Sashe 9
Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read
Can tsakiyar kansa ya jiyo muryar Baba Talatu, ji ya yi tamkar mai fassarar da Ammi ta ambata ce Allah ya kawo masa.
Talatu couldnt believe cewa muryar Uwais ce ke yi mata magana, sabida yadda ta sirance ta zaftare, duk wani thickeness da huskness da ke cikinta ya tafi.
Baba Talatu idan aka ce mutum tuntuni yana da mata me ake nufi?
Tambayar ta bai wa Talatu dariya, ta ce, Ubangidana ana nufin yana da matar aure ko?
Abin da ban fahimta ba shi ne, an yi auren ko za a yi ne nan gaba?
Uwais ya hadiyi miyau kamar ya hadiyi kunama, ya ce, Baba Talatu wace ce FAHIMAH?
Talatu ta kai idonta da sauri ga hoton Fahimah da ke gefen gadon Ammi daidai inda ta ke saka kanta.
Ta ce, Uban masu gida, Fahimah ai daya muke da ita, kuma daya muka sani wata ce ban da abokiyar haihuwarka?
Ina nufin Fahimah ta gidan nan, autar Ammi.
A lokacin ne kwakwalwar Uwais ta soma daukan caji, ya ji wani irin bacin rai da bakin ciki sun zo sun tokare shi a kahon zuci.
Bai yi aune ba ya ji cikinsa na hautsinawa Talatu ba ta ankara ba sai ganin Uwais ta yi yana kelayo amai a tsakar dakin Ammi.
Amai sosai ya yi kamar zai amayar da yan hajinsa.
Talatu sai faman sannu ta ke masa ya tashi yana rangaji ya bar dakin ba tare da ya karbi ruwan da ta kawo masa daga firji tana fadin ya wanke fuskarsa ya kurkure baki ba, zai ji dan dama-dama.
Ta gaban Ammi ya wuce fuuu tana zaune a falo, ko kallon fuskarta bai yi ba ya wuce, abinda bai taba yi ba.
Ammi ta kyabe baki ta dauke kanta daga bayan sa.
Ba don aikinsa ba yau zai bar garin.
Tafiyar da sai Ammi ta janye mummunan furucinta sannan ya dawo.
To Banki ba su san excuse ba.
Yau yayi nadamar zabar aikin banki matsayin career din sa.
Amma ya kudire a ransa cewa Ammi ta samu matsala irin ta cutar dimentia wadda tsofaffi ke fama da ita.
Zai yi kokari ya nema mata magani.
Tun daga ranar gidan ya koma wani iri ba dadi, kowa ba ya cikin walwala.
Ammi ranta a mugun bace yake da maganar auren da Uwais ya rakito, Fahimah ciwon so ya gama kassara ta, ya karar da kuzarinta, ya tafi da duk wani karsashi da ta ke da shi a cikin gidan ko falo ta daina fitowa.
Yayin da Uwais yana can yana neman mafita, ga balain da ke shirin tunkaro shi yo bala'i mana!
Rashin Amrah ai catastroph ne, haka zancen da Ammi ta yi (abin amai), shi ma babban balaI ne a gare shi.
Don in ya tabbata Ammi ba ta da dimentia kuma tana nufin abin da ta ke fadi ne har zuciyarta wace irin mafita zai nema wa kansa ba tare da ya fada fushin Ubangiji ba?
Ammi ba uwa ba ce kadai, Uba ce, dangi ce, abokiya ce komai ce a gare shi, amma ba zai iya yi mata wannan uzurin ba, ko da duk duniya za ta taru a kanshi.
Zai iya hakura da Amrah in abinda auren ta zai janyo masa kenan, amma auren Fahimah sai dai ayi da gawar sa.
******
Walwalar gidan duk sai ta ragu, kowa yana dakinsa kullum, Talatu ce kadai ke shige da fice don tsaftace muhalli, abinci sun daina ci tare a dining yadda suka saba, sai dai ta kai wa kowa dakinsa, ta kuma lura ko ta kai din ba wani cin kirki suke masa ba kamar da, musamman Uwais ko tabawa ba ya yi, in ya fice tun bakwai na safe sai bakwai na magriba ko a ofis coffee kawai yake sha wanda yake hadawa da kansa.
Amrah ta koma Malaysia tuntuni, kullum suka yi waya tana jin muryar Uwais ba yadda ta saba jinta ba, ko da ta tambayi dalili sai ya ce mata,
Aiki ne yake masa yawa.
Yanzu ya rage zuwa gidan Jabir tun bayan komawar Amrah, tsiya iri-iri Jabir ya masa amma sai dai kawai ya yi murmushi ya ce, To me zan zo in yi maka, kai ma ka san ba don kai nake zuwa ba.
Ko kusa bai gaya masa yana da matsala da Amminsa a kan maganar Amrah ba.
Yau yana ofis kawai wani tunani ya fado masa, Kawu Shuraim.
A kasar Sudan, shi ya fado masa a rai, Yayan Ammi da suke uwa daya uba daya, kuma wanda Ammi ba ta iya tsallake maganarsa.
Wata ajiyar zuciya Uwais ya saki, ya mika hannu ya dauko wayarsa a kan tebir din gabansa ya lalubo lambar Kawun nasa.
Uwais na nan da larabci zam a bakinsa, don Ammi tana yi masa sosai tun yana yaro.
Sannan akwai aminci sosai tsakaninsa da Kawun nasa don yana yawan yi masa alkhairi ba tare da sanin Ammi bama.
Shi kadai ya rage babba a family din su Ammi, ya manyanta, ragowar duk kannenta ne maza da mata.
Suka gaisa sosai da Kawun, shi da kansa ya tsinkayi damuwa a muryar Uwais, ya ce,
Uwais gaya min ko me ke damunka, insha Allahu za'a samu mafita.
Uwais ya runtse idonsa ya ce, Kawu, matar aure na samu wadda nake so, daidai da ra'ayi na, mai duk qualities din da nake bukata a matar aurena, ina sonta sosai, kuma ta amince min in turo magabatana yanzu haka.
Da na zo na gaya wa Ammi, sai ta kawo wani batu wanda har yau na kasa daidaita maanarsa a kwakwalwata.
Kawu, na dai fahimci wai ta yi min mata ne already, imagine Kawu da wannan tsintacciyar magen da ta dauko a gidan marayu.
Yaa Subhanallah!
In ji kawu Shuraim cikin kakabi.
Ya ce, Ita Safiyyar da hankalinta za ta aura maka wannan bakar yar mara asali?
Kamar matan Sudan da na Najeriya sun kare?
Uwais ji ya yi kamar Kawunsa ya yayyafa masa ruwa a kan wutar da ke tiriri a kirjinsa, ya ce, Kawu na saya maka tiket, don Allah ka zo a yi ta ta kare.
Kai kadai ne last hope dina Kawu, don Allah ka taimaka min ka gaya wa Ammi ta aura min mata hudu a rana daya in dai da Amrah a ciki, amma ta cire wannan yarinyar a cikin su zan iya hadiyar zuciya na mutu.
Da sauri Kawu Shuraim ya ce, Zan zo cikin satin nan insha Allahu, abin bai kai haka ba, ka kwantar da hankalinka.
Ammi ba ta san me suke kullawa shi da Kawunsa ba.
Yanzu ta fara maida walwalarta tana harkokinta cikin gida, amma ta cire Uwais daga shirginta, musamman da ta lura shi ma ya dauki gaba da ita.
Damuwarta yanzu a kan Fahima ne, wadda ke ta faman ramewa babu gaira babu dalili, kuma ba ta son cin abinci.
Ga jarrabawarsu ta barin sakandire na tunkaro su.
Wajen karfe goma na dare, Ammi har ta yi barci ta farka, so ta ke ta binciki halin da Fahima ke ciki a daren nan.
Ta sauko daga gadon ta a hankali ta daura laffayarta kamar wadda za ta unguwa, sannan ta nufi dakin Fahimah.
Tun daga bakin kofa ta ke jiyo shesshekar kukan Fahimah ta karasa da sauri ta murda kofar ta shiga.
Ta kifa kai a kan filo ta dunkule jikinta sai kuka ta ke.
Sai jin muryar Ammi ta yi a kanta.
Fahimah!
Yau sai kin gaya min abin da yake damunki.
Wani ke yi miki abin da ba ki so cikin gidan nan ko kuwa kin gaji da zama da ni ne?
Fahimah ta dago a hankali cikin tsananin faduwar gaba, ba ta taba tsammanin Ammi a wannan lokacin ba, she will never shed tears a gaban Ammi, don haka tashin hankalinta a yanzu shi ne ganin kukanta da Ammi ta yi fiye da damuwar da ta ke ciki.
Hajiya Safeeyyah ta zauna a gefen gadon ta ce, Fahima ta ba ki da wanda ya fi ni duk fadin duniyar nan, don haka daure ki gaya min ko mene ne damuwarki, na yi miki alkawarin sai inda karfina ya kare wajen sama miki farin ciki, don ke amana ce a hannuna fiye da wannan yaron, kuma amanar ce tsakanina da ke, ki gaya min ko mene ne Fahimah ta.
Fahima ta riga ta kudire a zuciyarta sai dai ciwon son Uwais ya yi ajalinta, amma ba za ta taba furta hakan ga kowa ba balle mahaifiya a gare shi.
Idan ta tursasa shi ya aure ta to ta kai shi ina?
Mutum gashinan kamar malaikan daukar rai wane dadi mace za ta ji a aurensa?
Macen ma wadda ya fi tsana fiye da kowa a duniya?
Don haka ta soma tunanin abin da za ta fada wa Ammi ba tare da ta sanya mata kokonto ba.
Abubuwa da yawa na damunta, not only UWAIS SHAGARI.
Tana son sanin asalinta, tana son sanin su waye suka yi sanadin zuwanta duniya.
Ammi ba ta son tambayar nan ko kankani, amma yau dole da ita za ta bi ta kare kanta da mutuncinta a idanun Ammi Safiyyah.
Ammi, babu ciwo mafi muni ga dan Adam irin a ce ba ya da asali, bai san su waye suka haife shi ba, bai san shi dan sunnah ne ko shege ba.
Ammi ko ba ki fada ba na dade da ganewa, orphanage da muke zuwa shi ne gidanmu, shi ne asali da tushe na, a can ki ka dauko ni.
Ta karasa cikin wani irin kuka da ya keta har cikin zuciyar Hajiya Safiyyah.
A yau ita kanta Ammi ta rasa da kalaman da za ta lallashi Fahimah, ta fahimci irin ciwon da ta ke ji a ranta, kuma ba ta isa ta warkar mata da shi ba.
Kama ta ta yi ta rungume a jikinta ta ce, Fahima, in kin yarda ni ma UWA ce, sannan kokarina ya kai na kowacce UWA, to ki dubi Allah ki cire wannan damuwar daga ranki.
Im your mother, father and Uwais is your brother.
Ki sani babu wanda rayuwa ta ke cikakka a gare shi, babu kuma wanda Ubangiji ba ya jarraba in one way or the other.