← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 35

Sashe 23

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga bakin kofa ta tsaya, muryarta ta dushe don kuka har ba ta fita sosai, ta ce.
a zo ka maida ni wurin su Ammi
Ya daga rinannun idanunsa ya dube ta, ta kauda kai.

Jin wani abu kamar kibiya ya fito daga idonsa ya shiga nata.

Uwais ya taso daga kwanciyar gaba-gadi ya tako ya tsaya a gabanta har tana iya jin hucin sassanyar numfashinsa.
a ni na kawo ki?

Ko ni nace ki biyo ni?

Ban ce ki bi Mahdi ku koma ba kika ki?

Ban gaya miki zuwanki baya amfana min komai ba?

Ya tambaya a jere, da wata murya tamkar zai doke ta.

Sannan ya sa hannu ya dago habarta.
ou can tell the whole world kin gan ni ina abin da ki ka ga ina yi, amma in mahaifiyata ta ji, na rantse sai na sauya miki kamanni, yadda in na sake ki ba wanda zai yarda ya kwashe ki, don ba za ki ganu ba wallahi Fahhimah
Fahimah ba ta san sanda ta buge hannun Uwais daga habarta ba, duk wani shayinsa da ta ke ji ada, ai yanzu babu shi, ya gama bata rawarsa da tsalle a idanunta, ta ce,
o ka sakenin mana, sai me in ka sake ni?

Sai aka ce bazan rayu ba ko a gidan mu na marayu ne?

Menene a auren naka banda bakin-ciki?

An gaya maka ko ba ka sake ni ba akwai sauran zama a tsakanin mu?

Allah ya tsare ni, wallahi ko Ammi za ta min baki yaya Uwais na gama auren ka.

I never know this is your habit, Amrahn ma na tabbata bata sani ba wallahi da bazata aure ka ba
Ta saki kukan da ya taho tun daga kololuwar zuciyar ta.

Ita kuma kalolin kaddararta ke nan?

Daga wannan sai waccan?

Uwais da ta bai wa dukkan so da kauna ashe haka yake?

Sabon Allah kiri-kiri da aurensa da komai?

So ta ke ta gane ko matsayinsa da soyayyarsa sun ragu a zuciyarta a dalilin hakan?

Ba raguwa kadai ba, komai ya zagwanye hatta shakkarsa da ta ke ji ta kau (istimna'i yana daukewa mai yin sa kwarjini, yana sabbaba illoli ga lafiya da yawa sannan haramun ne a addinance).

Uwais ya yarfa hannuwa ya ce,
ell, ki gaya ma Ammi ga abin da ki ka ga ina yi, ni ma in gaya mata cewa kin yi rantsuwa da ki hada jiki da ni gara kin mutu.

Ni ma na mutu kowa ya huta....

A dalilin ba ni da mafita ne kuma na fita a tunanina, na nema wa kaina relief, amma ko ki yarda ko kada ki yarda ban taba yi ba sai jiyan, kuma inda wanda ya sanya ni a wannan halin to ba wata ba ce, ke ce Fahhimah
Yana gama fadin hakan ya yi dialling number din Mahdi.

Mahdi ya ga kira da sassafiyar Allah, sai ya dauka ba lafiya ba.

Yana dagawa ya ce,
lease Mahdi come and take me to airport, and take this girl to Ammi, ka gaya mata zan kira ta a waya, wani muhimmin uzuri ya taso min a ofis
Mahdi ya amsa da,
o ga shi nan
Har zuwa wannan lokacin Fahimah na tsaye a inda Uwais ya barta kamar mutum-mutuma, tana mai tauna kalaman Uwais a bisa ma
uni na hankali da tunaninta.

Ba'a fi minti goma ba da kiran wayar Mahdi ya kira shi, cewa yana reception sannan ya gaya wa Ammi batun tafiyarsa ta ce, lallai ya biya da su wajenta kafin ya tafi.

Cikin takaici Uwais yake dubansa,
e ya sa ka yi min wannan karambanin Mahdi?

Mahdi ya ce,
a ya ya ba zan yi ba?

Ka zo da niyyar yin kwana uku, washegari ka ce za ka tafi, don kawai matarka ta bata maka rai, sai in kyale ka ka bar kasar ba tare da sanin Ammi ba?

Don ta ce da hadin bakina ko?

Tsaki ya yi cikin haushin Mahdi, sannan ya wuce gaba, Fahima ba ta yi wata-wata ba, ta rufa masa baya harda gudu-gudunta.

Fatanta kawai ta bude ido ta ganta gaban Ammi ba tare da Yaya Uwais ba.

Ta tsane shi yanzu kam ba ta ko son ganinsa.

Allah wadaran soyayyar.

Ammi ta tsura musu ido suna sunkuye a gabanta, kowanne fuska ba walwala, da alama Fahimah kuka ta ci ta koshi.

Sai ta ji duk farin cikin da ta ke ciki ya koma.

Ta dubi Uwais da idanun rahma, ta ce.
e ya faru za ka tafi unexpected kuma ba tare da Fahimah ba, ka san ba zai yiwu ta yi har sati biyu a nan ba saboda makaranta, kuma na yi zaton kwana uku aka ba ka?

Uwais ya c
mmi ba abin da ya faru, aiki ne kawai ya taso min
Ta dubi Fahima,
e ma ba za ki gaya min ba?

Kukan me ki ke yi?

In laifi ya yi miki ki gaya min kin san ba zan kyale shi ba
Da kyar Fahimah ta motsa bakinta, ta ce,
a abin da ya yi min Ammi
Tana kallon yadda Uwais ya saki wata boyayyar ajiyar zuciya.

Haushi ya kama Ammi, ta ce,
o tunda haka ne, ku yi ta rikon bacin ranku a ranku, amma ba inda za ku je sai kun yi kwanakin da ku ka zo da niyyar yi, kun zaga dangi kowa ya ganku.

Uwais ina gaya maka ina kara gaya maka Fahimah amanar Allah ce a hannunmu in ka cutar da ita Allah ba zai barka ba
Uwais bai san sanda ya katse ta ba,
n kuma ita ta ke cutar da ni fa?

Ita sai Allah ya barta?

Ammi na yi kokari na tausa zuciyata na karbi amanarki ko da bana jin sonta a raina, amma ita tana neman halakar da ni, don haka Ammi ki daina jin tausayin Fah-himah don kuwa ba abun tausayi ba ce, muguwa ce
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Ammi ta kusa yin dariya don tuni ta je gano ga matsalar tasu.

Ta dade da sanin wannan cewa; Uwais irin mahaifinsa ne, in haka ne kuwa ba za ta sha wahalar sanya Fahimah a zuciyarsa ba, wuyarta mu'amalar aure ya gitta a tsakaninsu.

Ammi ta gyara zama tana murmushi, ta ce,
n dai ka hakura da tafiyar a yau, to ka je ku ci gaba da karbar gaisuwa.

Ni kuma zan yi magana da Fahimah
Ya tashi ya fice ba tare da ya ce komai ba, sai ma kafar Fahimah da ya kusa takewa, Ammi ta bi shi da kallo tana ajiyar zuciya.

Uwais na bada baya, Ammi ta ce.
o ke Fahimah, an gaya miki ana hana miji wannan ne a zauna lafiya?

It's the greatest weakness of men, sannan hanya mafi sauki ta shigewa sukuf zuciyarsu.

Ni dai a matsayin uwa nake miki magana ba suruka ba.

Don ni ke na haifa ba Uwais ba
Idanun Fahimah suka cicciko da hawaye, amma ga mamakinta ji ta yi ko za a dora mata wuka a makoshi ba za ta iya fada wa Ammi ko wani daban abin da ta kama Uwais yana yi ba, which means har yanzu da dan sauran burbushin son, no matter laifukansa a rayuwa.

Kuma ai yace ya tuba, bai taba yi ba, na jiyan ma itace sila.

Ita ta ja, tunda ta hana shi abinda Allah ya halatta a gare shi.

Ba kuma kowanne dan adam ne mai iya tsallake hudubar shaidan a irin wadannan lokutan ba.

Maimakon tace komai, sai ta saki kukan da ke cin ranta.

Ta kifa kai a cinyoyin Ammi.

Ammi ta janyo ta jikinta ta rungume ta.
mmi he keeps on telling me cewa ba ya sona, ta ya ya zan iya sakin jiki da shi?

Kalmar tana kona min rai Ammi yadda ba kya zato
Ammi na shafa bayanta cikin lallashi, ta ce,
et him say it... let him say it loudly to the whole world ba ke kadai ba, sai ya gama fada zai kore zafin kiyayyar daga zuciyar sa.

Kada ki damu da wannan, tunda har mun samu cewa yana son physical relationship (gamayyar jiki) ya shiga tsakanin ku.

Wannan ma ba ya zuwa sai da so Fahimah, ki kyale shi ya yi ta fada, watarana da kansa zai janyeta da gwiwoyi a kasa, ko mumbari zai hau yana fadi ba ya son naki ya je ya yi, amma ki barshi ya dabbaqa sunnarsa, sauran ki bar wa Allah ki kuma zuba ido ki sha kallo.

Allah fa na sonki da Uwais, shi ya sa ya kautar da hankalin matarsa daga kansa ta nisance shi,da tana nan bazamu taba samun kansa haka ba, don haka Fahimah yanzu lokacinki ne kada ki yi wasa da damarki don sau daya ta ke zuwa a rayuwa kin ji ko?

Fahimah ta gyada kai.

Ammi ta ce,
o tashi mu je mu karya kumallo, na tabbata ba ku ci komai ba ku ka fito.

Shi ma zan sa a kai masa nasa yanzu
Ba su kara haduwa da Uwais ba sai da daddare, ya shigo a gajiye ya yi wa Ammi sallama cewa zai wuce masauki.

Ko da abin da ta ke so?

Ammi ta yi murmushi ta ce,
unda ka fasa tafiyar ka ji maganata na gode Uwais, Fahimah tashi ku je, Allah ya ba mu alkhairi
Fahimah ta yi kicin-kicin da fuska daidai lokacin da Uwais ya dago suka hada ido, harara ya sakar mata, ba ta bata lokaci ba ta rama, sannan ta mike don Ammi ta sake maimaita umarninta.

Suna tafe a hanya Mahdi ke tuki ba wanda ya kula dan uwansa, sai wakokin (Sudanese singers) da ke tashi a cikin motar cikin harshen larabci ta shahararren mawaki Mahmoud Abdul
ziz.

Suna isowa Fundaq Mahdi ya ajiye su ya juya, Uwais sai da ya tsaya a reception ya karbi mukullin sannan suka haura ta lifter zuwa dakinsu.

Tunda suka shiga dakin bai kula Fahimah ba, ita ma ta kama kanta ba ta shiga sha
ninsa ba, amma ta ki barin dakin da yake a kan dalilin da bata sani ba.

Mafi rinjaye na zuciyarta ya fi raja
a kan ba za ta kara nesanta kanta da shi ba, ko da kuwa ba za su hada shimfida ba.

"Yaa Allah!
Chapter 23 · 0% Book details