← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 35

Sashe 3

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

In Amrah ta same shi, to hakika ta yi dace da miji na nuna wa saa.

Suka taho gidan Jabir inda Uwais ya sauke shi, Jabir ya yi masa tayin shiga gidan ko zai so yin magana da Amrah.

Uwais ya yi murmushi ya ce da shi,
Not now, Im not in contentment, tunda na samu licence dina.

Zuwan Uwais na farko wajen Amrah a wani daren asabar ne, ana tsula ruwan sama, ruwan har ya fara jika shi, a lokacin da ya yi parking ya fito daga mota, ya bi ta garage zuwa falon Jabir inda nan ne ba shi da shamaki, kuma sun yi waya da Jabir ya ce yana gida ita ma Amran tana nan.

Amma ya ce masa ya zo da wuri don Amrah in ta fara karatun darenta ba ta so a katse ta.

Kuma wannan ne karo na farko da za su ga juna officially, ta sanshi a fuska amma a matsayin abokin Yayanta.

Yana zaune a falon Jabir yana mai duba agogon hannunsa.

Jabir ya ce da shi ya jirata tana zuwa, sannan ya gaya wa Murjanatu Amrah na da bako a falo, kuma da sanin Daddy ya zo ganinta.

Bako daga Daddy?

Amrah ta tambayi Aunty Murjanatu cikin mamaki.

Murja ta ce, Haka dai ya ce, kuma ki yi sauri yana jiranki.

Ko kadan Murjanatu ba ta yi mamaki da zuwan Uwais yau wajen Amrah ba, don ta dade da sa wa a ranta in ka ga kare na sunsunar takalmi dauka zai yi.

Amrah ta yi sallama a falon da siririyar muryarta mai kidima nutsuwar Uwais.

Mikewa tsaye ya yi ba tare da ya san lokacin da ya yi hakan ba.

Har sai da Amrah ta shigo suka tsaya suna kallon-kallo ta hasken farin kwan lantarkin da ke falon.

Zuciyarsu na bugu iri guda a lokaci guda, yayin da Amrah ta ji tamkar an sauke mata wani nannauyan dutse daga kirjinta.

Uwaisun da ta ke kwana da shi tana tashi da shi Uwaisun da ya yi wa zuciyarta babakere ya hana ta sukuni da jin dadin rayuwar ko ta ya ya, yau ga shi a gabanta officially ya kawo kansa matsayin manemin auren ta..Me zata ce?

Ko me zata yi?

Banda tazbihi ga Ubangiji?

Ita ta fara dauke idonta daga cikin na Uwais amma ta yi-ta yi ta furta kalmar ina wuni?

Ko sannu da zuwa ta kasa.

Zama ta yi a kujera mafi kusa da ita, ta jingina kanta a makarin kujerar don hana kafafun ta kayar da ita daga wadannan kaifafan sexy eyes din na Uwais, tana sauke numfashi a hankalitamkar Uwais ya karanci abinda ke ranta, sai bai wahalar da kansa wajen gabatar da kan sa ba.

Kai tsaye ya tafi straight to the point .

Amrah am I welcome as a husband?

Uwais ya fada daga karshe, yana mai durkusawa a gabanta a kan gwiwoyinsa.... wani abu abu da bai taba tunanin zai iya yi a kan diya mace ba.

Murmushin da Amrah ta yi, da fuskarta da ta rufe da tafukan hannunta kadai a matsayin ta na bafullatana tamkar amsa ce ga UwaisUwais Shagari, Uwais Abdulkarim Shagari.... and that is the beginning mafari, tushe, sila, na dukkan abubuwan da suka biyo baya......Sannan silar data zamo hanyar auren UWAIS da FAHIMAH......
****
Ya dauki lokaci mai tsayi yana zuwa zance wajen Amrah, sun fahimci juna sun yarda da juna, soyayya ta yi kaka-gida, hutun nata da ma na watanni uku ne, har ga shi gobe za ta koma Abuja inda daga can za ta zarce makarantarsu ta Limkwokwing, Malaysia.

Yau da ya zo sallama ce za su yi, in ka gansu very emotional kamar masu shirin barin duniya don damuwa, Amrah ta shiga ran Uwais yadda ba'a zato haka Uwais ya samu matsayi mai girma a zuciyar Amrah, ta yadda suke jin rabuwar tasu ta yau har cikin bargonsu.

Ba don kada in yi wa Daddy laifi ba ya ce zan hana ki karatu, da na kawo miki ziyara a Malaysia.

Amrah ta zaro ido ta ce, Kada ma ka fara 'Habib - Qalby', Daddy bai hada karatu na da komai, za mu kasance a waya koyaushe insha Allah.

Abinda zan sake dawowa bayan watanni hudu kuma a nan Kano zan sake yin hutuna?.

Ke kike ganin watanni hudu kwana hudu Amrah, i see them like eternity.

To Amrah ta ya ya zan amince ni ina nan goho ina jira, wani a can ba zai min shigar sojan badakkare ba?.

Ya fada sounding emotionally worried.

Amrah ta yi murmushi, ta ce, Tunda Daddy ya amsa maka, to ka kwantar da hankalinka ya tsumma a randa, domin Daddy ba ya magana biyu.

Sannan ni wa zan kula?

Karatun da ke gabana kadai ya ishe ni, ka yarda da ni Habib-Qalby...(sunan da ta rada masa) a Hausance yana nufin 'masoyin zuciya ta'..

Ya ce, Na yarda da ke Amrah, in na ce yarda ina nufin yarda ta har abada cikin aminci.

Ki yi karatu mai yawa with me in mind and our next coming babies.

Amrah ta kai tafukanta ta rufe fuskarta cikin jin kunya.

Ba ta ga lokacin da Uwais ya taso daga kujerarsa ba, sai tsinkayarsa ta yi tsaye a gabanta, hannayensa duka biyu zube cikin aljihu, ya ce,
Amrah kin amince min kafin ki dawo in tura magabatana wajen Daddy su kara rokonsa a gabatar da neman aurenmu?

Na yi alkawarin za ki cigaba da karatunki ko da kina Malaysia ni ina nan Kano.

And I promised you eternal love Amrah, jiran ne ba zan iya ba.

Amrah ta kai hannu ta rufe fuskarta, kyakkyawan murmushin da ke kan fuskarta kadai amsa ce ga Uwais, na ta amince ya tura neman auren ta.

Don haka da karfin gwiwarsa ya koma gida duk da yana cikin alhinin rashin Amrah da zai yi a kwanakin.

Ta riga ta zama wani bangare na ruhinsa cikin dan lokaci kalilan.

Ya shigo gida misalin karfe goma na dare.

Tuni Ammi ta dade da kwanciya.

Har ya shiga bangarensa.

Ya yi wanka ya canza kaya zuwa Pajamas farare sol ya ankara da yana jin yunwa, yunwa sosai da ke bukatar tallafi, ya san yanzu Talatu ta jima da komawa Baskwata, Ammi kuma ta kwanta, don haka ya yanke shawarar zuwa kitchen ya nema wa kansa dan abin da zai iya ci ko ya yi barci cikin nutsuwa.

Ta juya baya tana fasa kwai a cikin tangaran, ita ma yunwar daren ce ta taso ta, kawai sai ta jiyo takun mutum a bayanta, ta juyo da sauri duk da kamshin turarensa ya riga ya gaya mata ko waye.

Ya sunkuya ya bude firji ba tare da ya lura da tsayuwarta ba, Fahima ba ta kara mallakar kanta ba daga lokacin sabida rudewa da bugun zuciya wanda ke faruwa da ita a duk sanda ta ga Uwais.

Kwan hannunta ya subuce ya fashe a kan kafarta, daidai lokacin da ya dago da gorar ruwa a hannunsa sai idonsa cikin na Fahimah.

Wani haushi ya kama shi da karfi ya ce,
What are you doing here?

You Goddam Black, mai idanu irin na kyanwa!

Ganinki cikin dare sai ya firgita mutum get out from here.

Ya fada da tsawa.

Jikin Fahimah na mugun rawa ta juya ta bar kicin din, ko kamin ta kai dakinta hawaye ya jika fuskarta.

Ta tsani tsawa, ta tsani kyara da hantara.

Amma inda sabo ya kamata a ce ta saba da su daga bakin Yaya Uwais, don tun tana karama duk wata haduwa da za su yi in dai ba'a gaban Ammi ba ne to irin haka ce ta ke kasancewa.

You goddam black
Ta saba da wannan kalmar.

Shin laifi ne in mace ta kasance baka?

Shin kyawun halitta shi ne yake sa wa a so mutum?

Ko kuwa dai akwai wani dalili da ya sa Uwais ya tsane ta bayan wannan da rashin asalin ta?

Za ta so wani makusancin sa ya samo mata wannan amsar daga Yayanta Uwais.

Amma ta san ba za ta taba samun wannan alfarmar ba, ta sanin wani abu da ya danganci wannan kwayan mutum guda daya mafi soyuwa a zuciyarta, sannan mafi munana mata.

Yunwar da ya shiga kicin din da ita sai ya ji ta dauke sabida bacin ran ganin Fahima.

Tsaki ya yi ya ajiye gorar ruwan ya koma daki.

Ya yi nafilfilin da yake yi kafin ya kwanta sannan ya dauko waya ya kira Amrah don jin muryarta ne kadai zai sa ya yi barci lafiya.

Sun dade suna hira, planning iri-iri na irin yadda za su gudanar da rayuwar aurensu.

Hatta yayan da za su haifa sai da suka kayyade.

Sannan suka koma musun da wa suke so yayan su yi kama, shi kuma ya dage da ita yake so su yi kama itama ta dage da shi take so, a haka suka shiririce suka bata lokaci.

Hirar da ta kai su har sha biyun dare, sai da Amrah ta soma hamma sannan suka yi sallama.

Da wani irin nishadi Uwais ya yi barci don in yana gaban Amrah ko yana jin sassanyar muryarta manta kansa yake yi, duk wannan miskilancin da izzar nemansu yake ya rasa in dai yana tareda Amrah, in ka ji shi yana zubo hira da kalaman soyayya ka kuma sanshi a tsumammen Uwais dinsa manajan GT ba za ka taba yarda cewa shi ne ba.

Fahimah a wannan dare ba ta runtsa ba.

Ba bacin ran abin da ya yi mata ke damunta ba, aa soyayya ce ta ke nukurkusarta, soyayyah yar usli mara algus daga indallahi wadda ba za ta iya tantance daga lokacin da ta samu muhalli a zuciyarta ba.

Abin da ta sani kawai shi ne, ta taso cikin son Yaya Uwais ba tare da ta san hakikanin mene ne maanar feelings dinta a kansa ba.

Sai yanzu a hankali da hankali ya soma game jikinta, ta fahimci zuciyarta is infactuated sosai a kan Yaya Uwais, son da ta tabbatar ba zai taba amfana ta da komai ba.

Don haka a wannan dare Fahimah ta yanke shawarar fara adduar Allah ya cire mata Uwais daga zuciyarta ko ta samu sa'idah.

Ya munana shi a zuciyarta kamar yadda ta ke mummuna a tashi zuciyar.
Chapter 3 · 0% Book details