← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 35

Sashe 17

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Me ya sa ba ki yi wata hobbasa don kwatar wa kanki
anci ba?

Ba ki da masaniyar ina da mata ne, wadda nake matukar so kamar na ba ta raina?

Tunda ya fara maganar Fahimah ba ta dago ba, firar dankali ta ke, amma da ya zo sentence dinsa na karshe sai ji ta yi ta tafi da tsokar hannunta, wato ta yanke hannunta da kakkaifar wukar da ke hannunta.
na da matar da nake so, kamar na ba ta raina
Wani statement ne wanda shi a wurinsa ba komai ba.

Amma a gare ta tamkar digar ruwan dalma ne a kan fatar jikinta.

Tana so ta ba shi amsa, daidai da wadda ta dace da munanan maganganunsa sai ta tuna UWAIS ne.

Wani kwayan mutum guda daya da zuciya da ruhinta ke so, wanda ta yi wa kanta alkawarin zama da shi da kasancewa tare da shi against all odds koda zai yi ta yankar tsokar naman jikin ta yana sanyawa a miya albarkacin Ammi Safeeyyah - Basudaniyyah.

Balle common bakar magana akan matar da yake so.

Sai ta saki wukar da ke hannunta kasa, hade da dankalin ganin jini yana fita.

Ta kudire ko dukanta Uwais zai yi cikin gidannan ba za ta soya masa dankalin nan ba, ko dai ya tafi da yunwarsa, ko ya kirawo matar da zai iya bai wa rai ta soya masa daga Malaysia.

Ta kashe komai ta wuce ta gabansa hannun ta nan digar jini ba tare da ta ce da shi komai ba.

Murmushin mugunta ya yi, ko ba komai ya ci nasara, ya yi spoiling mood dinta ita ga amarya zata bi miji Ikko, ta samu miji a bagas sabida ba Amrah, kuma gashi ya janyo ta yanke hannu.

Sai yaji bai ji dadi ba daga kasan ransa saboda ko kadan ba ya son ganin jini ko yaya daga jikin dan Adam.

Don haka ya sauya shawara ya bi bayanta zuwa dakinta ba tare da ta san ya biyo ta ba.

Toilet ta shige ta sakar wa hannun famfo a sink, tana kalon jinin jikin ta na gudu treda ruwan tana hawaye, sai jin motsin mutum ta yi daga bayanta.

Da sauri ta juya a tsorace, ashe har ya iso gab da ita sai da ta bigi kirjinsa.

Da sauri ta ja baya.

Dan farin bandeji ne a hannunsa na nade ciwo da ruwan hydrogen, daya dauko a dakin Ammi, sabida bata wasa da first aid ita, ba tare da ya ce komai ba ya kama yatsan ya zuba hydrogen a kan yankan, sannan ya soma kokarin daurewa da bandejin.

Fahimah, ta kusa suma a wannan lokacin sabida kyakkyawan closeness din da ya shiga tsakanin ta da Uwais.

Wanda hakan bai taba faruwa ba koda da kuskure.

Ita da Uwais sai kallo daga nesa.

Wani irin sassanyar kamshi yake yi na Maison Francis (Baccarat Rouge) dake tashi a hankali daga jikin sa.

Shi kuwa Uwais bai yi don wata manufa ba, sai don tunawa da ya yi da kalaman Ammi.
ahimah amanar Allah ce tsakaninmu Uwais
? na ba ka amanarta
? idan ka cutar da ita kai da Allah
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Ita in wani ne ya gaya mata a baya cewa Uwais na magana haka ma, ba za ta taba yarda ba.

He is not that miskili to such an extent kamar yadda ta dauka a baya, kawai dai magana sai ya ga damar yin ta, kuma in ya so yana yin abar sa sosai ko da bazaka bashi amsa ba.

Uwais Shagari, ya fara sassauta wa ransa kiyayyar Fahima a bisa dalilai da dama.....

Muhimmi shi ne, ganewa da ya yi ita din is a source of geniune happiness na mahaifiyar sa wadda in ya zauna da ita ko da ba ya kyautata mata in disguise Ammi za ta yi ta farin ciki da shi ne, tareda sanya masa albarka.

Sannan auren su wani abu ne inevitable (wanda ba makawar sa) wanda bazai iya tsallakewa ba, watakila har abada, don ba zai taba iya mikawa Ammi takardar saki ko ta wata mace daban, balle wannan wadda take so kamar ita ta haifa ba.

In haka ne kenan takurawa rai da kiyayyar da babu riba a cikin ta aikin banza ne.

Zai zauna da Fahimah koda har abada ba zaya so ta ba.

Sai ta zauna zaman Ladan Noma (as he called it).

Tunda haka Ammi ta zaba mata.

A kullum yana tuna dawainiyar da Ammi ta yi da shi tun yana yaro, da dawainiyar ilminsa a bayan ran mahaifinsa ba tare da taimakon kowa ba.

Ita ke kaishi makaranta ta dauko shi tun daga primary har secondary bata yarda kowa yayi mata wannan aikin.

Yau ga shi yana ta cin gajiyar ilmin ta ko
na, sannan ta bar shi ya auri Amrah duk da yakinin da yake da shi na ba ta sonta, amma ta kwatanta adalci ko a fuska ba ta taba nunawa Amrah ko wani ba.

Ammi na da wasu irin principles (doctrines) akan akan karan-kanta, wadanda ta dora Fahimah a kai, wanda su ne ta ke masa kwadayi, amma ya kasa ganewa da gangan.

Yana can ga kyale-kyalen da baya lasting.

Tana da tabbacin watarana zai gane din, tana raye ko bata raye, cewa Fahimah matar rufin asiri ce kuma babban alkhairi a gareshi, har ma ya zo ya gode mata da dukkan godiyar da zai iya.

What he needs most is time ....and closeness ga Fahimah.

Bayan fitarsa Fahimah ta ga ya dace ta sauya sutturar jikinta ko da ba ta yi kwalliyar da Ammi ke so ba, don haka ta yi wankanta a nitse, da Olay shower gel (goats' milk), ta fito ta zauna shafa, sannan ta fiddo wani jan material da aka yi wa fitted gown ta sanya, yana da ratsin golden da baki a jikinsa.

Ta yi daurin kai ya zauna cif, sannan ta matsa gaban mudubi tana duba turarukan da Uwais ya ajiye a wajen har guda uku.

Ashe sunan turaren Uwais ke nan (Maison Francis, Baccarat Rouge).

Kwarai ta dade tana son kamshin, domin kuwa kamshinsa na mannewa a zuciya ne tamkar maganadisu, musamman ga ruhin diya mace ma'abociyar soyayyar da bata samu martani ba.

Ba ta san lokacin da ta kai turaren ga bakinta ta sumbata ba, and it feels like
?.. like Uwais din himself ta ji ta sumbata apparently.

Wanda hakan ya aika wani irin sako cikin ruhinta, wanda ta ji shi tun daga kwakwalwa har zuwa toe wato babban yatsar kafar ta.

Something like emotion mai narka zuciya, da sanya wani irin daddadan feeling.....

Fahimah ta shiga waiwaye ko da wanda ya ga abun kunyar da ta yi (sumbatar turaren Uwais).

Ga dukkan taimakon Allah, sai ya kasance babu kowa.

Daga ita sai Ubangijin ta kadai, sune kuma kadai suka san adadin son da ta ke yi wa Uwais Shagari.

Tana kuma rokonSa Azza Wa Jallah a kan in son da ta ke yi wa Uwais, ba alkhairi ba ne a gare ta to ya yaye mata bakidaya ko ya sassauta mata.

Akuyar cikinta ta yi kukan da ke tuna mata rabonta da abinci tun jiya.

And cikinta na da nasa hakkin a kanta ba soyayyar Uwais kadai ba.

Wadda ta zamo mafi rinjayen abin da ke consuming lokacin ta.

Idan ta lula a duniyar tunanin Uwais, ba ta sanin cewa lokaci na tafiya, sai ta farga da awannin da ta karar ba tare da ta san me ta ke yi ba.

Hormones dinta suna da karfi, da ba su sabbaba mata ciwon tunani a kan Uwais ba.

She then decided to pray
? wato ta yanke shawarar komawa ga addu'a akan Uwais Shagari, tunda an ce addu
maganin komai ce.

Addu'ar data dukufa yi a yau itace.

Idan son da ta ke wa Uwais alkhairi ne, Allah ya juyo da hankalinsa kanta cikin gaggawa.

Idan ba alkhairi ba ne a gare ta, Allah ya nesanta zuciyarta daga kansa Ya raba ta da wannan koshin wahala.

Karfe biyu aka kawo mata abinci mai rai da motsi taci sama-sama daga nan kuma barci mai dadi ya dauke ta, barci sosai ta yi wanda ba ta farka ba har Uwais ya dawo.

Karar sautin talabijin shi ya sanar da ita dawowarsa.

Da ta bude ido ta dubi inda yake zaune yana shan lemun power horse daga shi sai farar singlet da dogon wandon suit din da ya cire.

Jikinsa ne ya gaya masa tana kallon shi, ya juya ya sakar mata harara a ran shi yana fadin ta kafe shi da ido kamar mayya, ko sun hada jini da maitar ma wa ya sani ne?

Kunya sosai ta ji da ya kama ta kane-kane a cikin kallonsa.
re you not praying ne ke? (Ke ba kya sallah ne)?

Tunda muka zo ban ga kin dungura goshinki gaban Ubangiji ba, sai kallon mazan mutane kamar kya cinye su?

Fahimah ta tsuke baki da fuska cikin bacin ran kalaman sa, sannan ta mike daga kwanciyar.

Ya dan bi ta da kallo tana wucewa ta gabansa, sai ya ji kamshin turaren sa na tashi a jikin ta kadan-kadan.

"Lallai ma yarinyar nan ta fara raina ni".

Uwais ya fada a ransa.

Amma bai furta mata ba dai in ma ta yi ne don ya tanka.

Anyway jan kayan nan sun mata kyau as black as she is, sannan she
tall, slim and well-structured.

Bar ta dai da 'bakin ta' da ke munana ta (dark-skinned).

But even her lips are looking luscious, succulent and irresitable to every tensed man
?" da sauri Uwais ya shafo sumar kansa cike da fargabar Allah ya sa ba a fili ya fadi wadannan baranbaramar kalaman ba.

Daidai lokacin da ta fito daga toilet fuskarta da damshin ruwa, sai ya ga ruwan ba ya mannewa a kan fatarta sabida sulbinta.

Sai digewa yake dis-dis.

Da sauri ya kauda kansa da suka hada ido, yana tambayar kansa, me yake kallo ne haka???

Duhu ya shigo, bayan ya yi sallar isha ya ji yana da bukatar fita supermarket, akwai abubuwan bukata da yake son sayo musu.

Ya mike ya maida rigar sa, ya dau wayarsa ya sa a aljihu ya durfafi kofa.
Chapter 17 · 0% Book details