← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 35

Sashe 11

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ya yi, ya janyo ta ta dawo gabansa, wani irin kissing dinta ya shiga yi, passionately, ya ce, Amrah in ki ka ba ni Da, kin gama min komai a rayuwa, ni ko ba za ki shayar da shi ba ki haifa ki ba ni abina, zan bai wa Ammi na ta kula min da shi.

Amma in ki ka ce sai kin zama likita za ki haihu Amrah ai zuwa lokacin na soma furfura ina neman abokin tafiya masallaci ne.

Zan taya ki raino ke har nakudar in ba ki so na yarda ki yi epidural.

Ni dai burina in haihu da ke Amrah ko sau daya ne a rayuwa sabida son da nake miki.

Yatsunta ta kai ta toshe masa baki, Na amince Habib-Qalby, Im now ready to conceive, kuma tare za mu raini dan mu ko yarmu insha Allahu, zan raba lokacina biyu in ba ku rabi, ka taya ni addua Allah ya ba ni kafadar dauka...

Da sauri Uwais ya ce, Lah yukallifullahu nafsan illa wusaha.

Maana, Allah ba ya dora wa wata rai face abin da za ta iya.

Ke mace ce Amrah, kuma mace da aure da haihuwa a ka santa, don ita jaruma ce fiye da namiji, boko shi ne last priority hidimar aure tana kan gaba da komai.

Amrah don ita ce hanyar shiga aljannah.

Daga haka Uwais ya canza akalar hirar zuwa mafi aala a gare shi.

Sumbutarta yake kusfa-kusfa kamar zai hadiye ta.

Ya yi kewar Amrah a kwanaki uku kacal yadda biro ya yi kadan ya bayyana, haka ita ma sai da ta ji idanunta sun cika da hawaye don tausayin Uwais, domin ta lura ba karamin azabtar da shi ta yi ba.

Addua ta ke, Allah ya ba ta lafiya da tsawon ran da za ta ci gaba da kulawa da bukatar gangar jikin Uwais da lafiyar haifa masa yaya, ta yarda Uwais mai sonta ne, mai kuma matukar kaunarta wanda ya bambanta da sauran maza a halayya da dabi'a wajen nuna wa matansu soyayya a fili, abinda maza da yawa basa iyawa a wannan zamanin sabida girman kai.

Alhaji Umar Dikko ya raini yayansa ne da tarbiyya ta ilmin boko zallah don haka ya;yan gidansu duka sun fi fifita boko a kan komai.

Abin da Uwais ya lura da shi ke nan da ya sa yake ta yi wa Amrah uzuri a bisa sababbn dabiun da yake ta gani a tare da ita, wadanda suka sabawa nashi upbringing din.

Alal misali, Amrah ba ta canza daga irin shigarta ta baya ba, wadda ta ke yi kafin aure ta dan kankanin gyale, hira da abokan karatunta maza, ta waya duk sanda take so, girki ma kuma ba kullum ta ke yi ba yanzu, in kuma ta yin, to sau daya a rana, sannan kuma very simple wanda ta tabbatar ba zai wuce mata minti goma ba, haka Uwais yake hakuri da abubuwa da dama bayan wadannan wadanda yake ganin sun sha bamban da na gidan da ya fito.

Su ma yan boko ne, amma ba masu dabiun nasara ba.

Uwarsa is an Associate Professor.

Amrah ko a ina ta ke za ta iya bude lemo ta sha a tsaye haka yanayin dressing dinta ba ka iya bambance shi da na budurwa mara aure.

Wani abun ko ya gyara mata in bai yi daidai da raayin gidansu ba, ba za ta yi ba.

A wurin Uwais duka wannan mai sauki ne tunda yana samun yadda yake so da Amrah a shimfida.

A wannan fannin kam yana yaba mata, kuma yana samun contentment don haka duk wani flaws na Amrah kankani ne a idanun sa.

Hausawa suka ce, so hana ganin aibi, shi Uwais bayan son da yake wa Amrah har da kauna yar usli mara algus.

Ya kama nan da kwana uku Amrah za ta koma Malaysia, bayan sun shafe watanni ukku tare suna barzar amarci, don haka Uwais yau duk a dame yake, ya zama upset ya kasa nutsuwa a ofis.

Kusan duk bayan mintuna talatin sai ya kira Amrah a waya don ji yake kamar kafin ya kima gida zai je ya tarar ta koma Malaysia.

Sai yanzu da ya san dadin aure ya fahimci cewa yayi babban kuskure da ya yarda da yarjejeniyar karatun Amrah, lokacin idanun sa sun rufe da neman aure, bai yi tunani consequences ba, yanzu kam ya fahimci bai iya rayuwa shikadai na tsayin sati biyu ma ba watanni hudu ba babu mace, in hakan ta faru akwai babbbar matsala, wadda bai san yaya zai yi da ita ba..

Duk da kasancewar sa matashi mai jini a jika, mai tashen kuruciya da hatiman banki, Ubangiji Allah bai dora masa sha'awar zina ba, bai taba fatanta wa kansa ba don haka ya shiga tunanin mafita ga rayuwar sa.

Don ba zai bar Halal ya sabawa Ubangiji don karatun Amrah ba.

Don haka yau da ya taso aiki shine sayi banza sayi hopi duk da yasan Amrah na so na makulashe da kayan amfani saida ya biya ya sayo mata.

Ya san abinda ya tarkowa kansa ba karami bane amma an ce faduwar gaba asarar namiji, kuma a ganin sa a halin yanzu ai yafi Alhaji Umar Dikko iko da Amrah.

Amrah tun daga kofar falo ta tare shi, ta ci sassanyar kwalliyar ta mai taba ruhin Uwais, bakaken riga da wando ne a jikin ta samfurin CK, ta makalkale cikin jikin sa kamar zata yi kuka "Habib-Qalby, yau ka dade baka dawo ba, saura kadan in bi bayanka, ga duhu ya fara shigowa ka sanni da tsoro".

Makale ta yayi a kafadun sa suka karasa bedroom din su yana fadin " i'm sorry Amrah, na je nemo miki pizza dinnan ne da kike so ta Dominos, na tarar basu bude ba sai da naje wani wajen mai nisa" ya fada yana bude ledojin da yayo mata sayayyar, sai smiling take yi gashi duk abubuwan da take so ne.

Uwais ya gama sanin Amrah ciki da bai, ta manna masa kyakkyawar sumba a kunci sannan tace "nagode Habiby, amma tare zamu ci, i'll be chewing it for you (zan dinga tauna maka)".

Dariya Uwais yayi ya marairaice ido tamkar yaron dake gaban Mamarsa "a hakan kuma da dukkan zuciyar ki murna kike zaki tafi ki barni ni daya.

Anya Amrah ba zamu sake shawara ba?

Nace me zai hana tunda bakiyi nisa da fara karatun nan ba a shekarar farko kike ki hakura, na nema miki admission a BUK, Ammi na acan take bazaki sha wahalar samun admission ba.

A ganina Amrah kasancewar mu tare yafi komai muhimmanci, mu shirya welcoming our incoming babies......

Amrah i'm sorry na yi alkawarin da na zo ina tantamar yiwuwar sa, i can't live without a wife Amrah, bansan irin ragaitacciyar rayuwar da zan yi ba.

In kin amince Daddy ba zai ce komai ba tunda rayuwar mu ce mu biyu ba tasu ba.....".
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: Idanun Amrah har wani kanakancewa suka shiga yi sabida bacin rai, tace "Habiby, ka san abinda kake fada kuwa?

BUK?

Who?

Ni Amran?

Amran da na sani Amrah Umar Dikko?

In ma wasa kake tun wuri ka bari kafin Daddy ya ji ka".

Ta mike cikin fushi ba tare da ta dauki komai daga sayayyar da ya yi mata ba ta nufi dakin ta.

Tana shiga daki mahaifin ta ta kira, tana kuka ta gaya masa duk abinda Uwais ya ce.

Alh.

Umar Dikko murmushi yayi irin na manya da suka san halin dan adam.

Yace.

"Ke ba tantabara sarkin soyayya ba?

Duk Yayyen ki wacece tayi aure kafin ta ci karfin karatun ta sai ke?

Kin ga farar fata kin rude kin yarda da dadin bakin sa.

Abinda baki sani ba mu maza duk halin mu daya bama iya rayuwa babu mace.

Kafin ya aure ki ba abinda bazai ce ba, amma yanzu tunda kin zama nama sai yadda yayi dake.

Tun farko ma me ya kai ki kula shi har kika bari soyayya ta shiga tsakanin ku kina level 1?

Inda kin bi tsarin dana yi miki tun farko da hakan bata faru ba.

Amma tunda bisa yarjejeniyar nan muka amince aka yi auren ni da iyayen sa to yayi kadan wallahi.

Gobe zan turo direba kawai ki biyo shi ku taho, daga nan Abuja ki wuce Malaysia, in zai iya auren ya jira ki as promised, in bazai iya ba babu dole fa a rayuwar nan Amrah... your future is your life, kafin kiyi tunanin farin cikin namiji think of your future, think of yourself first, kafin kowa ya biyo baya.

Your husband only wants to destroy your future......" Amrah bata iya ta karasa sauraron abinda Daddyn ta ke fadi akan Uwais ba ta kashe wayar ta.

Ta san Uwais yana son ta, kuma son ne yasa yake son kasancewa da ita, amma is it true that he wants to destroy her future??

Tambayar da bazata iya yiwa Uwais ba, domin yanada kima a idanunta da madaukakiyar daraja, saidai bazata yarda ta bari ya kassara burin rayuwar ta ba don amfanin kansa.

Yau ma kowa a dakin sa ya kwana.

Everyone of them is entitled to his opinion.

Uwais ya tafi aiki a washegari ba tare da Amrah ta bashi karin kumallo ba kuma batare da ya ganta ba.

Wajejen karfe biyu na rana yana fama da ayyuka a kwamfutar ofishinsa sakon Amrah ya shigo masa.

"On my way to Abuja, daga can zan wuce Malaysia, See you soon... so much Love.
-Amrah.

Al'amarin da ya daurewa Uwais kai, ya kasa koda motsi akan kujerar sa.

Bai taba hango matsala kwatankwacin wannan zata kasance tsakanin sa da Amrah ba.

In yayi la'akari da cewa auren so da kauna suka yi dukkannin su.

Amma Amrah har zata iya yanke wannan hukuncin ga auren sa ba tare da ta ji ko dar ba?

Lokaci na farko da ya ji yayi fushi matsananci da Amrah, fushi kuma ba na wasa ba.

Ya sa a ransa zai daure ba zai kara neman ta ba ko a waya har sai ya ga iya gudun ruwan su ita da mahaifin ta.
Chapter 11 · 0% Book details