ne akanta suna takokarin cero rayuwarta umar d daddy sai kuka suke ❤️❤️ KADDARATA😔✍🏼 Story and written by Nanah M Sha'aban✍🏼❤️ Page 42-43 Umar yakira daddy yafada masa abinda kefaruwa da Kuma halin da Mommy take ciki a yanxu hankalinsa yatashi Dan haka a ranar ya shiga shirye shiryen tawowa abuja duk da bai gama abinda yakaishi bah abangaren fahid kuwa abokinsa yakirasa har gida Yana xuwa yaganshi da Aisha fuskokinsu duk a murtuke zama yayi Yana tunanin Mai yasamesu ko mutuwa akayi musu neh kallonsu sukayi gaba daya sannan daga bisani hamxa yatashi yakarasa har inda fahid din yake tambayar data girgizashi Kuma baiyi tsammanin tambayar daga gurinsa bah Ina Samira take abokina wannan wace iriyar tambayace Samira tana gida Mana ok tashi ka kaini gurinta akwai abinda nakeso na tambayeta shuru yayi sannan yace bata gida gaskiya toh tana Ina hamxa yakara gefo masa tambayar bansan inda take bah nima kamar yah zakace baka San inda take bah bayan kuna gida numfasawa yayi batare da ya damu da abinda zai fadawa abokinnasa bah yace nafitar da ita daga cikin rayuwarmu gaba daya nan yafada masa yadda yadauketa ya jefar da ita a wani daji dake cikin garin kano wani irin mari yaji hamxan yayi masa hagu da dama ita kuwa Aisha mutuwar zaune tayi fahid yadago Yana kallon abokinnasa yace yau ni hamxa ka mara akan waccen bakauyiyar yarinyar ba laifinka bane laifina neh danaxo gidanka Yana fadar haka yatashi yafita shikuwa hamxa ko a jikinsa Dan yau din haushi abokinsa yakeji matuka Samira ce zaune kusa da wannan matar Mai ciki da bata san ko wacece ita bah ko Kuma ya sunanta aunty gashi muna tare daku Amman babu Wanda nasan Koda sunansune barantana ya akayi aka kawoku nan numfasawa tayi dakyar tace dafarko dai ni sunana suraiya muna zaune a cikin garin kano unguwar tofa ni din marainiyace iyayena sun Dade da mutuwa mijina Yana shi yadauki dawainiyata Amman tunda ya auro wata matar nazama bora acikin gidan Banda wani yanci ana haka sai matarsa tanuna bazata iya zama Dani bah shine yayi min korar kare nafito daga gidansa babu inda zanje shine nahadu da wadannan mutanan Banda wasu yaran wannan cikin shi kadai neh daya daga cikin yammatan itama tafara gabatar dakanta sunana bilkisu mahaifina alhaji Usman lale Dan garin Paris neh akwai yayannina biyu Yaya fauzan sai Kuma Yaya usman sai ni sai autarmu nafisa ana ce mata feenart naxo hutu anan Wanda duk shekara idan an bada hutu mukan tahowa tare dasu mommyna Amman yanxu nikadai nataho su su mommynah sai karshen shekarar nan zasu xo a gidan kanwar daddyna nasauka aunty asabe Ashe aunty asabe sun hada Baki da wadannan mutanan akan zata badani zasu bata wasu kudadai masu tsoka wannan shine dalilin zuwana nan sauran yammatan suma suka gabatar dakansu itama Samira ta gabatar musu dakanta Amman kawai tace musu ita marainiyace itama kuma wani kanin babanta neh ya wurgar d ita a dajin Dan bata son kowa yasan irin rayuwar data Dan Dana tabakin ciki tana so ta fara sabuwar rayuwa ta manta da wadda tayi a baya bayan tagama Basu tace tohm yanxu dai dole mufara shirin guduwa daga gidannan tunda kunga gobe zaa kashe su lantana idan bamu gudu yau bah tohm shikenan rayuwarmu zata tagaiyara hakane bilkisu tafada chan Kuma Samira tahango wani window dake chan saman daki tayi murmushi tare dacewa nasamo mafita dasauri suraiya tace mecece mafitar ta window zamu fita tafada tare d nuna musu window dake saman dakin cikin saurin suraiya takara cewa Samira bayan takalli window tohm yanxu tafiya zakuyi kubarni tunda nasan ni bazan fita daga cikin window nan bah murmushi Samira tayi aa ay muma bazamu iya fita daga cikinsa bah tunda Dan karamine wani karfe takalla tare d nunasa tana cigaba dacewa Amman da wanchan karfen zamuyi amfani mubude window sosai tayadda zaki iya fita muma zamu iya murmushi suraiya tayi tana kara jin son Samira nakar shiga ranta haka suka bude window nan sosai sannan bayan baiwar sarki tashiga Samira tace Ina su lantana gasu nan sai da nabari duk nasa musu maganin bacci sun fara gyangyadi na fito dasu duk ta window suka fita ita kuwa suraiya da taimakon Samira tafita daga cikin window gudu suke daga ita sai suraiya Dan su bilkisu sun Kama gabansu durkushewa suraiya tayi Dan nakuda ce takamata Samira ta tsaya tana tambayarta meyafaru tace Samira inaji nakudace kawai ki tafi karsuxo su kasheki aa suraiya bazan taba barinki cikin wannan halin bah anan take Samira tafara taimakon suraiya Dan Daman wata kawarta zara tafada mata yadda ake karbar haihuwa suraiya tana haihuwa Samira takalli rezar dasu taho da ita sabuwa ce Dan haka ta yankewa jaririyar cibiya Samira ki kula min da yarinyata Dan nasan kekadai ce zaki iya kula da ita Kuma Ina rokonki Koda ce babanta yaxo ko danginsa karki Basu yarinyar nan ki dauketa tamkar yarki Danni nasan bazan rayu bah tana gama fadar haka tafara kalmar shada Samira sai kuka take tana fadar bazaki mutu bah suraiya Amman Ina suraiya tariga takoma ga mahaliccinta😢 ❤️❤️KADDARATA😔✍🏼 Story and written by Nanah m shaaban✍🏼❤️ Page 44-45 Kuka sosai samira take rike d jaririyar a hannunta tana fadar suraiya karki tafi kibarnzi plx bansan inda zan saka raina bah jitayi an doso inda suke babu shakka tasan yaran sarki barkodi ne dan haka ta tashi rike da jaririyar a hannunta tafara tafi tana wai jen suraiya sai da tayi nisa sosai sannans u yankan baya suka iso inda suraiya ta don lokacin har maganin baccin yasakesu sarki barkodi yace suje su nemo duk inda suka shiga idan kuma basu dawo dasu bah suka sake suka dawo sai ya kashesu koda sukaga gawar suraiya haka suka kacaccalata yankan baya yakalli mikakkiyar hanya tare dacewa wannan matar sai da ta haihu sannan ta mutu kuma bamuga alamar jariri ina da tabbacin basuyi nisa bahh kuma dole murarrabu wasu subi wannan mikakkiyar hanya wasu bi hagu sai kuma wasu subi dama haka suka rabu yankan baya da wasu mutane hudu suka bi mikakkiyar hanya wadda itace samira tabi wani gida tagani dan akwai bukatar ace ta gyara yarinyar sai tacigaba d tafiya da sallama tashiga gidan wata matashiyar budurwa taga akan kujerar karfe tana tsifa ta amsa mata tare d binta ba kallo mahaifiyar yarinyar ceh tafito daga dakinta bayan samira tagaisheta tacewa matar Dan allah mamah taimako nake nema so nake nagyara yarinyata inna takalleta sosai sam yarinyar batayi kama da mara gaskiya bah kuma d alama yarinyarta ce tunda ga jini nan duk yabata mata kaya inna takarbi jaririyar tayi mata wanka kayan yarinyarta dabata huce shekara daya bah tasakawa jiririyar innah tace kema yakamata kiyi wanka ko kya samu karfin jikinki samira bata musa bah dan Daman taga duk kayanta yabaci kuma gashi zata dinga yin sallah bayan tafito daga wanka budurwar nan tabata kayanta d hijabinta ta goya jaririyar nan sannan tayi musu godia sannan tanufi hanyar waje su yankan baya tahango su tsaya a dai dai gidan sai da ta tabbatar sun bar gidan tafito batare d tasan ina zata bah abbane zaune akan gadon da aka kwantar d mommy yau kwanan mommy biyu bata farfado daga doguwar sumar d tayi bah a yau neh akesa ran zata farfado dakin yacika da mutane har saudat da aunty dakuma su ahmad suna cikin dakin duk da cewa saudat d mahaifiyarta murna sukayi jin baa san inda yarinyar nan take bah sadia tace ita kuma rahma da take wani suma tama tashi dan bikinku d fahid babu tashi dan dai kawai yar uwa tace da sai nace ay gwara tamutu mah gaskiya mom aykin bokannan yayi sosai a kwana uku pha duk abinda mukeso yafaru duk wannan hirar dasuke ahmad najinsu dan lokacin yana tukosu zai kawosu gidan mommyn a xuciyarsa yana jin bakin cikin cewar wai mahaifiyarsa dakuma yayarsa neh suke shirya wannan makircin kuma suke yiwa aunty rahma fatan mutuwa ina mah ace wannan bah mahaifiyarsa bace aunty binta ce tashigo dan xuwanta kenan kallo daya tayiwa hajiya sadia d saudat ta watsar tare d jan wani tsani dan kwata kwata basa jitu dasu ko kadan duk da cewar mommy taji haushin abinda aunty binta tayi musu amman babu yadda ta iya dole tabarta amman taci alwashin sai takoya mata hankali ita kuwa saudat harararta tayi amman lokacin aunty binta tajuya baya dan haka bata kula bahh da bazasu wanye ta dadi bahhhh ❤️❤️KADDARATA😔✍🏼 Story and written by Nanah m shaaban✍🏼❤️ Page 46-47 Fahid ne zaune akan daya daga cikin kujerun dake zagaye a tafkeken falon duk garin yayi masa zafi tun lokacin dayaji rashin lpyr mahaifiyarsa mommy yusuf neh yakirashi yake fada masa tun ranar da su yaya umar d yaya daddy suka fada mata wata magana tafadi a bangare guda kuma yana tuna maganar d abba yafada masa bayan yakirashi sun gaisa yace wallahi fahid kabani mamaki wannan ba irin tarbiyyar damuka baka bane bamu koya maka cutar da wani bah barantana samira d take tamkar yar uwarka abokinka hamxa yafada min cewar kaje kayarda ita a wani daji a garin kano toh hakan yayi maka kyau yanxu duk irin nasihar da nazaunar dakai nayi maka ashe bakaji bahh ace kaine babbah kuma kaine mai irin wannan dabi'ar tohm yanxu idan su umar sukayi bazan taba ganin laifinsu bahh numfasawa yayi yana fadar yanxu yarinyar nan nafitar d ita daga rayuwarmu ashe wata babbar matsalar na ballowa kaina Allah sarki momcy bazan iya xuwa gareki bah har sai kin wuce sannan abokinsa hamxa neh yafado masa a rai wanda tunda yaje gidansa sukayi baran baran bai kara bari sun hadu bah ko da kuwa a asibiti tsaki yaja daya tuna irin wulakancin da yayi masa akan wannan yarinyar bedroom dinsa yashiga ya kwanta
Chapter 10 · 0% Book details