Sashe 32
Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ce,
h Ammi ta tashi yanzu
Sannan ya sunkuyar da kai cikin jin nauyin abin da zai fada.
mmi na zo ne tafiya da Fahhima, sai ta zauna gidan Amrah kafin a karasa nata ginin.
Ammi kin ce duk ranar da na shirya karbar aurena da Fahimah da hannu bibbiyu ranar ne za ki ba ni ita.
Yau ga ni da kokon barana Ammi, gwiwa a kasa, ki yi min alfarma ki ba ni Fah-himah
Haj.
Safeeyah ta gyara zamanta tana kallonshi sosai, kamar mai son hango reality na maganganunsa cikin kwarar idanunsa.
Daga bisani ta ce,
wais, ka gaya wa matarka cewa kana auren Fahimah?
Ya girgiza kai, ya ce,
h tukunna Ammi, sabida na ga tana gidan, kuma Amrah ba ta gama samun karfin jikinta ba
Ammi ta yi wani miskilin murmushi, ta ce,
o ba da ni za a yi aikin rashin gaskiya ba, kuma Fahimah ba za ta je gidan matarka da kayanta a ciki da iyayenta suka zuba mata ta yi zaman aure ba.
Har sai ranar da ka zaunar da ita ka gaya mata cewa tare aka daura aurenta da na Fahimah, sannan ka kammala wa Fahimah ginin gidanta ita kadai, don ba za su zauna tare ba.
Sannan zan yarda ta tare.
Duk wannan
ar dadin da ka ga suna yi, ina tabbatar maka don Amrah ba ta sani ba ne, da tuni komai ya rushe.
Don haka ka je ka gama da wadannan matsalolin na gabanka kafin ka zo gabana da neman daukar matarka.
Sannan Uwais, na hana ka shiga dakin Fahimah daga rana irin ta yau, daga lokaci irin na yau, sai kun koma gidanku, don ni ba tsohuwar banza ba ce, da za ka dinga binta daki a gabana
"Yau dai Ammi tsagwaron mugunta ta ke ji!
Uwais ya fada a ransa, gumi na karyo masa ta kowacce kafa mai fitar da gumi a jikin dan adam.
Gini kam ya yi nisa amma bai karasa ba ai.
Amrah kuma in ba ta waya ake so ya gaya mata ba, cikinsa ya zube bai san ta hanyar da Ammi ke so ya je ya gaya matan ba.
Ya shirya a ransa ne sai ta dawo wannan hutun, nan da watanni hudu, lokacin cikinta ya kusa isa haihuwa.
Ya share gumin da ke faman tsatstsafo masa a goshi.
Da dai Ammi zata bari sai gobe ta sa masa wannan takunkumin.
Yau ta barshi yayi sallama da matar sa.
Yau sati biyu kenan rabon shi da Fahhimah.....Fahhimar da ta zo ta canza akalar rayuwar shi gabadaya ta juya ragamar ta cikin dan lokaci kalilan, gaskiyar magana a yanzu bai iya rayuwa ba tare da ita ba!!!
mmi, duk abin da ki ka lissafa zan yi.
Amma ki yi hakuri sai Amrah ta dawo hutu.
Yanzu zan maida hankali a kan ginin, ki taya ni addu
Allah ya hore in gama shi cikin dan lokaci
Yana gama fadin haka ya mike zai fice ko ganin gabansa ba ya yi, imagining yadda zai karar da daren yau babu Fahhimah, bayan har Allah-Allah yake Amrah ta koma ya samu wannan damar, don kuwa ba ta amfana masa komai tun zuwanta sai tsurfa da korafi irin na masu juna biyu.
Na Amrah har da karin sangarta a ganinsa, kamar a kanta aka soma ciki.
Allah kadai ya san iya burin da ya ciwa daren yau.
Don haka washegari ya bude wuta a kan ginin Fahimah kamar zai shiga ayi da shi, wanda ake yi a Unguwar Sulaiman Crescent.
Ya bai wa ma
ikatan watanni biyu su kammala komai.
Komai da ke account dinsa ya tafi ya shige cikin aikin ginin don so yake a yi mata komai kamar na Amrah.
Ammi zuciyarta kal!
Ganin yadda Uwais ya gigice da hukuncin ta.
Burinta ta saya wa Fahimah martaba kamar kowacce mace a gidan miji, in ta ci gaba da barinsa yana zuwa yana rage dare ba zai maida hankali ga muhimman al
muran ba, gini da sanar da matarsa gaskiyar magana.
Ita ba girmanta bane wannan boye-boyen da yake wa Amrah.
Gara ayi ta ta kare.
*****
Fahimah ta ci gaba da zuwa makaranta tare da Ammi, Uwais sabida haushin Ammi ta ce ba zai kara kebewa da Fahimah ba yanzu sai ya yi kwanaki uku bai zo gidan ba.
In ya zo kuma ba ya zama, abinci kawai yake ci ya tafi, in Fahimah na zaune a falon su gaisa yana faman kawar da kai, in ba ta falon ba ya nemanta.
Hakan ya fi komai sauki ga Fahimah don karatunsu ya fara zafi, sai ta maida hankali ga karatu sosai, da tukin mota da Ammi ke koya mata da yamma don ta ce ta fasa na Uwais din, don zai iya amfani da damar ya karya umarninta.
Don haka ta zage tana koya wa Fahimah tukin da kanta at her leisure time.
Allah cikin ikonsa kuma da yake ya sa pressure sosai cikin watanni biyu ginin gidan Fahimah ya kammala, har fenti da komai an gama.
A ranar da yake shirin gaya wa Ammi, ya samu takarda daga babban bankinsu na kasancewarsa cikin wadanda banki ya zaba ya tura kasar Switzerland yin wani muhimmin course da World Bank.
Abun farin ciki ne a gare shi domin in ya dawo karin matsayi zai samu, amma da ya tuna tafiyar na nufin nesanta shi da Fahimar da yake ganin ya kusa samu, sai duk murnar sa ta koma ciki.
Yaji kadaicin duniya da damuwar duniya sun lullubeshi kamar shikadai ya saura a fadin duniya.
Na farko dai ba a ba su damar daukar iyali ba, na biyu ko an ba su Fahimah ba za ta samu binsa ba domin tana gab da zana jarrabawarta ta karshen zango.
Kwas din na watanni uku ne, kuma su goma kadai suka samu wannan babbar alfarmar.
Za su tashi da zarar visa dinsu ta kammala.
A ranar ya zo ya gaya wa Ammi, maimakon ta ga yana murna ta fahimci jikinsa a sanyaye yake.
Kuma cikin matukar damuwa yake.
Ammi is over-excited domin da ma akwai kyakkyawan shiri da ta ke son yi wa Fahimah wanda a baya ba ta yi mata sosai ba.
Gara-gara ma a Sudan ta dan karba ta bata a wajen matar Mahdi.
Tafiyarshi zai ba ta damar yin komai a nitse, in ya so da ya dawo sai su koma gidansu.
Ammi ta ce,
annan ai abun farin ciki ne Uwais, tunda ci gaba ne ta fannin aiki.
Allah ya tsare Ya bada nasara.
Ita ma Fahimah jarabawa za ta yi, don haka in ka dawo sai ku wuce gidan ku insha Allah
Sallamar Fahimah da Uwais ta kasance a wani dare na litinin, bayan ya dawo aiki ya zarto gidan, ana i-gobe zai tashi zuwa kasar Switzerland.
A kalla ya shafe kwanaki masu yawa bai sanya Fahimah a idanunsa ba, kuma bai neme ta ba, don Ammi gasa shi ta ke ba da wasa ba.
In taga lokacin zuwansa ya kusa sai ta tashi Fahimah daga falon ta sata wani aikin.
Ita kuma ta kasa ta tsare a falon taki zuwa ko nan da can.
Sun yi sallama da Ammi har zai wuce ba tare da ya tambaye ta Fahimah ba.
Ransa a cumkushe.
A zuciyarsa yana fadin,
mmi ga
arki nan gabadaya na bar miki har wata uku, sai ki yi ta kullewa a daki.
Tunda dai duk kawaici na ba a gani ba
Shi kadai ya san halin da yake kasancewa a ciki duk daren Allah a gidansa ba Amrah ba Fahhimah, kuma ya yanke shawarar kin kiran Fahimah a waya har sai ranar da suka gama masa gashin kumar ita da Ammin ta, don ita ma ta biye wa Ammi ba ta nemansa, ta durfafi karatun makarantar ta, ba ji ba gani.
Amrah ko ko ya kira ta ma yanzu ba ta iya doguwar hira barci zai yi awon gaba da ita.
Ko ta ce masa ita karatu ta ke yi ya bari gobe za ta kira shi, sanda ta ke free din, shi kuma yana ofis yana fama da ayyukansa.
Don haka in ka ga Uwais a dan tsukin nan har ramewa ya yi, ya fada sosai, ga kasumba ta taru ya ki ya aske ta.
Sosai yake ragaita a zuci da gangar jiki.
Bayan sun yi sallama da Ammi zai wuce, sai cewa ta yi.
a za ka shiga ku yi sallama da Fahimah ba?
Idanun Uwais suka kifta kadan, ta wani fannin tamkar wanda aka aikowa da manzon Rahma, wani kuzari ya da rabon sa da irin shi tun ranar da ya zo daukar Fahimah su tare a gidan sa amma ta gwale shi da takunkumin ta, ya ce,
mmi kin yi izni?
Da murmushi a bakin Ammi ta ce,
a yi izni Uwais, ko da ma can ai ban hana ku gaisawa ba a waya ko a falon nan.
Na fi so ne dai ta tare a dakinta, sannan ku je ku karata.
Amma sallama ai ta zama dole
Tana gama fadin haka ta wuce zuwa dakinta, ta ce da Uwais,
aduwar alkhiri
Ammi na bada baya Uwais ya juya dakin Fahimah da takunsa na sassarfa.
Tana kwance tsakiyar gadonta ta rufe kanta da pillow, amma ba barci ta ke ba, tunanin Uwais ta ke yi da tsawon lokacin da suka dauka ba tare da juna ba alhalin suna gida daya, kuma suna jin muryar juna sau tari cikin gidan, sannan su kan ga juna jefi-jefi.
Ba ta san dalilin Ammi na nesanta su da juna har haka ba, amma ta yarda komai Ammi za ta yi akan su, to za ta yi ne for her own betterment.
Itama ta fi yarda Amrah ta san me suke ciki in ya so komai ta fanjama-fanjam, kuma tana bayan Ammi na ba za ta shigar wa Amrah gida ba don ba ta nan.
Da murda kofarsa da sallamarsa ciki-ciki duka ba ta ji su ba.
Sai kwanciyarsa a gadon bayanta.
Ya sakar mata dukkan nauyin sa.
An ce duk nauyin miji mace na dauke shi tsaf ba tare da ta ji nauyin ba ita.
Amma Fahimah har
ar kara ta saki sabida nauyin Uwais.