Sashe 8
Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta san in ta yi mata umarni ba za ta tsallake ba, amma ta zabi kawai ta yi shiru akwai lokaci mafi dacewa da ya kamata ta fada matan ba yanzu da ta ke fama da jarrabawa ba.
Haka ta je centre din da aka tura ta ta zana jamb dinta lami lafiya.
Fahimah ta yi sallama da Yan Dutse da kawayenta da suka yi zaman aminci musamman Majida Salisu.
Ya zama kullum tana gida, amma sam ba sa haduwa da Uwais.
Yanzu ta daina lekensa in ta san zai shigo gaida Ammi, daga ta ga karfe shidda na yamma ta yi, ta yi sallama da falo kenan.
Don ta san duk inda bakwai na magriba ta yi yana cikin gidan.
Da ma sun fi haduwa da safe, in ta fito za ta tafi makaranta, shi ma ya fito zai tafi aiki, to ita yanzu ta yi sallama da makaranta.
A hankali ta ji zuciyarta na samun sauki daga azalzalarta da ta ke yi a kan Uwais infatuation din yana raguwa musamman da ta daina ganinsa.
Yau saura sati biyu kenan daurin aure.
Ammi ta gaya masa yadda ya yi wa Amrah kayan aure, haka zai yi wa Fahimah, adadin sadakin da ya biya na Amrah haka zai biya na Fahimah.
Bai tanka ta ba a lokacin da ta ke maganar, amma zuciyarsa ta yi bakikkirin, sai babbakewa ta ke kamar ta kama da wuta.
Musamman ya kira Jabeer ya ce, yana son ganin Murjanatu, Jabeer ya yi masa iznin zuwa, suka zauna yana tambayarta dukkan favourite abubuwa na Amrah, colour da design da size.
Ita Murjanatu ya bai wa kwangilar hada komai don ta fi kowa kusanci da Amrah.
Amma ya roke ta kome ta saya ta sayi guda biyu kala ba daya ba kuma girma daya.
Murjanatu ta so ta yi mishi tambaya kan hakan ta fasa.
Don a yadda suka tabbatar Uwais na son Amrah, tunanin aurenta tare da wata ko yi mata kishiya ba zai taba zuwa kansu ba.
Cikin sati daya Murjanatu da kawarta suka hada komai na gani na fada irin nasu na 'yan gayu ya zo a kwashe saitin akwatunan a booth din motarsa ya kai wa Ammi, sai da ya yi sawu biyu sabida dozen biyu ne akwatunan, kowacce sha biyu, samfurin LV (Louis Vuitton).
Ammi ta yaba da kayan ta ce masa kowace ce ta hada kayan ta san abu mai kyau da quality, ya ce,
"Murjanatu ce matar Jabir".
"To Allah ya shi albarka".
In ji Ammi.
Talatu Ammi ta sa ta kwashe kayan ta kai dakin Fahimah, ta ce ajiya ce ta ajiye mata.
Talatu ta san komai, kusan ta fi kowa farin ciki da wannan hukunci na Ammi, don kullum tana zama ta yi tunani mai zurfi a kan auren Fahimah zai zamo kalubale mai girma ga rayuwarta.
Don haka hukuncin Ammi shi ne daidai ko da mata goma Uwais zai aura in dai zai hada da Fahimah hankalinsu ya kwanta.
Talatu ta zarce matsayin 'yar aiki
a gare su don ko kudin aiki ba ta karba, shekara da shekaru sai ihsanin da Ammi ta ga damar yi mata.
Ta zame musu kamar 'yar uwa ta jini.
******
Aka ce rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya.
Kwanakin daurin aure na matsowa, soyayya gangariya na karuwa tsakanin Uwais da amaryarsa Amrah talkless of Fahima da ba ta cikin lissafin sa.
Ya kama gobe daurin aure, wanda za a yi a gidan Alh.
Umar Dikko na Kano, tun jiya kawu Shureim da manyan 'ya'yan sa biyu Mahdi da Mohamed da kannen Ammi biyu su biyar kenan suka iso daga Khartoum, sai mutanen Shagari kwansu da kwarkwatarsu.
Duk Uwais ya yi musu masauki a gidan saukar baki na Tahir Guest Palace.
Yana zaune a kujera gefen Ammi, sanye cikin wani lallausar voyel milk colour kansa babu hula, sumar nan ta kara kwanciya sosai, ta kuma kara cika da yawa domin ya dade bai rage ta ba.
Ammi na daga gefensa tana shan shayin da Fahimah ta dafa mata ta kule a daki musamman da ta san Uwais zama zai yi a falon.
Wayoyin jama'a yake ta amsawa kala-kala, duk a kan shirin daurin auren gobe.
Sai da Ammi ta fahimci ya tsagaita da amsa wayoyin ta kira sunansa.
"Uwais!".
Ya dago lumsassun idanunsa ya dube ta.
"Gobe nan ne wurin haduwa (meeting point) na daurin aure kafin ku tafi gidan su yarinyar?"
Ya amsa mata da "Eh, Ammi".
Ammi ta ce, "tam...
To aurenka da Fahimah za a fara daurawa, ina nufin Fahimah ita ce za ta zama uwargida, sannan a yi na ita MATAR SO".
A yadda ta fadi maganar cikin shagube ya yi bala'in touching dinsa.
Sai dai ya yarda da abin da ta ce din, "Eh, Amrah matar so ce, ta ki 'yar kuwa matar shige wadda anka ce ba ta daraja sam".
Bai ba ta amsa ba sai ma tashi da ya yi ya bar wurin.
Ta san za a rina, da ma ba ta tsammaci ya tankata ba, umarni ta bayar kuma dole a bi in ana son zaman lafiya.
Ta kira Kawu Shuraim da madaurin aurensa su Baffa Haruna duk ta gaya musu hakan, su Baffa Haruna sun yi mamaki matuka, amma da Kawu Shuraim ya yi musu bayanin komai sai suka fahimta.
Washegari kofar gidan Late Grand Khadi Abdulkarim Shagari ya dinke da jama'a ko ta ina, musamman ma'aikata GT na Kano.
Aka daura auren Fahimah Abdulkarim Shagari da Uwais Abdulkarim Shagari a kan sadaki mafi kankanta amma mafi albarka.
Daga nan suka zarce gidan Alh.
Umar Dikko aka daura na Amrah Umar Dikko da Uwais Abdulkarim Shagari.
Daga nan shi da ma'aikatansa da abokansa suka wuce liyafar cin abinci ta bayan daurin aure wadda abokai suka shirya karkashin jagorancin Jabeer, a gidan saukar baki na Ni'ima.
Uwais farin cikin da yake ciki a yau ba zai misaltu ba, biro ya yi kadan ya bayyana shi.
At last ya mallaki AMRAH so duk wani kalubale, duk wani bacin rai zai zamanto nafilah.
Suna fitowa daga wajen liyafar ya kebe kansa a gefe, Amrah ya kira.
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: Cikin wani yanayi ta ganta tare da Yaya Uwais, yanayin da ya fi kama da muamalar auratayya.... it is something which goes far beyond mere explanation..da fatar baki but extent reality cikin idanunta, kamar ido biyu ba mafarki ba; mafarki ta yi ma ga ta a matsayin matar Uwais, sabida abinda ta gani yana faruwa cikin mafarkin ta sani baya yiwuwa sai da aure.
A karshen mafarkinta kuma ta ga yaya rututu zagaye da su, wadanda har ba ta iya kirga su ba sabida yawansu ya cika dakin da suke ciki.
A matukar firgice fahimah ta farka, jikinta ba inda ba ya rawa, a karshe ta mike zuwa toilet ta sakarwa kanta shower ta ruwa mai dumi ko ta samu karkarwar da jikinta ke yi ya tsaya, ko ta samu ta yi regaining consciousness dinta.
Barcin da ba ta koma ba kenan har rana ta fito.
Tana kwance lamo a cikin bargo, ta kasa fita taya Talatu aiki yadda ta saba, kasancewar yau lahadi ba ta da makaranta, kuma ta yi sallar asuba da azkar dinta na safiya, sai kawai ta ci gaba da kwanciyarta.
Karfe goma na safe Uwais ya fito daga bangarensa zuwa sassan Ammi, ya same ta tana sallar walha, sai ya samu gefen gadonta ya zauna yana tsumayinta har ta idar, ta yi addua suka shafa tare.
A yadda Hajiya Safiyya ta ga fuskar Uwais yau, tana wani irin annuri ta tabbata yana dauke da labarin da ya faranta ransa.
Ya sauko daga gefen gadon ya dawo daidai kafafun Ammi ya zauna.
Ko daga irin zaman da ya yi Ammi ta fahimci muhimmiyar magana ta kawo shi.
Ya ya aka yi ne ka zo ka sa ni a gaba yau Lahadi ma me ya fiddo ka da wuri haka?
Na dauka duk lahadin karshen mako sai sha biyun rana ka ke fitowa?
Uwais ya gyara zamansa sosai ya ce, Ammi na kasa barcin ne, sabida ina cikin farin ciki, Amrah ta amince min in tura magabatana a yi maganar aurenmu.
Ba sai ta kare karatu ba.
Ammi ta dube shi da sakakken baki, idonta na wani irin budewa ta ce,
Wace ce haka?
Kansa a kasa ya ce, Yarinyar da na ke nema, kanwar Jabir, na dade da gaya miki ina neman aure.
Hajiya Safiyyah ta yi masa wani irin sakaran kallo, ta ce, Uwais!
Da kakkausar murya.
Da sauri ya dago ya dube ta cikin tsananin fargaba.
Ta ce, Ba kanwar abokinka ba, ko kanwar shugaban kasa ce ban yarje maka aurenta ba.
Mace ko da zubarjadu da yakutu aka kera ta haka za ta ganka ta barka, don tuntuni kana da matarka.
Kalaman karshe tamkar saukar alburushi ya ji su a kirjinsa.
Hajiya Safiyyah ta ci gaba da cewa, Da ma na zuba maka ido ne in ga iya gudun ruwanka, wannan rawar kan da ka ke a kan yarinyar nan kadai zai hana ni yarda da batunta, don na san muddin ka aure ta ba za ka taba yi wa FAHIMAH adalci ba!
A matukar razane kuma a firgice Uwais ya dago ya dubi mahaifiyarsa.
Fahima?
Fahimah!
Fahima!!
A ina ya taba jin wannan sunan???
Kamar kullum yana jinsa cikin gidan nan.
Daga bakin Talatu da Ammi.
Cikin wani irin rashin kuzari yake kallon mahaifiyarsa.
Ammi, I didnt get you right, wallahi ban gane maganar da ki ke yi ba.
Hajiya Safiyyah ta mike tsaye tana nade sallayarta, In ma ka gane ai cewa za ka yi ba ka gane ba, sabida rainin hankali irin naka Uwais, tunda dai ni da Hausa na yi maganata.
In hausar ce ba ka ji sai ka je ka nemi wanda zai fassara maka.
Ta fice daga dakin ta barshi nan a zaune.
Uwais ya ci gaba da zama a inda ya ke tamkar an kafe shi.
Kokari yake ya yi digesting maganganun Ammi cikin kwakwalwarsa abu ya gagara.
Allah ne ya kawo Talatu wadda yake kira "Baba Talatu" da tsintsiyar kwakwa a hannunta za ta yi wa Ammi shara.
Ta ganshi a zaune kamar statue, ta ce, Uban masu gida tunanin me ake haka?