← Book details Fahimah Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 35

Sashe 5

Fahimah Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya tsani ya bude ido ya ganta gabansa, sabida yawan tsawar da yake mata ko hanyar dakinsa ba ta bi.

Haka in yana falo ta leko ta ganshi komawa dakinta ta ke ta rufe kofa har sai ya fita.

A haka suka taso, Fahimah na mamakin abin da ya sa ita nata Yayan ya tsane ta, bayan ba haka ta ga sauran yayyen kawayenta na makaranta suna treating dinsu ba.

Duk ranar da uzuri ya sa Ammi ba ta dauko ta a makaranta ba, ta tura shi ya dauko ta sai ta dawo da kumburarriyar fuska, ya mammake ta a motar ko ya rarrankwashe ta.

Dalili hakan ya sa Ammi daukar mata direba nata ita kadai lokacin da ta shiga sakandire a Yan Dutse.

Ammi ta yi nasihar, ta yi lallashin a kan Uwais ya karbi Fahimah a matsayin yar uwarsa da Allah ya ba shi, har ta koma ta zuba ido, domin kuwa Uwais kaifi daya ne.

Kuma mai gabadaya.

Abin nufi; In zai so abu dukkan soyayya yake masa, haka in zai ki shi, muguwar kiyayyah yake masa bata wasa ba.

Ya sha gaya wa Ammi shi ba zai taba son wannan tsintacciyar magen da ta kawo musu ba.

Tun yana yaro Allah ya zuba masa baiwar kyau na larabawan ifriqiyyah, wani irin kyau mai sanyaya idanun duk mai kallon sa, ya hore masa kwakwalwar karatu musamman darasin lissafi, don haka ne da ya zo shiga jamia ya zabi ya karanta aikin banki.

Ya yi digirinsa na farko da na biyu a jamiar Ahmadu Bello, inda ya karanci fannin accountancy.

Bai dade da kammala karatu ba ya samu aiki da babban bankin Guaranteed Trust (GT Bank) matsayin akawu (Accountant) sabida kyawun takardunsa.

Haka rayuwa ta mika wa wannan family cike da ci gaba da nasarori.

Zuwa wannan lokacin Ammi Safiyyah na amsa rank na (Associate Professor) a tsangayar Economics da ta ke koyarwa.

Fahimah na ajin karshe a sakandire.

Uwais kullum cikin promotion yake daga bankin GT sabida kwazonsa da persevearance.

A halin yanzu shine babban manajan Branch din GT da yake kan titin (Bank Road) da ke cikin birnin Kano.

Ya karbi ragamar kula da komai na nauyin gidansu ban da shaanin FAHIMAH.

A wurin sa kam Ammi ce kawai dangin ta.

Bai taba cewa wani yana da kanwa ba.

Koda dangin su na Sudan.

Baya bari ma wadanda suka san shi su san da wanzuwar ta tare da mahaifiyar sa.

Ya tsaya kamar shine Grand Khadi Shagari, baka taba gane babu mai gida a gidan sabida tsayuwar dakan Uwais akan komai na gidan.
*****
Hajiya Safiyyah ta nisa a hankali lokacin da tunaninta ya zo nan.

Ba ta haifi Faheemah ba, amma yadda ta ke jinta a zuciyarta ba maraba da yadda ta ke jin tilon danta Uwais.

Abubuwa da yawa suka yi sanadiyyar wannan kauna; halayen Faheemah da matsananciyar biyayyar da ta ke yi mata.

Kafin a samu yarinya nitsattsiya cikin yammata dubu irin Fahimah sai an tona.

Sai dai daga ita har Fahimar sun kwana da sanin cewa babu wanda Uwais ya tsana a duniya irinta.

A shekarun ta na kuruciya Fahimah ta san Hajiya Safiyyah ba ta haife ta ba, amma in za'a kashe ta, ba ta san ta ya ya aka yi ta zo hannunta ba.

Ta budi ido ne kawai ta ganta a gabanta cikin wata irin kulawa wadda mahaifiya ce kadai za ta yi wa dan da ta haifa.

Safiya ce mai tsananin hazo wadda matsanancin sanyin watan Nuwamba ya haifar, ranar ta kasance Litinin, aka ce ko Bature yana tsoron ki, tafe yake cikin motarsa Kia Picanto fara sol sanye cikin bakaken suit na maaikatan bankin GT, a nutse yake tukinsa kamar yadda ya saba misalin karfe bakwai na safe.

Daidai lokacin da danja ta tsaida su a shateletalen Beirut Road ya rage gudun motar ya tsaya a gefen wata mota Toyota Camry.

Hankalinsa na kan danja cike da kaguwar ta ba su hannu domin hakika ya kusa makara, sai ji ya yi daga gefensa an kira sunansa cikin tu'ajjibi..
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: UWAIS SHAGARI?!

Ya juya a hankali cikin aji irin nasa ya dubi mai kiran nasa, JABEER DIKKO.

Ya kira sunan mutumin da yanayi na mamaki.

Daidai lokacin da danja ta ba su hannu duk suka gangara gefen titi don su samu damar gaisawa da juna.

A tare suka fito daga motocinsu suka cafke hannun juna, they have been good friends during their university years a jamiar Ahmadu Bello, bayan sun kammala ne Jabir ya samu tafiya kasar Kuwait yin masters dinshi, yayin da shi Uwais ya ci gaba a nan Ahmadu Bello ba su kara haduwa ba kuma sai yau.

A gurguje suka yi musayen lambar waya da alkawarin Uwais zai zo gidansa in ya tashi ofis don shi Jabir ya yi aure ba dadewa, a yanzun yana aiki ne da FCMB.

Kamar yadda ya yi alkawari yana tashi daga ofis ya dawo gida ya yi wanka ya sake shiryawa cikin shadda wagambari mai hasken sararin samaniya, inda duk ya gifta sanyin Maison Francis dinsa ke tashi.

A falo ya tadda Ammi, Fahimah na murza mata menthol a kafafunta kamar yadda ta ke mata duk dare, kallo daya ya yi mata ya dauke kai, a ransa fadi yake, yarinya kullum kamar ana shafa mata shuni don baki.

Ammi ta dube shi affectionately (cike da kauna) ko ita da ta haife shi in ya dau wankan nan kwarjini yake mata.

Ta ce,
Sai ina haka?

Bayan ga abinci Talatu ta shirya maka?

Ya ce "I'm sorry Ammi, an gayyace ni cin abincin dare, abokina Jabir na Kuwait da na ke ba ki labari yau Allah ya sake hada mu.

Ammi ta ce, A dawo lafiya, a gaishe shi.

Ya sa kai ya fita, Fahimah na satar kallonsa ta gefen idonta, kirjinta na wani irin duka.

A karshe ita da Ammi suka ci abincin da ya bari din, suna gamawa ta kwashe komai ta kai kicin ta gyara wajen ta yi wa Ammi sallama cewa tana da karatun da za ta yi, sai ta shige dakinta ta kulle kanta.

ahimah Shagari.

Kamar yadda ake kiranta a makaranta, budurwa ce yar kimanin shekaru goma sha takwas da haihuwa.

A bana ne za ta kare karatun sakandire.

A jerin kyawawan mata ba za ka sanya Faheemah ba domin ba ta da artificial beauty irin na yammatan yanzu, komai nata natural daga kalar fata har gashin kai.

Baka ce sidik, fatarta mai sulbi da daukar idanu.

Tana da manyan ido mai haske da madaidaicin hanci, gashin kanta kakkarfa na asalin Hausawa wanda ba ta taba yi wa relaxing ba sai dai ta yi steaming dinsa.

Bakinta dan madaidaici, ba ta a layin dogaye kamar yadda ba ta a layin gajeru, ga ta nan dai yar dagwas da ita, wadda tsafta da wanka suka kama jikinta.

Fahimah ta dauko littafin Food and Nutrition daga jakarta ta makaranta da niyyar karantawa kamar yadda ta yi niyya, don tana da gwaji (test) a kansa a washegari talata.

Shine kuma best subject din ta.

Amma me?

Ko da ta bude shafin farko ba ta ga komai a ciki ba.

Shafin ya koma blank, sannan basudaniyar fuskarsa ta maye gurbinsa.

Ta bude shafi na biyu don a zatonta a wancan shafin ne kadai Uwais ke yi mata shifcin gizo, sai dai duka sammakal.

Cikin kowanne shafi da ta bude ba ta ganin komai sai Uwais Shagari, fuskarsa, tsayuwarsa, cin maganinsa da maganarsa cikin seriousness.

A duniya ba ta taba ganin abin da ke wahalar da ita da dagula mata lissafi ya hana ta jin dadin rayuwarta ko ta ya ya irin tunanin miskilin Yayan nata, wanda bai san tana yi ba, bai san Allah ya yi ruwan tsirarta cikin gidan su ba.

Ita din ba komai ba ce face abar wulakantawa, kuma abar kyama a gare shi, to a kan me ta ke yawan ganinsa cikin idonta?

Take jin amsa-kuwwar husky voice din sa?

Ta ke kuma jinsa har cikin ruhi da tsokar jikinta???

Za ta so a ce tana da wanda za ta iya yi wa wannan tambayar, tsakaninta da kawayenta na makaranta sabgar karatu ce kadai.

Ammi kullum na gargadinta a kan tara kawaye da fada musu sirrinta, ta gaya mata ita kadai za ta mayar babbar aminiyarta, komai ta ke son tattaunawa na rayuwarta da ita za ta tattauna shi, amma wannan karon ba ta jin za ta iya gaya mata cewa tana da wani irin feeling a kan Yaya Uwais da ke takura ruhinta wanda ita kanta ta ke neman sani a kansa, ko me za ta ce?

Da dai a ce ba Ammin ce ta haife shi ba shi ne za ta iya tattauna wannan alamarin da ita.

A karshe karatun da ta yi niyyar yi bai yiwu ba, haka ta tattara littattafan ta maidasu jakarta.

Ta koma ta kwanta a gadonta ta mike kafafu ta yi filo da hannayenta, ba don babu filon ba sai don ta fi jin dadin kwanciyar ta a haka.

Ta bai wa tunanin Uwais dama ya zo ya sha sharafinsa...... yadda ya ke so, ya ci gaba da lugwigwita zuciyarta....

Idanunta a rufe ruf!

Amma ba barci ta ke ba, ba ta hango komai sai surar Uwais dazu-dazu da zai fita, yana wadannan harare-hararen nasa, da maganar sa sauri-sauri da husky muryarsa mai huda mata ruhi da zuciya....
******
Tun kafin ya gama parking Jabir da matarsa Murjanatu suka fito tarbarsa.

Murjanatu ta sha lullubi a kan kwalliyarta kai daga ganinta ka ga irin mutunci, sannan kuma yar babban gida.

Gidan Jabir Dikko madaidaicin flat ne a unguwar Eastern Bypass.

Sun tsara gidansu shi da Murjanatu daidai da rayuwarsu ta yan boko.

Ita ma Murjanatu maaikaciyar banki ce, sai dai ita tana Polaris, sun hadu da Jabir tun a jamia duk da yana gabanta sosai, hannun Jabir cikin na Uwais suka shiga kayataccen falon nasu.

Murjanatu ba ta tsaya ba, ta yi ta shige da fice daga kicin zuwa falo don wadata su da dukkan abin da za su bukata wajen cin abincinsu.

Suna tsaka da cin abincin ta fito daga uwardakin Murjanatu tana mika..., ga dukkan alamu ba ta san da mutane a falon ba, sannan daga barci ta tashi.
Chapter 5 · 0% Book details