← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 35

Sashe 29

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amrah na can tana sharar barci ta yi daidai a kan gado ta baro Uwais kamar marayan da ya rasa uwa don ta roke shi kada ya zo inda ta ke in ba so yake ta amayar da
an hanjinta ba.

Uwais ya mike tsam yana daure igiyar pajamas din shi cikin ransa yake fadin,
na me?

Ni ba aminin gwauro ba?"
Dakin Fahimah ya nufa bayan ya leka Amrah ya tabbatar ta yi nisa a barcinta.

Kamar Fahimah ta san haka za ta faru don ta gama gane Uwaisun nasu cikin dan lokaci kalilan, kunya bata ishe shi ba a wannan fannin kam, zai iya janyo mata abin kunya wajen wadda ta dauke ta 'yar uwa, don haka tun sanda zata kwanta ta rufe kofarta ta ciki da key ta kuma barshi a jiki ta yadda ko ya sa nasa ba zai shiga ba.

Ya murda kofar sai ya ji ta gam-gam, wato ya ji ta a rufe, sai ya soma kiranta a matukar tausashe.
ah-himah, bude min kofar mana, ni ne Uwais
Fahimah da ke bisa darduma tana sallolin nafilah don gusar da birbishin kishin da ya cika zuciyarta ta yi sallama, sannan ta matsa jikin kofar cikin damuwa ta ce,
ani abu ka ke so Ya Uwais?
i bude na ce, ko ma me ye sai ki ji
askiya ba zan bude ba Ya Uwais".

Ransa ba karamin baci ya yi ba, kuma yana tsoron ya daga murya Amrah ta tashi don haka ya sassauta murya ya ce,
lease Fahhimah
begging you in the name of Allah
?...

Muryar Uwais dake raurawa har cikin tsokar zuciyarta, yadda muryar ke raurawa haka zuciyar ta ke raurawa, weakness na wanda kake so ba karamin rauni bane a gareka, amma ta gwammace ta tsaya a kan gaskiya da adalci, in ita aka yi wa haka ya ya za ta ji?

Amrah ba ta san da komai a tsakaninsu ba, sai kokarin kyautata mata ta ke da zuciyarta daya.

Ta dauketa kamar kanwar Uwais da ta kawo mata ziyara.

Amma sai ta saka mata da dauke Uwais a cikin dakin ta?
aya Uwais ka yi hakuri ba fa zan bude ba.

Don ban ga abin da ka ke so a nan ba
Muryarsa wani iri don tsananin bacin rai, ya ce,
ah-himah...., amma saboda takaici sai ya kasa karasawa, ya juya ya bar wurin.

Dakin Amrah ya koma yana fadin yau sai dai turarensa ya sumar da Amrah in ma suman za ta yi.

Fahimah ba ta san ya suka kare shi da matarsa ba, da asubah Amrah ta hau buga mata kofa, da Fahimah ta ji muryarta sai ta bude, Amrah ta fado dakin tana ajiyar zuciya, at last she escaped!

Smell din da bata so.

Sannan ta zauna a gefen gadon da Fahimah ta tashi, ta ce,
an kwanta a nan don Allah, bana son turaren Habiby, shi kuma ya ki fahimtata ya nisance ni ba da gangan nake yi ba
Ta yi ajiyar zuciya abin tausayi, sannan ta dubi Fahimah cikin rauni "kin huta da ba'a yi miki aure ba Fahhimah, aure takura ne, nauyi ne, jidali ne wallahi ina da na sanin yinsa
Fahimah ta ce,
ul!

Amrah ki daina fadin haka, domin aure umarnin Ubangiji ne kuma sunnar Annabi SAW ne.

Ya kuma ce wanda ba ya son sunna ta, to ba ya tare da ni
Amrah ta ce,
stagfirullah
? wa'a tubu ilaih, amma duk bayanin da zan miki bazaki gane ba tunda baki da aure, my husband mai yawan takurawa ne, yayin da ni nake tsaa-tsaki, sannan ina fama da kaina, amma ya kasa daga mun kafa ya bar ni in sarara ko kadan.

Yanzu kam na yarda gara ya kara aure, Fah-himah I so much like you, in da aure tsakanin ki da Habiby don Allah ki taimake ni ki aure shi... tafiyarmu ni da shi ba za ta yi tsayi ba in aka cigaba a haka
?...don bani da isashshen lokacin sa, yanzu haka na baro komai dake gabana na taho tun daga Malaysia don in ba shi lokacina amma na kasa faranta masa da komai, tunda na zo lafiyata ta ki daidaito.

Shi kuma ya kasa daga min kafa, jiya fada muka yi baram-baram ko barcin kirki yau ban iya na yi ba
Fahimah ta rungumo Amrah a jikinta cikin lallashi, ta ce,
i yi hakuri Amrah, marriage is not a bed of roses kuma duk soyayya sai ana samun misunderstandings
? amma Yaya Uwais is a nice person, duk da ba ni da experience a kan aure na san abubuwan da ki ke fama da su lalurorin karamin ciki ne kawai, da zarar kin samu lafiya ko kusa bazaki so kowa ya rabi Uwaisun ki ba, balle kiyiwa kan ki fatan ya kara aure, kuma insha Allah zai wuce, da zarar cikinki ya yi kwari
Ta yi shiru sannan cikin murmushi, ta ce.
mrah ki ke so ko in ce ki ke fatan wata ta auri Uwais?

Ba kya tsoron ta kwace miki shi ne?

Ki bar wannan tunanin wahalar ovulation ke damunki, da kin haihu ko kuda ba za ki so ya gifta a tsakaninku ba
Amrah dai ba ta ce komai ba, amma ta ji dadin maganganun Fahimah, ba ta san sanda ta fada ba tsabar bata cikin normal hayyacin ta, kuma tana bukatar taimako daga 'yar uwarta mace koda da shawarar fatar baki ne.

Tace.

"Fah-himah I just like you, and i love your simplicity ".

Da sauri fahimah ta girgiza kai tana jin kamar ta bude baki ta gaya mata gaskiya, don ba ta saba rashin gaskiya a rayuwarta ba sam sai yau.

Yau din ma don kada ta shiga hurumin da ba nata bane.

Kamar Uwais ya san me ta ke shirin yi sai kawai ya bude kofar ya shigo dakin babu zaton su.

Ya dau wankansa as usual ya yi shirin ofis cikin bakaken suit, ya dube su ya girgiza kai.
aga ganin wannan zaman naku gulmata ake, kin bar ni zan fita ban ci komai ba
?.

Ya fada yana kallon Amrah directly cikin idanunta.

Ji ya yi ya kara sonta duk flaws dinta, tunda tana son Fahimar sa.

Fahimah sai ta zame jiki ta bar musu dakin, kofar da ta ke da tabbacin kitchen ce can ta nufa.

A gurguje ta dama wa Uwais custard ta zuba madara (peak) ta ruwa gwangwani daya, ta soya plaintain da sauri ta zo ta aje masa a dining.

Daidai lokacin suka fito daga dakin nata shi da Amrah, ya ja kujera ya zauna ya soma tsiyaya vanilla custard din a kofin mug na tangaran.

Fahimah ba ta tsaya tare da su ba, ta koma kitchen din don ta sama wa Amrah wani abu mai dan gishiri da maggi kuma mai yaji da za ta iya ci kamar yadda ta gaya mata cewa abu mai yaji da maggi kawai taje iya ci..

Farfesun tarwada ta yi mata, Amrah ta ce ta saka tarugu sosai.

Haka ta yi ta shan romon da cokali tana gumi tana fyace hanci.

Da rana girki na musamman Fahimah ta yi wa Uwais tuwon semo miyan danyen kubewa da yaji zallar tsokar kaza, ta cire duka kasusuwan ta dagargaza tsokar cikin miyar.

Amrah ta ce ba za ta ci komai ba wanda Fahimah ta dafa don bata marmarin tuwo, sai spicy chicken take so, ta kira Uwais tace idan ya dawo aiki ya tsaya ya taho mata da ita daga Chicken Republic.

Amma Fahimah ba ta kyale ta haka ba, sai da ta yi mata dan wake da manja da yaji, ai kuwa Amrah ta yi ta zuqulqula tana shi wa Fahimah albarka.

Ita kuma ta zage ta gyare gidan ciki da bai dinsa, dakin Uwais ne kawai ba ta shiga ba.

Da ya dawo ya kawo wa Amrah kazar.

Kallo daya ta yi mata ta ji ta ginshe ta.

Ta ce,
abiby, na ci dan waken Fah-himah na koshi kuma ku nemi mai cin wannan
Kwanan Fahimah bakwai a gidan gaba daya rayuwar gidan ta yi armashi.

Amrah na samun hutu yadda ya kamata Fahimah na kula da cinta da shanta, tsaftar gidanta har ma da walwalarta.

Wani irin sabo wanda ya fi kama da na
an uwantaka ya shiga tsakaninsu.

Uwais ya gaya mata Ammi ke rikonta ba
ar aiki ba ce kamar yadda ya gaya mata a baya, amma ko da wasa bai fada mata Fahimah daga orphanage ta zo hannun Ammi ba.

A ganinsa wannan sirrin Fahimah ne wanda daga shi sai Ammi yakamata su sani, don sama wa Fahimah cikakkiyar walwala da sukuni a cikin mutane
an uwanta.

Uwais ya yi juriya kwarai, don kuwa bai kara attempting zuwa dakin Fahimah cikin dare ba, ya yarda da hujjarta na ce wa Amrah deserves respect, a gaban idonta ko a bayan idonta sabida kyakkyawar zuciyarta da kyautatawar ta..

Sati biyu na cika Fahimah ta soma shirya kayanta don komawa gida, Ammi ta yi waya gobe insha Allah za ta sauka a Kano.

Amrah har da hawayenta da Fahimah za ta tafi, ta hada mata cosmetics designer din AVON set guda.

Ita da Uwais da Fahiman suka tafi filin jirgi dauko Ammi.

Suna ta hira ita da Amrah, Amrah na fadi mata
cant' express my kind gratitude, for your being with me, for your kind assistance Fahhimah, ina ma Ammi za ta bar min ke mu ci gaba da zaman mu tare?

Uwais ya yi murmushi yana tukin mota zuciyarsa ta masa dadi, ya juya ya ce da Amrah da ke gefensa,
ta kuma ta yi ta zama kenan ba za ta je gidan nata mijin ba?

Amrah cikin zolaya ta ce,
i don ta ki ne, amma na ce mijin ma ta zo mu aura tare
Uwais daga jin haka bai iya kara cewa komai ba, ko kwakkwaran motsi bai kara ba, don mamakin Amrah ya gama kashe shi.

To amma ya ya za ta ji idan ta ji cewa all these while Fahimah zaman matarsa ta ke yi kamar ta?

He is just fooling her?

Ko ya ce they are just fooling her?

Daidai lokacin da suka shiga filin jirgin Malam Aminu Kano, tuni su Ammi sun sauka, a reception suka hango ta.
Chapter 29 · 0% Book details