← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 35

Sashe 19

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gara ya je ya nemi wani dakin ya kai ta, shi ba zai iya kwana da mace a daki ba Amrah ba.

Ya tada sallah, a ransa yana fadin, idan kafafunta suka tara jini za ta zauna ne.

Bayan ya idar, ya kira kan talfon ya yi odar abincin mutum biyu ba tare da ya tambaye ta wanda ta ke so ba.

Ya san dai abincin gidansu kullum ganye ya fi yawa (vegetables) don haka abin da ya yi order kenan, sai white rice and stew da farfesu.

Ba jimawa aka kawo, lokacin ta gaji da tsayuwar da runtse idon kamar yadda yayi hasashe ta shiga toilet.

A yanayin da ta ke jin jikinta ga gajiya ga takurar period wanka kawai za ta yi ta ji dadi, don haka ta yi wankan, ta kimtsa kanta, ta yi brush sannan ta maida kayan jikinta ta fito.

Samunshi ta yi yana cin abinci.

Looking smart and gentle a duk abin da yake yi.

Uwais, ba zai daina tafiya da ruhinta ba watakila har gaban abada!

Komai nasa mai ban kaye ne ga zuciyarta, ba tun yau ba ta dade tana satar kallon sa in yana cin abinci.

Wani irin gaye yake komawa mai yanga idan yana cin abinci amma ba wai ya san hakan ba shi.

Actually bai san me ya sa ba, jin haushinta da tsanarta da yake sun dan ragu, but bai da wani feeling ko kankani a kanta.

Ya sa wa ransa ta zame masa dole, dole kuwa ya yi hakuri da ita ya sawa rana juriya in yana son farin cikin Ammi.

Ya yarda wholeheartedly Ammi ke son Fahimah wato da dukkan zuciyar ta, da kyar in son da ta ke matan bai rinjayi wanda ta ke masa ba.

Da zamanta shiru ya ishe shi sai ya ce.
bincin ma jira ki ke in ce miki ga shi ko?

Ashe kuwa za ki kwana da yunwa, look, ki rage wadannan mayun idanun naki a kaina kada ki sa in kware
Uwais ya fada ganin ta je can karshen dakin ta zauna a dofane tana kallon sa, ba tare da ta bi ta kan abincin ba.
alama, ki yi maza ki ci mu je in kama miki daki, kada matata ta jiyo tsamin jikin nan naki ta waya
Wani murmushi Fahimah ta yi, maimakon maganarsa ta bata haushi, he noticed the murmushin, sai dai bai san ma
narsa ba.

Bakar magana ya gaya mata wadda kowacce mace ka gaya wa ranta zai sosu.

Burin sa har kullum shi ne bacin ranta, muzantar ta da wulakantar ta.

To ta daina bari wani abu nasa ya bata mata rai don ba zamansa ta ke yi ba.

Ba ta ci abincin ba har ta yi shirin kwanciya, a ranta tace ka ci kai kadai ka kara zama katoto dama gaka nan masha Allah.

Duk da irin kartawar da cikinta ke yi, ta gwammace ta barwa Uwais abincin sa tunda har ya ce tana tsami.

Ta ji haushi don haushi amma ko a fuska bata nuna ba.

Uwais kuma bai kara ce mata uffan ba, ya harde bisa gado sai faman kiraye-kirayen waya yake yana zuba turanci kamar bakon Ba
reshe.

Fahimah ta dauki filo daya ta jefa kan sofa ta rufe kafafunta da katon hijabinta ta yi kwanciyar ta.

Waya ta karshe da ya amsa ta fahimci da matarsa ne, kuma maganar da yake yi ba cikin dadin rai yake yin ta ba.

With a bitter tune take fita fiercely.

Duk da haka a tausashe.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat:
hatever Amrah
? whatever makes you to disgrace me ta hanyar tafiya babu izni na.

Ga dan iska ko?

Wanda bai isa ba, bai isa da matar sa ba don kawai yana son ta, tunda ni baki dauke ni a bakin komai ba ki je ki ji da boko, ni ma in ji da loneliness dina.

Ba'a sayen soyayyah da na sayowa kaina wata, sai dai duk abin da ya faru nan gaba kada ki yi kuka da ni.

Ki yi da kan ki.

Na fada miki na kara, ban iya rayuwa babu mace tare da ni, this is my hidden nature, ina na akan baka na na ki dawo B.U.K in kina son auren mu ya dore
Da sauri ya kashe wayar da ya tuna akwai mutum a dakin, shaf ya manta da ita, shi mutum ne mai sirri da ba ya son wani ya ji sirrin aurensa ko yaya yake da shi, balle Fahimah.

Gyaran murya ya yi don ya tabbatar ta yi barci ko ba ta yi barci ba?

Ta ji sirrinsa da Amrah?

Abin da bai sani ba ta dade da kaiwa birnin Sin a barcinta tun sanda ya fara maganar.

Har tashi ya yi ya wuce ta gaban sofa din ya tabbatar barci ta ke don ga numfashinta na sauka a hankali.

He felt relieved.

Ai in ta ji Amrah ta gudu ta barshi sai ta yi dariya ta kyakayata, ta gane son da yake mata ya fi nata yawa wanda hakan abun kunya ne a gare shi, kuma a zahiri ya dade da fahimtar hakan.

Ba ya so ya yarda ne da gangan, ya fi alakanta hakan da ra
yin gidansu,
an boko ne na ga ni kashe ni, wadanda za su iya sadaukar da komai don tsira da profession din su.

Soyayya is their last priority.

Shi kuma ba shi ya sanya wa kansa soyayyar Amrah ba, Allah ne ya sanya masa, idan za ta zama cutuwa a gare shi kamar haka, yana rokon Allah ya rage masa.

Ko ya cire masa bakidaya
Ya yi nafilfili masu yawa a daren yau kafin ya kwanta.

Da asubah yana so ya tada Fahimah sallah yana kwabar kansa shiga sha
ninta.

Kulawa ma ai yabawa ce.

Ita da kanta ta tashi ta shiga toilet ta yi changing sannan ta koma ta sake kwanciya.

Sai wajejen bakwai na safe ta tashi ta ga Uwais ya tsuke cikin Spanish suit bakake wul, wadanda suka maida shi bature zallah, sai tazar kwantacciyar sumarsa yake yi da kumb yana mulketa da Arganavita.

Aka kawo karin kumallo ya karasa ya karbo ya rufe dakin, ya zauna yana ci yana tunanin ya aka yi jiya ya manta bai je ya kama wa Fahimah daki ba?

Zuciyar sa ta yi gaggawar ba shi amsa da cewa,
manar Ammi
What if wani ya je ya cutar da ita a
bakon wuri, me zai ce wa Ammin ta?

Don haka ya cire maganar kama mata daki daga ransa sam-sam, zai ta jure hakurin zama da ita.

Da ganin bakar fuskarta.

Har Allah ya iyakance masa wannan kaddara, ya dauki aurenta matsayin jarabta wadda yake fatan Allah ya ba shi ikon cinyewa, ya sa ya gama da mahaifiyarsa lafiya.

Ammin da yake so fiye da yadda yake son kansa.

Yadda Uwais ya dauki aurensa da Fahimah matsayin mafi munin jarrabawa a gare shi, ita Fahima ta dauki aurenta da Uwais ne as a luck by chance, ko Uwais ba zai so ta ba aurensa rumfa ne, mafaka ne, kuma waraka daga tsohon ciwo, tsohon mikin da ya dade yana wahal da ita.

Don haka ita ko Uwais ba zai so ta ba, she's now contented and satisfied with everything in life.

Ammi ta yi wa zuciyar ta gata, gatan da ba za ta gushe tana mata addu
ba, tare da roka mata gamawa da duniya lafiya har karshen rayuwar ta.

Da ya so ta, da kada ya so ta, yanzu duk uwar su daya uban su daya a wurin ta.
an kananan shekarunta ta yarda love never fades
? wato soyayya bata taba kodewa (son da take wa Uwais na har abada ne) sannan sai ta ga dama ta ke yin kanta.

In haka ne kenan ba ta ga laifin Uwais Shagari da ba ya sonta ba, soyayyar ba ta ga damar yin kanta a kansa ba.

Tasa soyayyar a kan Amrah ta ke, wanda ko kusa ba yin kansa ba ne.

Ita kuma ta kasance mai yawan yi wa dan Adam uzuri a rayuwar ta, kamar yadda Annabi SAW yayi umarni, don haka komai Uwais zai mata uzuri za ta yi masa, uzuri bayan uzuri sau saba'in, uzuri albarkacin Ammi, da uzuri albarkacin soyayyah.

Ya ci abincinsa, ya kira Ammi a waya, ya ji yadda ta sauka, sannan ya gaya mata su ma sun sauka lafiya a jihar Lagos.

Ammi farin ciki kamar ta yi ya ya!

Ta sa wa Uwais albarka a waya ya fi cikin carbi, yafi sau shurin masaki.

Bai taba jin farin ciki a muryar Ammi irin na yau ba.

He was astonished!

Har haka ta ke son sa da Fahimar?

Shi kuwa me zai hana shi ya daure ya ci gaba da faranta wa Ammi, in ya so ita Fahimar ta ci gaba da ganin other side din Uwais ita kadai, uwarsa ta yi ta sanya masa albarka irin haka???

"He who has the blessings of a mother....never loss in life".

Ammi ta cancanci samun kowanne irin farin-ciki daga gare shi, sabida bata da kowa sai shi, kuma bata da mai rufawa Fahimah asiri bayan shi, kowa zai auri yarinyar ba zai mata rikon da zai gamsar da Ammi ba, idan aka yi la'akari da asalinta, amma idan shine yasan in reality zai rike auren ta koda a ladan noma ce, sannan ko gunduwa - gunduwa zai dinga yi da ita a bayan idon Ammi, a gabanta ya nuna shi mai kyautatawa ne ga Fahimar, albarka zai yi ta sha kwando-kwando irin wannan a wurin Ammi.

Murmushi ya yi mai sauti, a lokacin da ya gama wannan tunanin, har yanzu Ammina kan layi, tana ta zuba masa hirar mutanen Sudan, ya ce,
mmi ta ki cin abinci tunda muka zo, kuma bata magana, ko za ki yi mata magana kada wani abu ya faru a ce laifi na?

Ammi ta ce,
a ni Fahimar
Fahimah na jinsu, a ranta ta ce, ta inda ya koma ke nan?

Hada ta da Ammi?

Ina ruwansa da kin cin abincin ta?

Cikin sa ko nata?

Ita bata son munafurci.

Ta lura abinda ya koya kenan.

Tana karbar wayar ta yi sallama.
in ki cin abinci Fahimah, a wane dalili?
Chapter 19 · 0% Book details