Sashe 16
Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babban tashin hankalinsa a kwanakin nan shi ne in ya tuna Amrah tafiya za ta yi ta barshi shi kadai a gidansu, aikinsa kuma ba irin na yawo ba ne duk lokacin da aka ga dama.
Ya soma da ya sanin alkawarinsa na barin Amrah ta ci gaba da karatu a jamiar Limkokwing, sai dai ya san bai isa ba, ya yi kadan, yayi tsararo ya daga wannan alkawarin daga muhallinsa.
Amrah ta sangarta shi da abubuwa da yawa a sati uku kacal, ga iya girki, ga tsafta ga shagwaba sannan uwa-uba ta iya bi da shi a shimfida.
Duk da karancin shekarunta.
Suna tafe a kan hanyarsu ta zuwa gida daga airport tsakanin shi da Ammi kawai suke hira a motar, Fahimah tamkar ba ta gurin a motar, amma har cikin bargonta ta ke jin tasirin muryar Uwais har tsigar jikinta na tashi, suna isowa gida ko gama parking motar bai yi ba ta bude murfin motar ta yi cikin gida.
Ta gilashin motarsa ya saci kallonta, sanye ta ke da jallabiya kirar Oman ruwan toka da mayafinsu.
Kayan sun karbi choculate colour din jikinta sosai.
Sannan ta yi dan haske irin na kamawar wanka a jikin mace mai tsafta.
Uwais ya dauke kai daga dubanta yana sakin tsaki a ransa.
Mace sai fadin ran tsiya kamar diyar qaruna, nan kuwa diyar kwalin taliyar indomie ce.
Maigadi ya sauke akwatunansu zuwa ckin gida.
Da gudu Talatu ta fito tana "oyoyo uwar dakina", ta rungume Fahima wadda ke ta murmushi don ita ba ta kyalkyala dariya sam, murmushi kawai ta ke wanda ke maida ita kamar furen fulawa idan ta yi shi sabida bakin dadashin cikin bakinta da ke bayyana a duk lokacin da ta yi murmushi.
Da taimakon Talatu suka kimtsa duk kayan da suka dawo da su a muhallinsu bayan Fahimah ta ware mata tsarabarta.
Fahimah ba ta san cewa Uwais ya gaya wa Ammi washegari zai kawo Amrah ta yi mata barka da zuwa ba.
Gajiyar tafiya ya sa ta koma barci bayan sallar asubah, ba ta fito ba sai karfe goma na safe, ta yi wanka ta shirya cikin wasu riga da wando pakistan ruwan dorawa, ta kame kakkarfan gashin ta da ribbon kanta babu kallabi, tana tsaye jikin dining tana decorating wurin da kayan kawata dining area da ta sayo daga Saudiyyah ta ji sallamar mace.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: A hanyarsu ta dawowa Uwais tuki kawai yake ba ya ko kwakkwaran motsi har suka iso gida.
Yana yin parking Fahimah ta fice, har tana tuntube saura kadan ta fadi, Uwais ya bita da kallon takaici, dakinta ta shige ta murza key.
Ta jingina bayan ta a jikin kofar tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
Me ke shirin faruwa ne da rayuwar ta a yau?
Ammi na son actualizing wannan auren a lokacin da daga ita har shi Uwais din ba su shirya ba.
A baya ta ce ne sai lokacin da suka shirya karbar juna a matsayin ma'aurata don kansu.
Abinda su duka biyun suka tabbatar ba mai yiwuwa bane.
Amma yau kwatsam!
Ta shammaci kowannen su a lokacin da suka riga suka sakankance cewa auren na su ba mai tabbata bane sannan ba zai je ko nan da can ba.
Yau Ammi ta dauko wata gagarumar rigima wadda baza'a ce rikicin tsufa yayi dalilin ta ba.
Don kuwa bata yi tsufan da zata ce ta manta waye UWAIS ba?
Kuma kuma yaya matsayin ita Fahimah yake a gare shi?
Ta riga ta gama sakankancewa cewa auren ta da Uwais suna ne kawai, sannan a suna zai kare.
Daga ranar da aka daura shi zuwa ranar da zai gaji da ajiyar sa ya bata takardar saki.
Yau ina zata tsoma rayuwar ta idan ta bi Uwais zuwa inda bata san kowa ba?
A gaban Ammi ma ya ta kare da shi balle a bayan idon ta, karkashin mulkin sa da ikon sa?
Kawai sai ta ji hawaye na zubo mata.
Hawayen ba na komai ba ne na tausayin kanta ne.
Namiji sai ana rarrashin sa ana kalallamar sa ana nusar da shi a kan ya so ta!
Don kawai bata da iyaye kamar kowa!
Ko da ya ke watakila Uwais na kin ta sabida kalar fatar ta ne idan ta yi la'akari da irin kalaman da ke fita daga bakin sa akan ta duk lokacin da ya bushi iskar izzar sa.
Ita wace irin mara sa
ce a cikin mata?
Kuma wace irin kaddara ke bibiyar ta?
Daga maraici da rashin asali.... yanzu kuma zuwa BORANCI!
A wannan lokacin wani irin determination (kudiri) ya kutso ya shigi zuciyar Fahimah Shagari....
Determination na self-defence and self-actualization; abin nufi ta tsaya ta san hakikanin kanta, ta kuma kare kanta daga farmakin zuciyarta akan Uwais; kada ta bari soyayyar Uwais dake dankare a zuciyarta ta kassara ta, ta zamo barrier ga farin-cikin ta da cigaban rayuwar ta, ta zubar da kimarta ta diya mace mai daraja a dalilin soyayya.
Zata yi kokari iyakar yin ta, ta ga cewa ko ta ina aka je aka dawo ta baiwa Yaya Uwais mamaki sabani ga tunanin sa; she is not begging for his love.
Hakannan komai nasa yanzu ya koma ba komai ba a idanunta (ya daina burgeta).
Sannan duk yadda ta kai da son sa a baya, daga lokacin da aka sanar da ita an yi musu aure duk wani infatuation sai da ya kama gaban sa.
Su ci gaba da zama a yadda suke a duk inda za su je ba damuwar ta ba ne matukar zata rike determination dinnan nata.
Uwais ya rike duk abinda yake takama da shi itama daga yau ta koyi sarrafa kanta akan sa.
Abinda Ammi ke fatan ya kasance insha Allah ba zai kasance ba, karewa ma ita yau ta fara period kuma sai ta yi kusan kwana hudu yake daukewa.
Kuma an ce tafiyar ta kwanaki uku ce.
Tunanin hakan da ta yi ya sa ta jin wani irin relief a zuciyarta.
Ta bar bakin kofar zuwa toilet ta sakar wa kanta shower mai dumi kamar yadda ake a al
darta kullum kafin ta kwanta barci.
A duk lokacin da tayi hakan zata yi barci mai dadi ne har da saleba.
To yau ma hakan.
Domin kwata-kwata ta cire damuwar tafiyar daga ran ta.
Sai sake-sake da kintace-kintacen abinda zai faru.
Bayan sallahr asubah ta sake wanka ta shirya cikin koriyar atamparta vlisco, ba ta san takamai-mai karfe nawa za su tafi ba, don haka ta kishingide a kan gado da zummar kafin cikar karfe takwas na safe ta sake bincikawa in ma tafiya yayi ya barta ta sani, tayi abinda ke gabanta.
Ai kuwa barci mai nauyi ya sadado ya yi awon gaba da ita.
Don jiya tunani da sake-saken yadda tafiyar ta da Uwais zata kasance kadai bai barta ta yi barci yadda ya kamata ba.
Can!
Cikin barcinta ta ji ana buga mata kofa da dan karfi, kamar za'a jijjigeta.
ho is this?" Fahimah Ta tambaya cikin mamaki da mutstsike ido.
Shiru ba amsa, tamkar da dutse take magana, nan jikin ta ya bata ko waye, saukowa ta yi daga gadon ta bude kofar don ganin wanda ke mata wannan bugun kamar ana binta bashi.
Uwais ta gani harde da hannuwa a kirji sai huci yake kamar mesa, ya hade cikin jamfa da wando na wani tattausan voyel sky blue, as usual hular kansa ta nitse cikin tsakiyar sumar kansa.
Wani kallo ya yi mata kamar fararen kwayar idanunsa za su fado don harara, sannan ya nuna mata agogon hannunsa.
re you aware
? an lika min ke kuma zaki bata min lokaci ki ka shige daki kina ta barci?
Me za mu ci kafin mu bar gida ko ni ki ke jira in je in girka miki?
Fahimah ta tsuke baki, sannan ta murguda shi gefe ta rabe ta gefensa ta wuce zuwa kitchen ba tare da ta tanka masa ba.
Ya saki baki yana kallonta da madaukakin mamaki har ta shige kitchen, shi ta ke murguda wa baki?
Girgiza kai ya yi ya bi ta kitchen din.
Cikin hargagi yace.
ou Goddam Black, 15 minutes na baki ki sama min abin da zan ci, bana hawa jirgi ban ci komai ba, cikina hautsinewa yake yi
Fahimah dai bata amsa ba, ta baiwa banza ajiyar sa, sai kokarin kunna heater din dafa ruwan zafi da ta ke yi.
Da alama so yake ta tanka ya ji dadin bata mata rai, ya ci mutuncin ta a banza bata da mai tare mata, to ba za ta tanka shi ba.
Don an ce karfe daya baya amo.
rin ga dan iska din nan ko, ina magana kin bai wa banza ajiyata?
Fahimah ta ga in ba ta amsa ba zai iya yin zuciya ya shigo ya makure ta, ko ya samu ya huce haushin manna masa ita da Ammi ta yi, ga shi su biyu kacal a cikin gida babu mai ceton ta.
Sai ta ga gara ta tanka, don ya san ta daina tsoronsa yanzu, kuma tana iya mallakar kanta a gabansa.
Sannan ba zamansa take yi ba zaman Ammi take yi.
on Allah ka sarara min mana!
Kafin 15 minutes din ma zan kawo
?.
Ta fada ciki-ciki kamar mai kunkuni.
Babu tabbacin ya ji ta ko bai ji ta ba.
Tsiwa take so tayi masa amma tana tsoro.
Fatanta ya bar mata kicin din.
Ko ta samu ta saita bugun zuciyar ta.
Kada tayi abind ta saba yi a gaban sa.
Tsayuwarsa a wurin na maida ita unease, jikinta ya ki sakewa ya yi aiki yadda ya kamata.
Kamar wadda ke cikin sanyin kankara a dalilin kasancewar sa a wurin tare da ita.
Daurewa kawai take yi don tsira da determination din ta akan Uwais Shagari.
Amma ga mamakinta Uwais ya ki tafiya, karewa ma shigowa ya yi kitchen din ya haye kan island ya yi zamansa.
So yake ya gargasa mata magana ko yaya ne kafin ya yarda ya dauketa su tafi, wadda har ta koma ga mahaliccinta ba za ta mance ba ya sonta ba.
"Yanzu ke kin yarda Ammi ta rusa miki rayuwa da mijin da ba ya sonki, bai taba sonki ba, kuma ba zai taba sonki ba?