← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 35

Sashe 28

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakuri da juriya za ki sa a ranki, duk wata mace da ki ka gani da 'ya'yanta abin sha'awa sai dai ta yi wannan hakurin ta same su.

A hankali za ki saba kin ji ko Fahimah ta?

Lada ne babba ki ke samu a wurin Ubangiji wanda zai miki silar shiga aljannah".

Sosai ta fahimci cewa cikin al'amarin Ammi Safeeyyah babu son kai ko son zuciya, face kauna zallah ta fisabilillah da ta ke mata, shi ya sa ta ke so mata rayuwa da gudan jininta mafi soyuwa a gare ta.

Fahimah ta kwana addu'ar Allah ya ba ta lafiya, juriya da tsawon ran da za ta ci gaba da kulawa da bukatar gangar jikin Uwais, da komai nasa, har zuwa ranar da ta daina numfashi.
******
Washegari suka yi sallama da kowa, bayan Ammi ta tsuma 'yarta ta gyare ta tas da gyara irin nasu na Sudanese din asali.

Jirgin karfe tara na safe suka biyo wanda zai sauka a Kano.

A cikin jirgi babu irin korafin da Fahimah ba ta sha daga Uwais ba a kan abin da ta yi masa jiya, har da cewa,
"Me ki ka dauke ni ne?

Wanda bai iya rayuwa sai da ke ko me?

Dana kwana nikadai me kika ga ya same ni?

Karewa ma matata da na ke so ta dawo already, don ta bani kulawar da duk nake bukata.

Don Allah Fah-himah ki jika abinki ki shanye".

Fahimah ba ta tanka shi ba, amma ji ta yi gaba daya hankalinta ya tashi.

Idan da gaske Amrah ta dawo ita mene ne makomar rayuwarta?

Shin za ta iya sake barci a duniya ba tare da Uwais a gefenta ba?

Ya sanya ta cikin wata sabuwar rayuwa mai wuyar bari da wuyar mantawa.

Ta yarda ashe a can baya So kawai ta ke masa na fatar baki, yanzu ne ta san tana son Uwais har ruhi da bargon jikinta.

Idan kuwa abin da Ammi ta ce gaskiya ne (physical relationship between husband & wife).

Alamu ne na so, kuma ba ya faruwa sai da soyayya ko yaya ne, to ta yarda Uwais yana sonta ko da bai furta a fatar bakinsa ba.

Ita kam ai yanzu kalmar kiyayyar Uwais ta daina razana ta, ta daina bakanta mata rai ko da zai kwana yana fadi akan mumbari ta bakin Ammi, domin kuwa har kakannin I love you Uwais ya gaya mata ba tare da ya san lokacin da ya fada din ba.

In haka ne ashe ita ma mutum ce, kuma mace mai daraja kamar kowacce mace duk da kalar fatar tata, ba za ta kara bar wa Amrah miji ita kadai ba.

Da Uwais ya ishe ta da mita da korafinsa da ya ki karewa sai ta tashi tsam ta bar masa wajen, ta koma can wata empty seat a cikin jirgin ta zauna.

Tunda ya ambaci cewa Amrah ta dawo ta ji ko muryarsa ba ta son ji, kallonsa ma bacin rai yake sanya mata.

Ya so ya bi ta inda ta koma ya ci gaba da damunta da complain don kuwa ba da wasa ba ya azabtu a jiyan, ya ji haushin abinda tayi masa, yayi hakuri ne sabida Ammi, sai ya hango ta tana share hawaye, duk kuma sai jikinsa ya yi sanyi, domin ya fahimci ko me Fahimah ta ke wa kuka ba zai wuce RABUWAR SU ba tunda Amrah ta dawo.

To amma shin yana da guts na gaya wa Amrah yana da wani auren, auren ma na wadda ya taba kira
ar aikin gidansu?

Ko kuwa shin zai iya jure rayuwa yanzu babu Fahimah?

Tsakanin ita da Amrah wacece ta fi muhimmanci ga rayuwar sa?

Tambayoyi ne da ba shi da amsarsu, kuma bai san amsar tasu ba.

Sannan bashi da mai amsa masa.

Har jirgin su ya yi landing a Kano.

A nan airport dama ya adana motarsa, ya je inda ya bada ajiyar ya dauka suka wuto gida.

Baba Talatu ce ta bude kofar falo tana musu sannu da zuwa, ta karbi kayayyakin hannunsu, Uwais ya wuce bangarensa, ita ma sai ta wuce nata dakin domin ta yi wanka ko ta warware gajiyar da ke nukurkusarta.

Kafin ta fito Baba Talatu ta shirya musu abinci a dining mai rai da motsi, wanda ta yi musamman domin tarbar su, sinasir ne da waina da miyar egusi wadda ta ji ganyen alayyahu da naman rago.

Fahimah sai ta samu kanta da zama ta tsantsara kwalliya ta gani ta fada da kyakkyawar atamfa super Vlisco light blue.

Wai aka ce in ba ka yi ba ni wuri, ba za ta kara bari a barta matsayin
ar jiran gida ba.

Uwais ya fito bayan magriba ya canza zuwa kananan kaya, bakar riga ce shirt a jikinsa samfurin Balanciaga da wando chinose, sumar nan ta sha wanki da arganavita ta kara baki sai sheki ta ke.

Da Fahimah ta daga ido ta dube shi sai da tsigar jikinta gabadaya ta tashi.

Da ta tuna duka wannan kwalliyar ta Amrah ce ba tata ba, sai bacin ran duniya da wani bala
n kishi suka zo suka lullube ta.

Uwais gab da ita ya ja kujera ya zauna, kafadunsu na gugar na juna, sanyin kamshin (Maison Francis) har cikin ruhinta.

Ta lumshe ido sannan ta bude su a kanshi tana kallon sa da idanun rauni, jin yana take mata yatsun kafa da nashi yatsun.

Ya ce,
adame, ya ya kin gama shiryawa?

Yanzu za mu wuce fa
Fahima ta zaro sparkling eyes dinta a kanshi cikin rashin fahimta, Uwais ya gyada kai cikin tabbatar mata.
are za mu tafi Fahimah, gidanki za ki koma!

Sai ta ji tamkar an yi mata rahma, duk da bata da niyyar bin nasa, at least ya nuna yana son zama da ita koda bata bishi ba, tamkar ya yaye mata wani nannuyan dutse daga kirjin ta, duk wata damuwa da wani bacin rai sai ya kau.

Ta ji kamar ta rungume Uwais, amma ta kwabi kanta da ta ja ajinta.

Girgiza kai ta yi,
abu inda za ni Yaya Uwais babu sanin Ammi
Uwais ya juyo sosai ya sanya fuskar Fahimah cikin tafukansa biyu, ya sumbaci lebunanta keenly, skyblue kwalliyartacikin atampa ta yi mishi kyau ba dan kadan ba, ta kara fiddo da ainahin kalar fatarta mai kyau da ilhamar ta.

Ya ce,
dan kuma Ammin ta dawo ta ce na barki ke kadai fa?

Da sauri ta ce,
a komai, zan zauna, ai ga Baba Talatu ta dawo
re you sure za ki iya barci?
ure, I would
Sai ga hawaye kuma sun zubo.

Uwais ya sanya babbar dan yatsansa ya lakato hawayen, ya ce,
annan fa na mene ne?
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Uwais ne a gaba, Fahimah na biye da shi a baya suka ratsa ta tsararrun falullukan Amrah, a falo na karshe ya ce ta zauna don yana kyautata zaton Amrah ta yi barci.

Amma da ya daga labulen bedroom dinta sai ya same ta tana sallah, wadda bai san ta nafila ce ko isha ce ba.

Ya zauna a gefen gadonta har ta idar.

Tun tana sallar ya fahimci ta kai hannu ta toshe hanci, tsaki ya yi ya ce,
mrah why?

Wai a kanki aka fara ciki ne? ko ko naki ne ya fi na kowa tsurfa?

Ta sallame sallarta tana kallonshi cikin haushi, ya je ya dade ya yi dare son ransa kuma ya zo yana mata zancen wofi, zuciyar mai ciki da ma a kusa ta ke, ta ce,
on Allah fita min a nan Uwais, da kai da gallababben turarenka
Yau Uwais din tsura ta fada not Habiby ko Habib-Qalby, ya ce,
o kin sa na dauko
ar Ammi ko in maida ta ne?

Da sauri ta mike tana fadin,
i ban san tare ku ke ba, ba ka yi min bayani ba
Suka tadda Fahimah a inda ya barta, Amrah da fara
sosai ta ke mata barka da zuwa, ta dauki jakar kayanta ta ce,
abiby ya ya sunanta?

Irin kallon da ya yi wa Fahimah ya sa ba shiri ta sunkuyar da kanta.

Ya ce,
ambaye ta mana?

Ai tana jinki
Murmushi Fahimah ta yi ta dubi Amrah wadda a take ta ji Allah ya dauke mata kishin Amrah da ke ranta.

Ta ce,
unana Fahimah.

Wasu kuma kan ce, Fah-himah
? (tana nufin Uwais, shi ne mai kiranta da Fah-himah)
i ma Fah-himah zan ce, yafi dadi, Fahhimah please taso mu je in raka ki dakin da na ware miki tun safe.

Ki kwanta ki huta
Fahimah ta mike ta bi bayan ta.

Uwais ya bi su da kallo admiringly a zuciyarsa kuma yana taraddadin ranar da gaskiya za ta bayyana ga Amrah, duk sunan da ta kira shi da shi a lokacin daidai ne.

Makaryaci?

Maha
nci, mayaudari ko maciyin amanar soyayyah?

He
ready to face and accept all the names in dai a karshe za ta yi hakuri su hada kai su yi rayuwa mai albarka su ukun.

Amrah will never be enough for him shi ya sani, duk da cewa har gobe ita ce zabin zuciyarsa, muhallin da kowacce ke da shi a yanzu cikin ransa daban ne da na
ar uwarta; duka yana son abinsa, kowacce da bigiren da ta cike cikin zuciya, ruhi da gangar jikinsa.

Amma Fahimah na da wani extra matsayin a zuciyarsa wanda ya wuce soyayyah
? wanda sexual bond ke karawa tsakanin miji da mata, sama da wannan ita din abin so ce ga mahaifiyarsa da ba ya hada ta da kowa a duniya sannan ta zama wani babban bangare na barin jikinsa
? abin nufi, a ita ne yake samun nutsuwar da duk da namiji ke son samu a diya mace.

Yayin da Amrah har gobe take a matsayin MATAR SO ta likawa a goshi.

Ya yi kokarin ya daidaita matsayin kowacce da na
ar uwarta cikin zuciyarsa a daren yau, sai ya ga cewa daidaiton bai yiwuwa, domin ratar da ke a tsakani mai tsananin fadi da girma ce da ta shallake tunaninsa
?....Ashe namiji kan iya son wata a lokaci guda, sama da first love dinsa???
Chapter 28 · 0% Book details